Kasashen Waje

Al’ummar Afirka ba su buƙatar a yi musu lacca

Al’ummar Afirka ba su buƙatar a yi musu lacca

Daga LUBABATU LEI Ta hanyar amfani da tashoshin sadarwa na wayoyin salula da manhajojin waya da yanar gizo da dai sauransu, bisa fasahohinta na zamani, Amurka ta daɗe da yi wa gwamnatocin ƙasa da ƙasa da kamfanoninsu da ma al’ummarsu leken asiri, ciki har da ƙasashen Afirka, muna iya cewa, ta amsa sunanta na babbar ɓarauniyar satar bayanai. Sai dai a kwanan nan, barauniyar ce take sake yin kiran a kama barawo, inda mataimakiyar sakataren harkokin wajen ƙasar ta Amurka Wendy Sherman a ziyararta a nahiyar Afirka, ta ce wai, yadda wasu ƙasashen Afirka suka zabi kamfanin Huawei na ƙasar…
Read More
Masana sun yi Allah wadai da yunƙurin Amurka na neman daƙile cigaban al’ummar Xinjiang

Masana sun yi Allah wadai da yunƙurin Amurka na neman daƙile cigaban al’ummar Xinjiang

Daga CMG Hausa Kwararrun masanan ƙasar Sin sun soki lamirin ‘yan siyasar ƙasar Amurka masu adawa da ƙasar Sin, wadanda ke shirya maƙarƙashiya domin hana al’ummar yankin Xinjiang damamamkinsu na cigaba ta hanyar yaɗa ƙarairayin cewa, wai ana tilasta aikin kwadago a shiyyar. Sun yi Allah wadan ne a yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Juma’ar da ta gabata a Urumqi, babban birnin jahar Xinjiang mai zaman kanta ta Uygur ta ƙasar Sin. Cao Wei, wani shehun malamin jami’ar Lanzhou, ya bayyana cewa, sakamakon fargabar kakaba takunkumi daga ƙasar Amurka, ya sa wasu daga cikin kamfanoni ba…
Read More
Ƙasashen BRICS sun yi kira a haɗa kai don tinkarar sauyin yanayi

Ƙasashen BRICS sun yi kira a haɗa kai don tinkarar sauyin yanayi

Daga CMG HAUSA Kwanan nan ne aka gudanar da babban taron ƙasashen BRICS kan tinkarar sauyin yanayi ta kafar bidiyo, inda aka yi kiran a hada kai don tinkarar matsalar sauyin yanayi, da tattaunawa kan gaggauta rage fitar da iskar dake gurbata muhalli, da lalubo hanyar samun farfaɗowa mai ɗorewa da daidaito da nuna haƙuri. Ministan kula da muhallin halittun ƙasar Sin, Huang Runqiu ya gabatar da jawabin dake cewa, ta hanyar shirya babban taron ƙasashen BRICS kan tinkarar sauyin yanayi, ƙasar Sin na fatan yin ƙoƙari tare da kasashen BRICS, don tabbatar da aiwatar da ra’ayin kasancewar bangrori daban-daban…
Read More
Amurka ba ta cimma burinta a Asiya ba

Amurka ba ta cimma burinta a Asiya ba

Daga CMG HAUSA Ranar 13 ga wata, aka rufe taron koli na musamman tsakanin ƙasar Amurka da ƙasashe mambobin ƙungiyar ASEAN a birnin Washington, babban birnin ƙasar, wanda aka dakatar da kira a baya. Sai dai babu wani abu takamaimai cikin sanarwar haɗin gwiwa da aka bayar bayan rufe taron. Manazarta sun yi nuni da cewa, lamarin bai wuce zaton mutane ba, wato Amurka ta yi shelar ƙara yin abota da ƙasashen Asiya, amma haƙiƙa dai tana yunƙurin haɗa hannu ne da waɗanda ke adawa da ƙasar Sin. Kafofin yada labaru na ƙasashen duniya sun lura da cewa, Amurka ta…
Read More
Ya kamata Sin da Amurka su ƙara haɗin gwiwa a fannin aikin noma

Ya kamata Sin da Amurka su ƙara haɗin gwiwa a fannin aikin noma

Daga CMG HAUSA An gudanar da taron tattauna bunkasa aikin noma da yankunan karkara tsakanin ƙasashen Sin da Amurka ta yanar gizo a baya bayan nan, wanda kwalejin ilmin bunkasa ƙasa da ƙasa da aikin noma ta duniya, ta jami’ar ilmin aikin noma ta ƙasar Sin ta ɗauki baƙuncinsa. Mahalartar taron na ganin cewa, ya kamata Sin da Amurka su ƙara hadin gwiwa a fannin aikin noma, suna cewa, hakan zai amfanawa ƙasashen biyu, har ma da samar da gudummawa ga tabbatar da wadatar hatsi a duniya. Bisa ƙididdigar da aka yi, yawan kuɗin cinikin aikin noma da aka samu…
Read More
Babban titin da Sin ta gina zai bunƙasa ɓangaren yawon buɗe ido a Kenya

Babban titin da Sin ta gina zai bunƙasa ɓangaren yawon buɗe ido a Kenya

Daga CMG HAUSA Ana sa ran babban titin da ƙasar Sin ta gina a ƙasar Kenya, zai bunƙasa ɓangaren yawon bude ido na ƙasar.Sakataren ma’aikatar kula da yawon buɗe ido da namun daji na ƙasar, Najib Balala ne ya sanar da hakan ga manema labarai a birnin Nairobi, babban birnin ƙasar, yana mai cewa, ana sa ran motoci za su fara gwada titin daga ran Asabar. Ya ƙara da cewa, wannan wata makoma ce mai haske ga ɓangaren yawon buɗe ido na kasar, saboda ana sa ran babban titin na Nairobi zai rage lokacin da ake ɗauka daga filin jirgin…
Read More
Shugaban Haɗaɗɗiyar Daularar Larabawa, Kalifa bin Zayed ya kwanta dama

Shugaban Haɗaɗɗiyar Daularar Larabawa, Kalifa bin Zayed ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa kuma ɗaya daga cikin attajiran sarakunan duniya, Sheikh Khalifa bin Zayed al-Nahyan ya rasu. Sheikh Khalifa wanda ya bar duniya yana da shekara 73, ya soma mulkinsa ne tun a 2004, duk da dai galibi mataimakansa ke gudanar da harkokin mulki a madadinsa tun bayan da ya kamu da lalurar shanyewar ɓarin jiki a 2014. A halin da ake ciki, ɗan uwan marigayin Mohamed bin Zayed al-Nahyan, shi ne ke kula da sha'anin mulkin daular. Kamfanin dillancin labarai na WAM da ke daular, shi ne ya ba da sanarwar rasuwar basaraken. A matsayinsa…
Read More
An kafa ƙungiyar bada ilimin sana’o’i ta Sin da Afrika

An kafa ƙungiyar bada ilimin sana’o’i ta Sin da Afrika

Daga CMG HAUSA A ranar 11 ga wata, ƙungiyar mu’ammala ta fuskar ba da ilimi ta ƙasar Sin, ta kira wani taro na ingiza shirin ba da ilimin sana’o’i tsakanin Sin da Afrika, kuma taron kafa ƙungiya a wannan fanni ta kafar bidiyo da a zahiri, don tabbatar da shawarwarin haɗin kan Sin da Afrika, da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika. Mataimakin daraktan sashin hadin kan ƙasa da ƙasa, da yin mu’amala na hukumar ba da ilmi na Sin Jia Peng, ya taya…
Read More
MOFA: Sin da Amurka na iya yin hulɗar abota na bai ɗaya

MOFA: Sin da Amurka na iya yin hulɗar abota na bai ɗaya

Daga CMG HAUSA Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labarai Jumma'ar nan cewa, a matsayinsu na ƙasashen dake yankin Asiya da tekun Pasifik, ƙasashen Sin da Amurka za su iya yin hulɗar abokantaka na bai ɗaya. Zhao ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙarin haske, kan wani taro na musamman da ya gudana tsakanin Amurka da kuma ƙungiyar ƙasashen da ke yankin kudu maso gabashin Asiya (ASEAN), a birnin Washington a ranakun Alhamis da Jumma'a, don tunawa da cikin shekaru 45 da ƙulla hulɗar haɗin gwiwa tsakanin…
Read More
Jakadan Sin: Wanzuwar zaman lafiya ne kariya mafi kyau ga yara a Ukraine

Jakadan Sin: Wanzuwar zaman lafiya ne kariya mafi kyau ga yara a Ukraine

Daga CMG HAUSA Wakilin ƙasar Sin ya bayyana a ranar Alhamis cewa, cimma nasarar wanzuwar zaman lafiya shi ne kariya mafi kyau ga ƙananan yara a Ukraine. Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊƊ ya bayyana cewa, neman yadda za a cimma zaman lafiya shi ne kariya mafi kyau ga yara. Tattaunawar sulhu da neman cimma matsaya su ne hanyoyi mafiya tabbaci kuma hanyoyi masu ɓullewa da za su kai ga tsagaita buɗe wuta. Ya kamata al’ummun ƙasa da ƙasa su ƙarfafa gwiwa ga Rasha da Ukraine don su amince ga komawa kan teburin tattaunawar sulhu, kuma a…
Read More