KEDCO ta kai tallafin kayan abinci da na karatu a gidan yara na Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki KEDCO ta kai tallafin kayan abinci da kayan karatu a gidan yara wato (Nasarawa Children Home) da ke unguwar Nasarawa da ke Kano a ranar Asabar wanda ya yi daidai da ranar yara ta duniya.

Da yake jawabinsa yayin miƙa kayan, Babban Manajan Daraktan KEDCO, Alhaji Ahmed Dangana ya bayyana cewa maƙasudin zuwan shi ne sanya farin ciki da murna ga a zukatan yaran domin yawancinsu ba su samu ni’imar da Allah ya bai wa waxanda ba sa gidan ba.

Ya ƙara da cewa “mun zaɓi ranar 27 ga Mayu, 2023 ne saboda ita ce ranar yara ta duniya domin mu ba su tallafi kuma mu yi hira da su, mu ji mene ne buƙatunsu, sannan mu ga ta yaya za mu cigaba da taimaka masu daidai ƙarfinmu.”

Daga nan ya kuma yi alqawarin samar masu da mita, sannan ya ce ma’aikatansu za su riqa yin karo-karo suna saya musu kati don inganta wutar lantarki a gidan.

Hajiya Aisha Sani Kurawa ita ce jami’ar kula da gidan, ta gode wa KEDCO bisa namijin ƙoƙari da suka yi na kawo masu wannan tallafi, daga nan ya yi addu’a Allah ya saka da alheri.

Daga cikin kayayyakin da suka kai gidan sun haɗa: Shinkafa, taliyar Indomie, kayan karatu, omo, sabulun wanki da na wanka, tishu da sauransu.