23
May
Daga CMG HAUSA Ministan maaikatar cinikiyya ta ƙasar Sin Wang Wentao, ya ce ƙasar sa za ta yi aiki tukuru, wajen tabbatar da nasarar kafa yankin ciniki maras shinge na Asiya da Pacific, cikakke kuma bisa matsayin koli. Minista Wang ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa ta kafar bidiyo, yayin taro na 28 na ministocin ƙungiyar hadin gwiwar raya tattalin arzikin yankin Asiya da Pacific ko APEC, wanda ya gudana a ƙarshen mako. Wang ya ce kamata ya yi dukkanin ƙasashe mambobin APEC su jajirce, wajen gina alumma mai makomar bai daya a matsayin tushensu, su kuma ingiza haɗin gwiwa…
