Labarai

Yadda za mu bi da sabon ƙudirin harajin Tinubu – Majalisar Dattawa

Yadda za mu bi da sabon ƙudirin harajin Tinubu – Majalisar Dattawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce majalisar dokokin ƙasar za ta gudanar da muhawara a fili kan ƙudirin gyara harajin shugaban ƙasa Bola Tinubu a gabanta domin jin ra’ayin ’yan Nijeriya. Adaramodu, ya ce galibin waɗanda ke sukar ƙudirin a kafafen yaɗa labarai ba su san haƙiƙanin amfanin harajin ba, kuma suna tunani ne bisa aƙidar cewa duk wani haraji zai ɗora wa mutane nauyi, ya ce, “Ban ga wani abu da zai kawo koma baya a cikin ƙudirin gyara harajin ba.” Sanata mai wakiltar mazaɓar Ekiti ta Kudu ya…
Read More
Ban taɓa sanin ka roƙi Abacha kada ya kashe ni ba – Obasanjo ga Gowon

Ban taɓa sanin ka roƙi Abacha kada ya kashe ni ba – Obasanjo ga Gowon

Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya mayar da martani ga tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), wanda ya ce ya roƙi marigayi Janar Sani Abacha kada ya kashe shi. Obasanjo ya kasance cikin waɗanda aka kulle a lokacin mulkin Abacha kan zargin yunƙurin juyin mulki. Da yake magana a bikin Kirsimeti na haɗin kai na Plateau Interdenominational Unity Christmas Carols da Praise Festival da aka gudanar a Dandalin Addu’a na Umarni Goma a Du, Jos ta Kudu, a ƙarshen mako, Gowon ya bayyana cewa ya rubuta wa Abacha wasiƙa, yana masa nasiha cewa Allah ya ba shi mulki…
Read More
Majalisar Wakilai ta dakatar da tattaunawa kan ƙudirin dokokin gyaran haraji

Majalisar Wakilai ta dakatar da tattaunawa kan ƙudirin dokokin gyaran haraji

Daga USMAN KAROFI Majalisar Wakilan Nijeriya ta ɗage tattaunawa kan muhimman dokokin gyaran haraji da ake taƙaddama akansu har sai wani lokaci. Dokokin huɗu sune dokar harajin Nijeriya ta 2024, dokar gudanar da haraji, dokar kafa hukumar haraji ta Nijeriya da kuma dokar kafa kwamitin haɗin gwiwa na haraji sun samu suka daga ƙungiyoyi daban-daban, ciki har da ƙungiyar gwamnonin Arewa, majalisar sarakunan gargajiya, kwamitin tattalin Arziki na Ƙasa, da kuma ƙungiyar dattawan Arewa. Kwamitin tattalin arziki na ƙasa, wanda ya ƙunshi mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni, ya buƙaci shugaba Bola Tinubu ya janye dokokin tare da ba da damar…
Read More
Atiku da Obi sun musanta ganawa don yin takara tare a 2027

Atiku da Obi sun musanta ganawa don yin takara tare a 2027

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a 2023, Peter Obi, sun musanta jita-jitar cewa suna tattaunawa kan haɗa kai don tsayawa takara a zaɓen 2027. Wannan ya biyo bayan hotunan Atiku da Obi da aka gani suna tare yayin karin kumallo a gidan Atiku da ke Jihar Adamawa, wanda ya yaɗu a shafukan sada zumunta. Atiku ya wallafa bidiyon ganawar a shafinsa na X ranar Asabar, inda aka nuna su tare da wasu mutane suna zaune a teburin cin abinci. Mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyana cewa…
Read More

Yadda na yi wa Abacha magiya don kada ya aiwatar da hukuncin kisa kan Obasanjo – Gowon

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Shugaban mulkin Soji, Yakubu Gowon ya bayyana yadda ya roƙi marigayi Sani Abacha kan ya ƙyale Obasanjo da rai. A shekarar 1995 ne gwamnatin Abacha ta kama Obasanjo bisa zarginsa da laifin shirya juyin mulki. Daga bisani a shekarar 1998 aka sako tsohon shugaban ƙasar Shekara ɗaya bayan haka ne, Obasanjo ya zama shugaban ƙasa a ƙarƙashin jami'yyar PDP. A lokacin da ya ke magana a taron haɗin kan kiristoci game da bikin Kirismas a Jos, Gowon ya hakaito yadda ya rubuta saƙo ga Abacha akan rayuwar Obasanjo, ya na mai cewa ya shiga ƙunci…
Read More
Albashi: Wasu jihohi sun janye daga shiga yajin aikin Ƙungiyar Ƙwadago

Albashi: Wasu jihohi sun janye daga shiga yajin aikin Ƙungiyar Ƙwadago

Daga USMAN KAROFI Akwai alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta shirya yi a ranar 1 ga Disamba na iya samun cikas, bayan da wasu rassan ƙungiyar na jihohi suka bayyana cewa ba za su shiga cikin wannan yajin aikin ba. Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi na ₦70,000 ga ma’aikatan Nijeriya a watan Yuli, kuma ya yi alƙawarin sake duba albashin duk bayan shekaru uku. Yawancin jihohi sun amince da biyan fiye da ₦70,000, inda jihohin Legas da Ribas suka ba da mafi girman albashi…
Read More

An yanke wutar lantarkin Jami’ar ABU ɗungurugum

Daga BELLO A. BABAJI Hakan na zuwa ne sakamakon rashin biyan kuɗin wuta da Jami'ar ta Ahamadu Bello dake Zariya ta gaza yi. Lamarin ya auku ne tun ranar Alhamis, 28 ga watan Nuwamba inda Kanfanin raba wutar lantarki na Jihar Kaduna ya katse wutar jami'ar. Acikin wata takarda da ABU ta fitar, ta bayyana wa malamai da ɗalibai cewa ta na iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta biya kuɗin wutar da ake bin ta. Jami'ar ta shiga halin tsaka-mai-wuya ne tun farkon shekarar nan bayan da aka ƙara kuɗin wuta, kamar yadda ya ke ƙunshe a cikin takardar. Premium…
Read More

Inganta rayukan al’ummata na saka a gaba – Sen. Yari

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazaɓar Zamfara ta Yamma, Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar, ya bayyana aniyarsa ta samar da ababen more rayuwa ga al’ummar mazaɓarsa da nufin rage zaman banza musamman a tsakanin matasa. Sanata Yari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji), Shugaban kwamitin yaɗa labaransa na ƙungiyar siyasa, ya fitar a ranar Asabar. Ya ce, "Hakan zai taimaka matuƙa wajen hana su shiga wasu munanan ɗabi'u dake haifar da ƙara tabarbarewar tsaro a cikin al'umma." Sanarwar ta bayyana cewa, Sanatan ya faɗi haka…
Read More

Gwamnatin Jigawa za ta fara hukunta masu yin ba-haya a bainar jama’a

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Gwamnatin Jihar jigawa tace za ta Gina banɗakuna a kasuwanni da tashohin mota, a ƙoƙarinta na yaƙi da ba-haya a bainar jama'a da wasu ke yi. Kwamashinan ruwa na jihar, Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa ya bayyana haka a wajen bikin ranar tsafta da wanke hannu ta duniya da ya gudana a makarantar kiwon lafiya ta Jahun. Kakakin Majalisar dokokin jihar Alh. Haruna Aliyu Ɗan Gyatin ya wakilci Gwamna Umar Namadi a yayin taron ƙaddamar da banɗakuna da Hukumar Albarkatun Ruwa ta gina a makarantar. Hannun Giwa ya ce irin waɗannan banɗakuna, gwamnati ta…
Read More
Atiku ya karɓi baƙuncin Peter Obi a Adamawa

Atiku ya karɓi baƙuncin Peter Obi a Adamawa

Daga USMAN KAROFI Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya karɓi bakuncin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, a gidansa da ke Jihar Adamawa. Atiku ya bayyana wannan a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafin X a ranar Asabar. A rubutun da ya yi, ya ce: “Lokacin karin kumallo tare da abokina, Peter Obi.’” A bidiyon, an ga manyan shugabannin biyu, tare da wasu mutane, zaune a kan tebur suna shirin cin abinci. Wannan ba shi ne karo na farko da suka haɗu bayan zaɓen 2023 ba, domin sun gana…
Read More