Kasashen Waje

Afirka ta Kudu ta fasa shirin yi wa ‘yan ƙasar rigakafin korona

Afirka ta Kudu ta fasa shirin yi wa ‘yan ƙasar rigakafin korona

Daga AISHA ASAS Ƙasar Afirka ta Kudu ta ce ta fasa shirin yi wa 'yan ƙasar allurar rigakafin cutar korona da ta so somawa bayan da ta gano cewa gwajin maganin AstraZeneca jab da ta yi ya kasa yaƙar nau'in cutar da ya bayyana a ƙasar. Afirka ta Kudu ita ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa harbuwa da cutar a faɗin nahiyar Afirka, inda ta so soma aiwatar da shirin yi wa 'yan ƙasar allurar rigakafin korona da ta mallaka daga AstraZeneca da Oxford. A cewar Ministan Lafiyar ƙasar Zweli Mkhize, "Mun dakatar da rigakafin na wucin-gadi har sai…
Read More
Cutar Korona: Abu Dhabi ta haramta tarurrukan shaƙatawa da na bukukuwa

Cutar Korona: Abu Dhabi ta haramta tarurrukan shaƙatawa da na bukukuwa

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani mataki na yaƙi da yaɗuwar annobar korona a Abu Dhabi, Kwamitin Kula da Agajin Gaggawa, rikice-rikice da Ibtila'i na Abu Dhabi ya sanya dokar haramta tarurrukan shaƙawata da na bukukuwa a faɗin birnin sai dai ɗan abin da ba za a rasa ba. Kwamitin ya ce daga ranar 7 ga Fabrairun 2021, an taƙaita adadin mutane da aka amince su halarci taron bikin aure da na zumunta zuwa mutum 10, sannan mutum 20 game da tarurrukan da suka shafi jana'iza da zaman makoke. Haka nan an taƙaita yawan mutanen da aka yarda su gudanar…
Read More
Myanmar: An maka Suu Kyi a kotu

Myanmar: An maka Suu Kyi a kotu

Daga FATUHU MUSTAPHA Rahotanni daga ƙasar Myanmar sun tabbatar da cewa an gurfanar da jagorar Myanmar, Aung San Suu Kyi gaban kotu a Larabar da t gabata, kwanaki biyu bayan tsare ta da sojojin da suka kifar da gwamnatin ƙasar suka yi. Kazalika, bayanai sun ce, kiraye-kirayen tada ƙayar baya don nuna adawa da juyin mulkin ƙasar sai ƙaruwa suke. Ƙasar Myanmar da ke Kudu maso gabashin nahiyar Asiya ta sake faɗawa cikin mulkin soji ne bayan da wasu gungun sojoji suka damƙe jagororin mulkin farar hula a Litinin da ta gabata, lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin dimokraɗiyyar ƙasar…
Read More
Myanmar: Magoya baya sun buƙaci a sako Suu Kyi da sauransu

Myanmar: Magoya baya sun buƙaci a sako Suu Kyi da sauransu

Daga WAKILIN MU 'Yan jam'iyyar National League for Democracy a ƙasar Myanmar, sun yi kira da a sako Aung San Suu Kyi tare da sauran jagororinsu da aka tsare a Talatar da ta gabata. Suna masu bayyana juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi a ƙasar a matsayin al'amari da ya yi wa tarihin sojin ƙasar tabo mara kyau. Da sanyin safiyar Litinin da ta gabata sojoji suka kama Suu Kyi da ta kasance shugabar jam'iyyarsu tare da shugaban ƙasar, Win Myint. Bayan juyin mulkin, ba tare da ɓata lokaci ba sojojin suka naɗa wani tsohon janar, Min Aung Hlaing,…
Read More
China ta haramta wa ɗaliban firamare shiga aji da waya

China ta haramta wa ɗaliban firamare shiga aji da waya

Daga FATUHU MUSTAPHA Kasar China ta sanar da ɗaukar matakin haramta wa ɗalibai 'yan firame da na sakandare yin amfani da wayoyin salula a cikin aji. China ta ce, ta ɗauki wannan mataki ne domin kare ɗaliban daga fitinar intanet da kuma 'TV game' da kan hana ɗalibai maida hankali kan karatu yadda ya kamata. A wata takardar sanarwa da Ma'aikatar Ilimin ƙasar ta raba wa makarantu a Litinin da ta gabata, ma'aikatar ta ce daga yanzu ba a yarda ɗlibai a makarantun firamare da sakandare su riƙa amfani da wayoyi a aji ba. Tana mai cewa, "Duk ɗalibin da…
Read More
China: An cafke mutum 80 masu haɗa jabun rigakafin cutar korona

China: An cafke mutum 80 masu haɗa jabun rigakafin cutar korona

Daga WAKILIN MU Rahotanni daga ƙasar China sun nuna hukumomin ƙasar sun cafke wasu mutum 80 bisa zarginsu da harkar haɗa jabun maganin allurar rigakafin cutar korona. Wani kamfanin dillancin labarai na ƙasar, Xinhua ya ruwaito cewa, ana zargin tun a watan Satumban da ya gabata waɗanda lamarin ya shafa suka soma harkar haɗa jabun rigakafin korona tare da sayar wa mutane da sunan magani mai inganci. Hukumomin ƙasar sun ce, jabun rigakafin korona guda 3000 suka kama waɗanda aka yi aikin haɗawa a sassa daba-daban a ƙasar. Kafin wannan lokaci, China ta samar da allurar rigakafin cutar korona da…
Read More
An yanke wa dan Turkiyya shekaru 1,075 a kurkuku

An yanke wa dan Turkiyya shekaru 1,075 a kurkuku

Daga Umar Mohammed Gombe Wata Kotu a Istanbul na kasar  Turkiyya ta daure shugaban wata kungiyar asiri mai suna Adnan Oktar shekaru sama da 1,000 a bisa samun sa da aikata wasu laifuka 10, a cewar wata majiyar shari’a a kasar. An kama Adnan Oktar mai shekaru 64 ne a shekarar 2018, a wani samame da jami’an tsaron kasar suka kai a daidai lokacin da suke tsaka da miyagun laifuka, inda aka kama da yawa daga mabiyan sa wadanda yawancin su mata ne. Ana tsare da shi tun watan Yunin 2018 a matsayin wani bangare na fatattakar kungiyar sa da…
Read More
Kotun Kolin Amurka ta tabbatar wa Biden nasarar zabe

Kotun Kolin Amurka ta tabbatar wa Biden nasarar zabe

Daga Umar M. Gombe Kotun Koli na Amurka ta kawo karshen dogon takaddamar da ya dauki lokaci ana yi game da zaben shugaban kasa a kasar tun a watan Nuwamba, inda ta tabbatar wa dan takarar shugaban kasa na Democrat Joe Biden nasara. A cikin hukuncin da ta yi ba ranar Juma'a, kotun kolin ta kori karar da Shugaba Donald Trump ya shigar game da zargin tafka magudin zabe da aka yi a Pennsylvania da kuma jihohi uku na kasar. Jihohin hudun sun gabatar da shaidu gaban kotun, inda kuma suka bukaci alkalan kotun da su yi watsi da karar,…
Read More