Labarai

‘Yan sanda sun cafke ma’aikacin banki da ya saci N18m ta ATM a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda a Katsina sun kama wani ma'aikacin banki mai suna Adewale Bolaji Gabriel da ke aiki a reshen bankin Access na garin Daura bisa laifin satar Naira miliyan 18 wanda kuɗi ne na wani kwastoma a bankin. Kakakin ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar wa manema labarai haka a inda ya ce yanzu haka wanda ake zargin ya shiga hannu. Ya ce mataimakin jami'in gudanarwa na bankin ne ya kawo koken wanda ake zargi da haɗa kai da abokinsa wani mai suna David Masioyen da ke aiki a bankin Access reshen…
Read More
Isra’ila na cigaba da kisan Falasɗinawa – Amnesty International

Isra’ila na cigaba da kisan Falasɗinawa – Amnesty International

Daga USMAN KAROFI Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana yaƙin da Isra’ila da Amurka ke yi wa al’ummar Falasɗinawa a matsayin kisan ƙare dangi. A cewar kungiyar, “wannan mummunan al’amari ya kamata ya zama abin farkawa ga al’ummar duniya: wannan shi ne kisan kare dangi. Dole a dakatar da shi yanzu.” Tun daga fara wannan yaƙin a Gaza kwanaki 426 da suka wuce, rahotanni sun nuna cewa mutane 44,466 ne suka rasa rayukansu, tare da 105,358 da suka samu raunuka, yawancinsu mata da yara. Duk da haka, har yanzu dubban mutane suna maƙale ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Rahoton ya kuma bayyana cewa…
Read More
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da shirin tallafawa masu buƙata ta musamman

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da shirin tallafawa masu buƙata ta musamman

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), ta hannun Shirin Abinci na Duniya (WFP), ta sanar da wani sabon shirin samar da kaya da nufin bai wa kamfanonin da masu buƙata ta musamman ke jagoranta. Wannan shirin na daga cikin dabarun tabbatar da daidaito a tsarin samar da kaya ko bada kwangila na Majalisar Ɗinkin Duniya. Shugaban Cibiyar Sayen Kaya na Majalisar Ɗinkin Duniya kuma babban jami’i a WFP, Daniel Kuhe, ya bayyana wannan sabon shiri yayin taron tattaunawa kan damammaki ga masu buƙata ta musamman da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba. Taron ya yi…
Read More
Mataimakin Gwamna tare da wasu fasinjoji sun tsallake rijiya da baya

Mataimakin Gwamna tare da wasu fasinjoji sun tsallake rijiya da baya

Daga RABIU SANUSI a Kano Mataimakin gwamnan Jihar Borno, Umar Kadafur, tare da wasu fasinjojin jirgin Max Air, sun tsallake rijiya da baya sakamakon lalacewar jirgin da suke ciki. Wakilin mu ya rawaito cewa mataimakin gwamnan yana daga cikin mutane 100, da suke cikin jirgin na Max, lokacin da jirgin ya samu matsala sakamakon kamawa da wuta da injin jirgin yayi jim kaɗan bayan tashi daga filin tashi da saukar jiragen saman ƙasa da ƙasa na Maiduguri a jiya Laraba. Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 7 na daren Laraba yayin da jirgin ya ɗauki hanyar zuwa birnin tarayya…
Read More

Sinima ta na ƙarfafa haɗin-kan al’umma – Ministar Al’adu

Daga BELLO A. BABAJI Ministar Ma'aikatar Al'adu, Hannatu Musa Musawa ta ce sinimar haska finafinai ta na ɗaya daga cikin ginshiƙan da ke ƙarfafa haɗin-kan al'ummar ƙasa. A lokacin da ta ke jawabi a bikin finafinan Zuma na Ƙasa da ƙasa (ZUFF) karo na 14 a Abuja, Musawa ta ce fim wani fage ne na musamman da ke inganta haɗin-kai acikin mutanen da suka zo daga ɓangarori daban-daban. Taron ZUFF na wannan shekarar an fara shi tun a ranar 1 ga watan Disamba wanda a yau ne ake ƙarƙare shi, ya bayyana yadda harakar fasaha ta sa sinima ta ƙasaita.…
Read More

Mai yi wa ƙasa hidima ta raba kayan makaranta ga ɗalibai 100 a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wata mai yi wa qasa hidima ta NYSC mai suna Nafisa Umar Hassan, ta bayar da tallafin kayan makaranta ga ɗalibai 100 a makarantar firamare ta ƙaramar hukumar Ɓatagarawa da ke Jihar Katsina. Nafisah mai lamba KT/24A/1178 wadda a halin yanzu ke gudanar da aikin hidimar a Ma’aikatar Muhalli ta jihar, ta raba kayan makarantar ne ga ɗaliban a harabar makarantar. Da take jawabi ga waɗanda suka ci gajiyar tallafin, Nafisa ta ce hakan yana daga cikin tallafi da ƙungiyarta ta tallafawa al'umma ke bayarwa da nufin rage raɗaɗin halin da iyayen yaran ke ciki…
Read More
Netflix ya ƙaryata jita-jitar ficewarsa daga Nijeriya

Netflix ya ƙaryata jita-jitar ficewarsa daga Nijeriya

Daga USMAN KAROFI Kamfanin Netflix ya musanta rahotannin da ke cewa zai bar kasuwar Nijeriya, inda ya jaddada ƙudurinsa na cigaba da zuba jari a masana’antar fina-finai ta ƙasar. Wannan karin haske ya biyo bayan rahotannin da suka yaɗu bayan jawabin wani shahararren ɗan fim, Kunle Afolayan, a lokacin bikin Zuma International Film Festival na 2024. Afolayan ya bayyana cewa Netflix ya soke wasu ayyukan da wasu masu shirya fina-finai suka gabatar kwanan nan, wanda ya sa ake tambayar makomar kamfanin a Najeriya. “Lokacin da muka sanya hannu kan yarjejeniyar fim guda uku da Netflix shekaru uku da suka wuce,…
Read More
Lakurawa na da hannu a harin bom ɗin Zamfara, inji ‘yan sanda

Lakurawa na da hannu a harin bom ɗin Zamfara, inji ‘yan sanda

Daga USMAN KAROFI Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta zargi sabuwar ƙungiyar ta’addanci mai suna Lakurawa da hannu a fashe-fashen boma-bomai da suka auku a hanyoyin ƙauyuka biyu a yankin Ɗansadau, ƙaramar hukumar Maru. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Muhammad Shehu Dalijan, ya bayyana hakan yayin wata hira ta wayar tarho da wakilinmu. A ranar Laraba, News Point Nigeria ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun dasa bama-bamai a hanyar dake tsakanin Ɗansadau da Gusau, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar matafiya. Shaidun gani-da-ido sun bayyana yadda bam ɗin ya hallaka mutane shida tare da jikkata wasu takwas bayan wata mota ƙirar…
Read More
Kamfanin Netflix zai bar Nijeriya

Kamfanin Netflix zai bar Nijeriya

Shahararren kamfanin samar da fina-finai na intanet, Netflix, ya sanar da ficewarsa daga kasuwar Najeriya bayan shekaru shida, sakamakon tsananin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Rahotanni daga Peoples Gazette sun bayyana cewa rashin ƙwarin gwiwa da kamfanin ke samu daga masu biyan kuɗi da kuma matsin lambar darajar naira ya sa dole su yanke wannan shawara. Wani jami’i daga Netflix wanda ya zanta da Peoples Gazette cikin sirri ya bayyana cewa, “Mun rasa yawancin masu biyan kuɗi, kuma sauyin darajar naira da dala ya ƙara mana matsaloli.” Wannan mataki ya biyo bayan ƙarin hauhawar farashi…
Read More

Bankuna sun ƙara adadin cire kuɗi zuwa N50,000

Daga BELLO A. BABAJI Bankuna a Birnin Tarayya Abuja sun ƙara adadin kuɗin da ake iya cirewa zuwa Naira 50,000. Rahotonni sun bayyana cewa bankunan Zenith da GT sun ƙara adadin daga N5,000 a watan da ya gabata. Bankin GT dake hanyar filin jiragen sama a birnin yana biyan kwastomomi N50,000 aciki yayin da yake biyan N20,000 a ATM. Wani jami'i ya ce hakan ya samu ne sakamakon yalwar kuɗaɗe da bankin yake da shi. A ƴan kwanakin nan ne masu POS suke cazar kwastomomi N800 a kowacce N20,000 yayin da suke karɓar N2,000 a N50,000. A ranar Laraba ne…
Read More