29
May
Daga CMG HAUSA Ranar 29 ga watan Mayu, ranar ma’aikatan kiyaye zaman lafiya na ƙasa da ƙasa ce karo na 20. Alƙaluman ma’aikatar tsaron ƙasar Sin sun nuna cewa, a cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce, sojojin ƙasar Sin kusan dubu 50 sun shiga ayyuka guda 25 na MƊD na kiyaye zaman lafiya baki daya. Ƙasar Sin ta ɗauki hakikanin matakai wajen kiyaye zaman lafiyar duniya, ta zama ƙasa ta farko wadda ta fi tura sojojin wanzar zaman lafiya, cikin ƙasashe 5 da ke da kujerun dindindin cikin kwamitin sulhu na MƊD. Cikin shekaru fiye da 30 da…
