03
Dec
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mataimakin Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya sanar da sauya wajen ɗaurin auren ƴarsa daga Jihar Kano zuwa birnin tarayya Abuja. Hakan na zuwa ne sakamakon sanarwar da wasu matasan Arewa suka fitar don hana sanatoci shiga kowacce jiha ta Arewa, tare da cewa matukar suka yi kunnen ƙashi suka shigo, to za su yi musu ruwan duwatsu, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Hakan ba zai rasa nasaba da fusatar da al’ummar Arewacin Nijeriya suka yi ba kan kudirin dokar sauya fasalin haraji da ake kallon jihar Lagos ce za ta fi cin…
