19
May
Daga CMG HAUSA Wakilin ƙasar Sin ya buƙaci a bada fifiko wajen bunƙasa cigaban yankin Sahel. Zhang Jun, zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD, ya ce Afrika tana fuskantar wahalhalu wajen cimma nasarar samun cigaba. Matsalolin ƙarancin abinci da duniya ke fuskanta a halin yanzu, da matsalar makamashi, da ta kuɗaɗe, sun kara tsananta halin da ake ciki a Afrika, sannan matsalar ta fi kamari a yankin Sahel. Zhang Jun, ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin sulhun MƊD game da shirin G5 Sahel, wato wani shiri ne na hadin gwiwa don tsara manufofin bunƙasa cigaba da tabbatar da…
