Labarai

Za a gudanar da jarrabawa ga shugabannin makarantun gaba da firamare a Katsina

Za a gudanar da jarrabawa ga shugabannin makarantun gaba da firamare a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina za ta gudanar da jarrabawa ga shugabanni da mataimakan su na makarantun gaba da firamare a faɗin jihar. Wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan rashin kataɓus da ɗaliban jihar suka yi a jarabawar NECO na wannan shekara. Kwamishinan ilimi a matakin farko Hajiya Zainab Musawa ta sanar da haka a hira da manema labarai a ofishin ta. Ta ce jarrabawar shi zai taimakawa gwamnati wajen sake naɗa shugabannin makarantun bisa cancanta. Haka kuma kwamishinan ilimin ta sanar da cewa ma'aikatar ta za ta dawo da karatun dare ga duk…
Read More
Hukumar zaɓe ta ɗauki ma’aikata 14,794 domin zaɓen ƙananan hukumomi a Jigawa

Hukumar zaɓe ta ɗauki ma’aikata 14,794 domin zaɓen ƙananan hukumomi a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Jigawa ta ce ta shirya tsaf domin tinkarar zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a ranar 5 ga Oktoba 2024. Shugaban hukumar zaɓen mai zaman kanta Malam Auwalu Harbo ya sanar da haka a wani taron manema labarai da hukumar ta shirya a ofishin ta. Ya ce zuwa lokacin da yake zantawa da manema labaran sun sami adadin jam'iyyu 11 da aka tantance za su shiga zaɓen da za a gudanar a cikin makon gobe. Ya cigaba da cewar nan bada jimawa ba zasu kafe sunayan…
Read More

Yahaya Bello ya maka EFCC a Kotun Ƙoli kan almundahana

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya kai ƙarar Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ga Kotun Ƙoli kan shelanta shi a matsayin wanda ake nema. EFCC ta na tuhumar Yahaya Bello ne da hannu a laifuka 19 bayan zargin sa da hannu a sauya akalar wasu kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 80.2. A ranar Laraba ne aka buƙaci Bello ya halarci babban kotun tarayya don sauron ƙarar da ke kansa. Saidai, a lokacin fara tattaunawa kan batun, tawagar lauyoyin da ke kare Bello ƙarƙashin jagorancin A. M. Adoyi sun…
Read More

Shettima ya nemi a samar da mafita ta dindindin ga yaƙin Gaza

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga shugabannin duniya su samar da mafita ta dindindin game da yaƙin Gaza da ake cigaba da yi. Ya ce, akwai buƙatar al'ummar Palestine su samu ƴanci ganin yadda ake cigaba da ɗaiɗaita su. Shettima, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabin yayin muhawara da shugabannin duniya a taron game da batutuwan da suka shafi al'umma. A ranar 7 ga watan Oktoba, 2023 ne aka fara yaƙin Gaza a ƙasar…
Read More

Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da aniyar Tinubu na yi wa ministocinsa garambawul

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa ta yi wa tawagar ministocinsa garambawul. Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya bayyana hakan wa wakilan Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja inda ya ce gwamnati ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na farfaɗo da tattalin arziƙi wanda al'umma ba ta sani ba. Onanuga, ya ce Shugaba Tinubu ya umarci ministocinsa su ke bayyana wa al'umma ayyukan da ma'aikatu da dama ke yi na inganta ƙasa. A baya ne Tinubu ya sha alwashin yin nazari game da ayyukan ministocin wanda hakan…
Read More
Kotu ta hana jam’iyyu 19 shiga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Kano

Kotu ta hana jam’iyyu 19 shiga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Kano

Daga USMAN KAROFI Babbar kotu a Jihar Kano wanda mai shari'a Sanusi Ado Ma'aji ke jagoranta ta dakatar da aƙalla jam'iyyun siyasa 19 daga shiga zaɓen ƙananan hukumomi a jihar. Umarnin koton kamar yadda hukumar zaɓe ta jihar ta buƙata shine hana jam'iyyun yin katsalandan a zaɓen a ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin kano. Mai ƙara itace hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Kano. Sai kuma waɗanda ake ƙara sun haɗa da jam'iyyu kamar su , People Democratic Party (PDP), Accord Party( AP), All Progressive Congress ( APC) da sauran su. Alƙalin ya ɗage shari'ar zuwa 10 ga…
Read More

Majalisar Dokokin Kogi ta buƙaci Tinubu ya tsige shugaban EFCC kan yunƙurin kama Yahaya Bello

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dokokin Kogi ta yi kira da a tsige shugaban Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), Ola Olukoyede kan nuna rashin ƙwarewa game da batun rashawa da ake tuhumar tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello a kai. An gabatar da hukuncin ne a ranar Litinin a yayin zaman majalisar, a Lokoja babban birnin birnin jihar inda ƴan majalisar suka bayyana samamen da jami'an EFCC suka kai masauƙin gwamnatin jihar da ke Abuja a matsayin cin-fuska ga Gwamnan jihar, Usman Ododo da al'ummar jihar. Hakan na zuwa ne bayan wani kira na gaggawa da Hon.…
Read More

Ta’addanci: Gwamnan Zamfara ya kai ƙarar Matawalle ga Ribaɗu

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ce Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu da Shugaba Bola Tinubu sun san akwai zargin ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle na cewa ya na da hannu acikin ayyukan ta'addanci a jihar. Gwamnan ya ce, ya sanar da NSA da Shugaba Tinubu game da batun tare da gabatar musu da wasu hujjoji. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan Matawalle, wanda tsohon gwamnan jihar ne ya musa batun zargin cewa ya na da alaƙa da ƴan bindiga a jihar. Cikin wata hira da aka yi da Kakakin…
Read More

Alƙali Nyako ta tsame hannu a shari’ar Nnamdi Kanu

Daga BELLO A. BABAJI Mai Shari'a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ta cire kanta a shari'ar shugaba ƴan ƙabilar Igbo (IPOB), Nnamdi Kanu da ke tsare. Hakan na zuwa ne bayan Kanu ya nemi Alƙalin ta janye daga shari'ar tasa. Kanu ya bayyana hakan ne a ranar Talata a lokacin tsaka da ake shari'ar wanda gwamnatin tarayya ke tuhumar sa da laifuka bakwai da ke da alaƙa da ta'addanci. A lokacin da lauyan Kanu, Mista Alloy Ajimakor ke ƙoƙarin neman kotun ta ɗage shari'ar kasancewar ba a bai wa Kanu damar shirya kare kansa ba, sai…
Read More

Raɗɗa ya gwangwaje ma’aikata da kyautuka a bikin cikar Katsina shekaru 37

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Raɗɗa ya bayar da kyautuka ga wasu daga cikin ma'aikatan jihar 14, waɗanda suka fi nuna ƙwazo a yayin gudanar da ayyukansu. Gwamnatin jihar ta ƙaddamar da bayar da kyautukan ne a wurin cin abincin dare da aka shirya albarkacin cikar jihar shekaru 37 da kafuwa. An ƙirƙiri Jihar Katsina ne a lokacin mulkin soji ƙarƙashin shugabancin Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekarar 1987. A yayin da wasu daga cikin ma'aikatan suka samu kyautukan motoci, wasu kuwa sun samu kyautar kuɗaɗe. Waɗanda aka bai wa kyautar motocin sune; Lawal Halilu…
Read More