Labarai

Gwamnati za ta saurari koken mutane kan sabon daftarin haraji

Gwamnati za ta saurari koken mutane kan sabon daftarin haraji

Daga NASIR USMAN KAROFI a Abuja Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, za ta saurari koke-koken jama’a kan sabon ƙudirin haraji da ta miƙa gaban Majalisar Dokoki ta Ƙasa. Idris ya faɗi hakan ne a wata sanarwa da ya fitar yau, inda ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya umurci ma’aikatar shari’a da ta yi aiki tare da Majalisar Tarayya kan ƙudirin gyaran harajin. Bugu da ƙari ministan ya ba da tabbacin cewa za a warware matsalolin da ake da su a ƙudirin, kuma babu ƙamshin gaskiya kan zargin cewa…
Read More

Boma-boman da ƴan bindiga suka sake dasawa a babbar hanyar Zamfara sun hallaka matafiya

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne, ƴan bindinga suka sake dasa waɗansu boma-bomai a babbar hanyar Ɗan-Sadau zuwa Gusau a Jihar Zamfara, waɗanda suka yi sanadiyyar mutuwar matafiya da dama. Wasu hotunan da kafafen labarai suka wallafa sun nuna yadda mutane suke zube a gefen titi bayan fashewar boma-boman. Wasu mazauna yankin Ɗan-Sadau sun bayyana wa manema labarai cewa suna zargin ƴan bindiga ne suka dasa boma-boman a titin garin wanda ya haɗe shi da wasu sassan jihar. Wani mai suna Abdullahi Ɗan-Sadau ya ce wata mota ƙirar Volkswagen Golf 3, ta haye kan wani bom da aka…
Read More

Ƙudirin gyaran haraji: Majalisar Dattawa ta umarci kwamiti ya dakata da aiki, ta samar da wani don magance matsalolin da ke ciki

Daga BELLO A. BABAJI Shugabancin Majalisar Dattawa ta umarci kwamitinta na kuɗi da ya dakatar da aiki akan ƙudirin neman gyaran haraji har zuwa bayan kammala babban zama da Antoni Janar na Ƙasa, AGF. Mataimakin shugaban majalisar, Sanata Barau Jibrin ya sanar da hakan a yayin zaman majalisar, a ranar Laraba inda ya ce an samar da kwamiti na musamman don warware matsalolin da suka haifar da muhawara acikin al'ummar ƙasa game da ƙudirin. A ranar Alhamis ne kwamutin zai gudanar da zaman tattauna batun don samar da mafita game da muhawarar da ƴan majalisa da masu-ruwa-da-tsaki suke yi a…
Read More
Afrika ta Kudu ta sassauta dokokin biza ga ‘yan Nijeriya

Afrika ta Kudu ta sassauta dokokin biza ga ‘yan Nijeriya

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta sanar da sauƙaƙa tsarin neman biza ga 'yan Najeriya masu sha'awar yawon shaƙatawa da kasuwanci, inda yanzu za su iya nema ba tare da miƙa fasfo ba. Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya bayyana hakan a ranar Talata yayin buɗe zaman taron haɗin gwiwa na Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 11 (BNC) a birnin Cape Town, wanda Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya halarta. A cewar wata sanarwa daga mai ba Shugaban Najeriya shawara Bayo Onanuga, Shugaba Ramaphosa ya ce an sauƙaƙa tsarin neman biza don ba da damar tafiye-tafiye ga masu…
Read More
Hayaniya ta kaure a Majalisar Tarayya kan ƙudurin gyaran dokar haraji

Hayaniya ta kaure a Majalisar Tarayya kan ƙudurin gyaran dokar haraji

Majalisar Wakilai ta Tarayya ta fuskanci yanayi mai cike da hayaniya yayin da ɗan majalisa daga Jihar Ekiti, Akin Rotimi, ya taɓo batun ƙudurin gyaran haraji da aka gabatar wa majalisa. Rotimi, a lokacin da yake gabatar da wani rahoto, ya bayyana kansa a matsayin ɗan majalisa daga Ekiti, jihar farko da ta amince da ƙudurin gyaran haraji. Wannan furuci ya haifar da cece-kuce yayin zaman majalisar. A lokacin da ya ce, “Ni ɗan Jihar Ekiti ne, jihar farko da ta amince da ƙudurin gyaran haraji,” mambobin majalisa sun yi ihu suna cewa, “A’a, ba haka ba.” Wannan ya sa…
Read More
Ranar masu buƙata ta musamman: Mun ware aji don koya masu Ilimin fasahar sadarwa – CITAD

Ranar masu buƙata ta musamman: Mun ware aji don koya masu Ilimin fasahar sadarwa – CITAD

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Cibiyar fasahar sadarwa da cigaban al’umma (CITAD) ta yi bikin ranar tunawa da masu buƙata ta musamman da ake gudanarwa duk ranar 3 ga watan Disambar kowace shekara, da ya gudana yau a cibiyar CITAD da ke Kano. Shugaban Cibiyar Fasahar sadarwa da cigaban al'umma ta CITAD wanda jami’in shirye-shirye na Cibiyar, Mal. Isah Garba ya wakilta ya bayyana cewa, muhimmancin ranar ne ya sa CITAD ta shirya taron domin tattauna matsalolin matune masu buƙata ta musamman da kuma shawarwari akan yadda za a magance matsalolin na su. "CITAD ba wai kawai mun shirya taron…
Read More
Sarkin Katsina ya bada shawara yadda Arewa za ta dawo da martabarta

Sarkin Katsina ya bada shawara yadda Arewa za ta dawo da martabarta

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman ya ce Arewa ba za ta taɓa komawa yadda take ba sai al'umma da shugabanni sun so junan su tare da haɗa kai wajen cigaban yankin. Sarkin ya faɗi haka a lokacin da sabon Maraɗin Katsina Hakimin kurfi Ach Mansir Ahmadi kurfi da tawagarsa su ka kaiwa sarkin ziyarar godiya a fadar Sarkin. "Allah na tare da mu idan muka ƙaunaci junan mu, kuma mu aikata alheri" inji sarkin. Ya bayyana ƙasar Kurfi a matsayin gidan sa na biyu kuma shi marigayi Maraɗin Katsina mutum ne fitacce…
Read More

Al’umma sun shiga ɗar-ɗar bayan ƴan bindiga sun dasa boma-bomai a babbar hanyar Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Mutane sun shiga fargaba a yankin Masarautar Ɗan-Sadau dake ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara sakamakon samun labarin cewa ƴan bindigar da suka addabe su sun fara amfani da boma-bomai wajen ayyukansu. Wani mazaunin yankin mai suna Bello Ɗan-Sadau ya bayyana cewa, sabon salon da ƴan ta'addar ke amfani da shi abu ne mai matuƙar haɗari. Ya ce ƴan ta'addar sun yi yunƙurin kai hari ne a ƙauyen Ƴar Galadima a safiyar ranar Lahadi, saboda haka ne suka dasa boma-boman don kare ɗaukin da jami'an tsaro ka iya kawo musu. Ɗan-Sadau ya ƙara da cewa, an…
Read More
Tinubu ya miƙa wuya: Ya umarci majalisa da Ma’aikatar Sharia su yi duba ga sabon ƙudirin haraji

Tinubu ya miƙa wuya: Ya umarci majalisa da Ma’aikatar Sharia su yi duba ga sabon ƙudirin haraji

Daga USMAN KAROFI Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Shari’a ta tarayya da Majalisar Dokoki ta Ƙasa da su duba ƙorafe-ƙorafe da ake yi kan sabbin ƙudirorin gyaran haraji da ya gabatar wa majalisa. Wannan ya biyo bayan suka da cece-kuce da ƙudirorin suka jawo, musamman daga wasu gwamnonin jihohi, inda daga yankin Arewa ake samun mafi yawan adawa. Wasu daga cikin masu sukar ƙudirorin sun bayyana cewa dokokin na da illa ga yankin Arewa, yayin da wasu ke cewa za su ƙara jefa 'yan Nijeriya cikin talauci. Don magance wannan matsalar, Shugaba Tinubu ya umarci Ma’aikatar Shari’a ta…
Read More
Gwamna Dauda Lawal ya sha alwashin kare ‘yancin ɓangaren shari’a

Gwamna Dauda Lawal ya sha alwashin kare ‘yancin ɓangaren shari’a

Daga USMAN KAROFI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa 'yancin ɓangaren sharia da kuma samar da adalci cikin gaggawa a jihar. Gwamnan ya yi wannan jawabin ne ranar Litinin, yayin buɗe wani taron horaswa na musamman ga alƙalai, rajistran kotu da ma'aikatan kotu a babban kotun jihar da ke Gusau. A cewar kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, taron ya bai wa mahalarta damar duba nasarori da ƙalubale a ɓangaren shari'a tare da tsara sabbin hanyoyin da za a bi wajen inganta ayyukan kotu. Gwamnan ya yaba wa shugabar alƙalan jihar, Mai Shari’a Kulu Aliyu saboda…
Read More