Kasashen Waje

Ƙasashe mambobin BRICS sun ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwa game da binciken samaniya

Ƙasashe mambobin BRICS sun ƙaddamar da kwamitin haɗin gwiwa game da binciken samaniya

Daga CMG HAUSA A jiya Laraba ne ƙasashe 5 mambobin ƙungiyar BRICS, suka ƙaddamar da wani sabon kwamitin haɗin gwiwa, wanda zai bude sabon babi ga ayyukan su na amfani da taurarin ɗan adam, da musayar bayanai game da sararin samaniya tsakanin su. Da yake tsokaci game da hakan ta kafar bidiyo, shugaban hukumar lura da ayyukan binciken sararin samaniya na ƙasar Sin Zhang Kejian, ya ce kwamitin zai tsara ayyukan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen na BRICS, ta yadda za su ci gajiya daga managartan hidimomin sanya ido ta amfani da taurarin ɗan adam, matakin da zai taimaka wajen raya…
Read More
Waɗanda suka bijiro da batun “halartar Taiwan a taron WHA” sun ji kunya!

Waɗanda suka bijiro da batun “halartar Taiwan a taron WHA” sun ji kunya!

Daga IBRAHIM YAYA Ƙasar Sin daya ce tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar Ƙasar Sin, ita ce kaɗai halastacciyar gwamnati dake wakiltar ƙasar Sin. Haka kuma wanzuwar ƙasar Sin daya tilo a duniya, ita ce babbar manufar da ƙasashen duniya suka amince da ita, kana shi ne tushen siyasa na raya hulda tsakanin Sin da duk ƙasashen da suka ƙulla ko ma suke son ƙulla alaƙa da ƙasar Sin. Duk da cewa ƙasar Amurka na daga cikin ƙasashen da suka amince da wannan manufa, baya ga sanarwoyi uku da ƙasashen biyu suka aminta da su a kan alaƙar dake…
Read More
Xi Jinping ya gana da Michelle Bachelet

Xi Jinping ya gana da Michelle Bachelet

Daga CMG Hausa Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gana da babbar jami’ar hukumar MƊD mai lura da kare haƙƙoƙin bil adama Michelle Bachelet ta kafar bidiyo a yau Laraba a nan birnin Beijing. A yayin ganawar, Xi Jinping ya yi maraba da ziyarar Bachelet a ƙasar Sin, kuma ya nuna cewa, ƙasar Sin tana son aiwatar da shawarwari, da haɗin gwiwa tare da dukkan sassan duniya bisa daidaito da mutunta juna, don sa ƙaimi ga bunƙasuwar ayyukan kare haƙƙin bil'adama na ƙasa da ƙasa, tare da amfanar jama'ar ƙasashe daban daban. A cewarsa, yanzu haka abu mafi mahimmanci shi…
Read More
Wani kamfanin ƙasar Sin ya ƙaddamar da gidauniyar tallafawa al’umma a ƙasar Saliyo

Wani kamfanin ƙasar Sin ya ƙaddamar da gidauniyar tallafawa al’umma a ƙasar Saliyo

Daga CMG HAUSA Kamfanin “Leone Rock Metal Group” na kasar Sin, mai aikin hakar ma’adanai a ƙasar Saliyo, ya sanar da ƙaddamar da gidauniyar bunƙasa ci gaban al’ummar ƙasar. Kamfanin ya ce zai rika keɓe kaso ɗaya bisa ɗari na ribar da yake samu a duk shekara, wajen tallafawa al’ummun gundumar Tonkolili, dake lardin arewacin ƙasar inda yake gudanar da ayyukansa. Da yake ƙarin haske game da hakan yayin ƙaddamar da gidauniyar, babban jami’in kamfanin Zhao Ting, ya ce har kullum kamfaninsa a shirye yake, da ya ba da gudummawa ga manufar raya masana’antun ƙasar Saliyo, tare da bunƙasa rayuwar…
Read More
Ko kiyaye ‘yanci ya fi kare rayukan jama’a muhimmanci?

Ko kiyaye ‘yanci ya fi kare rayukan jama’a muhimmanci?

Daga AMINA XU Abokaina, yau “duniya a zanen MINA” na mai da hankali kan haƙiƙanin ma’anar‘yanci? Tun kafuwar ƙasar Amurka, aka gabatar da “Sanarwar samun ‘yanci”, inda aka nanata cewa, haƙƙin tabbatar da rayuka, da neman ‘yanci da kuma alheri, haƙƙin ne na daukacin Bil Adama. Rayukan jama’a shi ne na farko, amma ‘yan siyasar Amurka suke nacewa ga tsattsauran ra’ayi game da ‘yanci, ta rashin mayar da hankali kan rayukan jama’a tun bayan ɓarkewar cutar COVID-19, inda mutane fiye da miliyan ɗaya suka mutu sakamakon annobar, ko wannan shi ne haƙiƙanin ma’anar ‘yanci? Mai zana: Amina Xu
Read More
Ziyarar Michelle Bachelet shaida ce cewa ƙasar Sin ba ta da abun ɓoyewa

Ziyarar Michelle Bachelet shaida ce cewa ƙasar Sin ba ta da abun ɓoyewa

Daga CMG HAUSA Batun kare haƙƙin dan Adam batu ne mai muhimmanci ga al’ummar duniya. Sai dai, wasu na fakewa da shi wajen yayata manufarsu da ingiza rikici da ta da zaune tsaye. A jiya ne shugabar hukumar kare haƙƙin dan Adam ta MDD, Michelle Bachelet ta fara ziyara a ƙasar Sin, inda za ta ziyarci lardunan Guandong da kuma jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta. Ƙasar Sin ta shafe shekaru da dama tana fuskantar suka daga ƙasashen yamma ta hanyar ruruta batun kare haƙƙin dan Adam a ƙasar, musammam ma a jihar Xinjiang. Ƙasar Sin ta sha…
Read More
Masanin Zambiya: Takunkumin ƙasashen Yamma na haifar da illa ga tattalin arzikin duniya

Masanin Zambiya: Takunkumin ƙasashen Yamma na haifar da illa ga tattalin arzikin duniya

Daga CMG HAUSA Kwanan nan ne a yayin da yake zantawa da kafar CMG, shahararren masanin siyasa na ƙasar Zambiya, Neo Simutanyi ya ce, Rasha, babbar ƙasa ce dake fitar da alkama da makamashi, kuma irin takunkuman da Amurka da sauran wasu ƙasashen yammacin duniya suka sanya mata, sun riga sun haifar da mummunar illa ga tattalin arziki da rayuwar al’ummar duk duniya. Mista Simutanyi ya bayyana cewa, duba da takunkuman da aka ƙaƙƙaba mata, Rasha ta ƙasa halartar harkokin kasuwancin ƙasa da ƙasa, kana, ba za ta iya fitar da wasu manyan hajojinta zuwa kasuwannin duniya ba. Rikicin Rasha…
Read More
Labarin Xi Jinping da mahaifinsa

Labarin Xi Jinping da mahaifinsa

Daga CMG HAUSA Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya ce “Ina fatan ƙara koyon kyawawan ɗabi’u masu daraja daga mahaifina”. Mahaifinsa Xi Zhongxun, “wani jagoran al’umma ne wanda ya samo asali daga al’umma”. Ya kan ce shi da ne na manomi, wanda har kullum ya kan maida shi kansa a matsayin ɗaya daga cikin al’umma. Duk wanda ke ƙaunar al’umma da samar musu da alheri, al’umma za su maida shi tamkar dan uwansu. Samo asali daga al’umma, da kuma sake dawowa cikin al’umma, shi ne ainihin buri na farko na Xi Jinping da na mahaifinsa. A lokutan juyin juya hali…
Read More
Kamfanonin Amurka sun ci riba yayin da ake fama da wahalar hauhawar farashin abinci

Kamfanonin Amurka sun ci riba yayin da ake fama da wahalar hauhawar farashin abinci

Daga CMG HAUSA Abokaina, a wajenku, farashin kayayyakin abinci ya karu? Yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, da takunkuman da ƙasashen yamma suka ƙaƙaba wa Rasha, sun dakatar da cinikin takin zamanin da ake samarwa a ƙasashen Rasha da Belarus, lamarin da ya sa kuɗin da ake kashewa a aikin gona ya ƙaru. Baya ga wannan batu, yadda Ukraine da Rasha suka dakatar da aikin fitar da alkama da masara zuwa ƙasashen waje, sun sa farashin kayayyakin abinci na ƙasashe daban daban ya ƙaru sosai. Yanzu a ƙasar Masar, farashin burodi ya karu da kashi 50%. Yayin da…
Read More
Wang Yi ya halarci bikin ƙaddamar da taron shekara-shekara na ESCAP karo na 78 ta kafar bidiyo

Wang Yi ya halarci bikin ƙaddamar da taron shekara-shekara na ESCAP karo na 78 ta kafar bidiyo

Daga CMG HAUSA Yau ne, mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kuma ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya halarci bikin ƙaddamar da taron shekara-shekara na hukumar tattalin arziki da zaman takewar al’umma ta yankin Asiya da tekun Pacifik ta MƊD wato ESCAP karo na 78 ta kafar bidiyo a birnin Guangzhou, fadar mulkin lardin Guangdong dake kudancin ƙasar Sin, inda ya gabatar da jawabi. Cikin jawabinsa, Wang Yi ya bayyana cewa, ya dace a hada kai domin gina kyakkyawar makomar ƙasashen yankin Asiya da tekun Pacifik, ta hanyar ɗaukar matakai uku, na farko, nacewa kan manufar kiyaye zaman lafiya da…
Read More