24
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Wata dabar ƴan bindiga ta yi nasarar kashe shahararre kuma Kwamandan ƴan bindiga, Kachalla Tukur Sharme a yayin wata ba-takashi a tsakanin su. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce an kashe Sharme ne tare da wasu ƴan dabarsa. Aruwan ya ce, a lokacin da ɓangarorin biyu ke fafatawa, wasu mutane da aka yi garkuwa su sun samu nasarar tserewa daga komar ƴan ta'addar. Ya kuma ce, akwai wasu daga cikin ƴan bindigar da suka samu raunuka, waɗanda a…
