Kano: Allah Ya yi wa Sheikh Nasir Muhammad Nasir rasuwa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A ranar Larabar da ta gabata Masarautar Kano ta sanar da rasuwar Limamin waje, Masallacin Juma’a na Fagge, kuma Waziri Murabus a Fadar Kano, Sheik Nasir Muhammad Nasir.

Babban Limamin ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya inda ya bar duniya da shekara 80.

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya jagoranci sallar jana’izar Marigayin wadda aka gabatar da misalin ƙarfe tara na safiyar Alhamis a Fadar Sarkin Kano.

Mai martaba sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero yana daga cikin manyan mutane da suka halarci jana’izar haɗi da sauran manyan mutane da shehunnai da limamai da ‘yan kasuwa da sauran al’umma.

Bayan idar da Sallar jana’zar sai Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da ɗan uwansa Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da sauran ɗaruruwan al’umma suka raka gawar zuwa makwancinta

An binne marigayin ne a maƙabartar Ɗan Dolo dake Goron Dutse cikin yankin Ƙaramar Hukumar Gwale da ke jihar.

Basaraken ya yi addu’ar Allah Ya gafarta wa mamacin Ya sa Aljanna makoma a gare shi tare da baiwa iyalai da ‘yan uwa da sauran al’umma haƙurin jure rashin.

Kafin rasuwarsa, Sheikh Nisir Muhammad Nasir babban amini ne ga marigayi Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayero wanda ya bayar da gudunmawa a ɓangarori daban-daban.

Marigayin ya rasu ya bar matansa na aure da ‘ya’ya da kuma jikoki masu yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *