Labarai

Ka rantse da Ƙur’ani ba ka da hannu a ayyukan ta’addanci – Matawalle ga gwamnan Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya yi watsi da zargin da Gwamnan jihar, Dauda Lawal ya yi akan sa na cewa ya na da hannu acikin taimaka wa ta'addanci. Matawalle, wanda shi ne ƙaramin ministan tsaro a Nijeriya, ya ƙalubalanci ƴan siyasa ciki har da Gwamna Dauda kan cewa su rantse da Ƙur'ani ba su da hannu acikin ayyukan ta'addanci da ya addabi jihar. Ya ce, "Ni kaɗai ne gwamnan da ya rantse da Al-Ƙur'ani mai tsarki cewa ba ni da hannu a ayyukan ta'addanci." "Na ƙalubalanci duk ƴan siyasar, har da Janar Ali Gusau da…
Read More
Ina rubutu ne don cika burin mahaifiyata – Fauziyya Sani Jibril 

Ina rubutu ne don cika burin mahaifiyata – Fauziyya Sani Jibril 

Alaƙata da masu karatun littattafaina alaƙa ce mai ban sha'awa da burgewa Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Komar shafin Adabi a wannan mako ta yiwo babban kamu ne daga tekun marubutan adabi, inda wakilin Manhaja Blueprint, Abab Abubakar Yakubu, ya samu nasarar tattaunawa da jajirtacciyar marubuciya, 'yar kasuwa, malama, kuma mawallafiyar waƙoƙin yabon manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW), Malama Fauziyya Sani Jibrin, marubuciyar littafin ɗalibai da wasu da dama, wacce ƙwarewarta wajen rubuta gajerun labarai ya sa ta samun nasarori masu yawa, a gasanni daban-daban na marubuta. Tana daga cikin marubutan onlayin waɗanda baiwarsu da natsuwar su wajen kiyaye ƙa'idojin rubutu…
Read More
Gwamnatin Tinubu ta fi kowacce gwamnati a Nijeriya sauƙin sha’ani ga masu zuba hannun jari – Shettima

Gwamnatin Tinubu ta fi kowacce gwamnati a Nijeriya sauƙin sha’ani ga masu zuba hannun jari – Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada jajircewar Gwamnatin Tarayya wajen samar da yanayin da zai taimaki masu zuba jari. Ya bayyana hakan ne a taron kasuwanci na manyan shuwagabanni na Amurka da Nijeriya. Shekaran farko da aka cire tallafin man fetur wanda ke zama kamar nauyi a wuyan Nijeriya, Shugaban Ƙasa Tinubu ya ɗauki matakin farko na cire tallafin man fetur da haɗa kasuwannin musayar kudi da dama. Shettima ya bayyana haka a wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai Stanley Nkwocha, ya fitar a ranar Litinin. “Na roƙe ku, ku bai wa Nijeriya wata…
Read More
Majalisar dokokin Katsina ta buƙaci akai jami’an tsaro Kankia

Majalisar dokokin Katsina ta buƙaci akai jami’an tsaro Kankia

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar dokoki ta jihar Katsina ta buƙaci akai jami'an tsaro cikin gaggawa a wasu garuruwa da ke ƙaramar hukumar Kankia. Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kankia, Hon Salisu Hamza Rimaye, ya gabatar da ƙudirin a zauren majalisar. Ya buƙaci abokan aikinsa a zauren najalisar su goya masa baya a turawa ɓangaren zartarwa domin a samar da tsaro a wasu garuruwa guda shida da ke ƙaramar hukumar. Garuruwan sun haɗa da Tasha Fanni, Malamawa, Tudun wulli, Walwala, Sukuntuni da Magani. Da yake gabatar da ƙudirin a zauren majalisar ɗan majalisar ya nuna rashin jin daɗinsa…
Read More
Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da wata sabuwar yarjejeniya domin inganta tsarin shugabancin duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da wata sabuwar yarjejeniya domin inganta tsarin shugabancin duniya

 Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Shugabannin duniya sun yi taro a Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar 22 ga Satumba, 2024 don tattabatar da cikakkiyar “yarjejeniya saboda gaba,” wanda ya ƙunshi Yarjejeniyar dijital ta duniya da sanarwa kan ci gaban zamanunnuka masu zuwa. Yarjejeniyar ƙasa da ƙasa mafi fa'ida a cikin shekaru da yawa, wacce ta shafi sabbin fannoni gaba ɗaya da kuma batutuwan da yarjejeniyar ba ta yiwu ba a cikin shekaru da yawa, yarjejeniyar tana da nufin samar da dukkan abubuwa don tabbatar da cewa cibiyoyin ƙasa da ƙasa za su iya ba da gudummawa ta fuskar duniyar da ta…
Read More

An sace babur ɗin ɗan jarida a gidan gwamnatin Bauchi

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Alhamis da ta gabata ne aka sace babur ɗin wani wakilin gidan telebijin na AIT mai suna Damina Yusuf a gidan gwamnatin jihar Bauchi, bayan gayyatar sa zuwa wani taro da aka yi. Ɗan jaridar, wanda ke zama a Bauchi, an gayyace shi ne don ɗaukar rahoton wani shiri na "Renewed Hope Agenda" wanda matar shugaban ƙasa, Misis Remi Tinubu da na gwamnan jihar Bauchi, Hajiya A'isha Bala Mohammed suka shirya don inganta mata a jihar. Jaridar 'WikkiTimes' ta ruwaito cewa, ɗan jaridar ya ce, "an baza jami'an tsaro sosai a lokacin da na…
Read More
‘Yan banga sun yi nasarar kashe makusancin Turji, Kachalla Sani Black

‘Yan banga sun yi nasarar kashe makusancin Turji, Kachalla Sani Black

Ɗan bindigar da ya shahara da sunan Kachalla Sani Black, ya mutu a hannun 'yan banga. 'Yan bangar da suka yi wannan aikin sun kuma bindigu biyu AK-47, kuɗi da ba a bayyana adadin su ba da kuma bindigar PKT. PRNigeria ta kuma tattara cewa 'yan bangar gida suka kashe Kachalla da 'ya'yansa biyu a wani kwantan ɓauna a Magama Mai Rake, a karamar hukumar Maru. Kachalla Sani Black, yana da alaƙa da Bello Turji a ta'addancida ya ke aikatawa. Kuma ya kasance shugaban 'yan bindiga da ya shahara a Chabi, yankin Ɗan Sadau na karamar hukumar Maru. PRNigeria ta…
Read More

Kwanan Bello Turji ya kusa ƙarewa – Janar Musa

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya tabbatar da cewa kwanan nan za su kama shahararre kuma jagoran ƴan bindiga, Bello Turji yayin da jami'ai ke ƙara kusantarsa inda ya ke ɓuya a dazukan Jihohin Sakkwato da Zamfara. A lokacin da ya ke magana a taron bikin cikar shekara 38 na makarantar Kwalejin horo ta sojoji a Kaduna, Janar Musa ya ce maganar kama Turji abu na wani lokaci wanda a halin yanzu hukumomin tsaro na aiki tare wajen ganin ɗan ta'addan ya shiga hannun doka. Ya ce, "Mu na bibiyar Bello Turji. Abu…
Read More
An kashe ɗan bindiga Sharme mai alaƙa da sace ɗaliban Kaduna Baptist

An kashe ɗan bindiga Sharme mai alaƙa da sace ɗaliban Kaduna Baptist

Ɗan bindigar nan da ya shahara da sunan Kachalla Tukur Sharme, wanda aka danganta da sace ɗaliban Bethel Baptist High School 121 a Jihar Kaduna da kuma mutum biyu daga ƙungiyar 'yan bindiga mai adawa, sun mutu a rikicin da ya ɓarke tsakanin dabar su a cikin dajin da ke kewaye da Rijana da Kaso, Jihar Kaduna. A cikin wata sanarwa, kwamishinan kula da harkokin tsaro na cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya ce rikicin, wanda ya faru a ƙarshen makon, ya jikkata 'yan bindiga da dama, yayin da wasu daga cikin waɗanda aka sace suka yi nasarar tserewa…
Read More

Kwamitin sa-ido kan aikin jarida ya ce Daily Trust ta yi kuskure akan labarin Samoa

Kwamitin karɓar Ƙorafe-ƙorafe kan Kafafafen Yaɗa Labarai na Kasa (NMCC), ya fitar da rahotonsa kan taƙaddamar zargin goyon bayan auren jinsi a yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta sanya wa hannu ta Samoa. Kwamitin, wanda gogaggun ƴan jarida da lauyoyi ke yi wa shugabanci, ya ce kamfanin jaridar 'Daily Trust' ya tafka kuskure a wancan labarin akan yarjejeniyar ta Samoa. Binciken ya biyo bayan ƙorafin da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya ta yi akan Daily Trust. Hukumar, a cikin rahotonta mai shafuka 19, ta ce bayan ta binciki ƙorafin gwamnati da kuma martanin da jaridar tayi,…
Read More