Labarai

Gwamnatin Tarayya za ta gina tituna 14 a inda ambaliyar ruwa ta yi ɓarna

Gwamnatin Tarayya za ta gina tituna 14 a inda ambaliyar ruwa ta yi ɓarna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Zartarwa ta ƙasa ta amince da aikin gina tituna 14 da gadoji wanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Ekiti da Adamawa da Kebbi da jihar Enugu. Ministan ayyukan, David Umahi ne ya bayyana hakan yayin yi wa manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayani bayan zaman majalisar zartarwar. Ya ce sauran jihohin sun haɗa da Cross Riɓer da Ondo da jihar Osun da Ebonyi da Abia da jihar Imo. Ya ce, an bada aikin kwangilar gina hanyoyin ne ƙari kan kwangilar gyara gadar Gamboru dake Gamboru-Ngala da Kala-Balge a jihar Borno. Minsitan…
Read More
Shari’ar Yahaya Bello: Majalisar Kogi ta nemi Tinubu ya gaggauta tsige Shugaban EFCC

Shari’ar Yahaya Bello: Majalisar Kogi ta nemi Tinubu ya gaggauta tsige Shugaban EFCC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Dokokin Jihar Kogi ta nemi Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta tsige Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede, wanda ta zarga da kawo ruɗani a batun binciken tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello. Sun yi tir da abin da shisshigin kutsawa Gidan Gwamnatin Kogi da ke Abuja, wanda EFCC suka yi har suka yi harbi a cikin gidan. EFCC ta afka cikin Gidan Saukar Baƙi na Gwamnatin Kogi a Abuja cikin makon jiya, domin kamo Yahaya Bello, wanda ke cikin gidan. To sai da ‘yan majalisar sun ce EFCC ta keta doka da ta yi…
Read More
’Yan ta’adda 20 sun dulmuiye cikin ruwa a yunƙurin tsallaka iyakar Nijeriya da Nijar

’Yan ta’adda 20 sun dulmuiye cikin ruwa a yunƙurin tsallaka iyakar Nijeriya da Nijar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kimanin 'yan ƙungiyar Daesh 20 ne suka nutse a ruwa a lokacin da suke ƙoƙarin tsallakawa wani kogi da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar. Lamarin ya faru ne a tsakanin yankin Kafetoa da Bulabulin Gaidam a jihar Yobe a Nijeriya, a cewar wani masani kan yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama. Rahotanni sun ce maharan na kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen Tam da ke jamhuriyar Nijar, kusa da unguwar Kannamma da ke jihar Yobe, inda wata igiyar ruwa mai ƙarfi ta tafi da su, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsu. Makama ya bayyana cewa an…
Read More
El-Rufai ya kwatanta dawo da Sarki Sanusi a matsayin abu mafi muhimmanci a rayuwarsa

El-Rufai ya kwatanta dawo da Sarki Sanusi a matsayin abu mafi muhimmanci a rayuwarsa

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana matuƙar jin daɗin sa na mayar da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na 16. El-Rufa’i ya bayyana haka a matsayin “Ɗaya daga cikin muhimman al’amura a rayuwata” a gare shi, inda ya bayyana muhimmancin wannan mataki. Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata a wurin taron Arewa Tech Fest, taron da ya tattaro shugabannin siyasa da na fasaha domin tattauna ci gaban Arewacin Najeriya. Bikin ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da Gwamnonin jihohin Kano, Katsina, da Zamfara. "Mayar da mai martaba na ɗaya…
Read More
 Ana fama da ƙarancin jami’ai a hukumomin tsaron Nijeriya — Lagbaja

 Ana fama da ƙarancin jami’ai a hukumomin tsaron Nijeriya — Lagbaja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Hafsan Sojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya bayyana damuwar cewa ana fama da ƙarancin jami’ai a hukumomin tsaron Nijeriya. Lagbaja ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron lakca kan mutumin da ya fi fice a shekarar 2024 mai taken, “rawa da gudunmawar rundunar sojin Nijeriya ga ci gaban ƙasa”, wacce Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya da Muhimman Fannonin Ilimi, na Jami’ar Ilori ta shirya. Ya buƙaci kowane ɗan Nijeriya ya shigo a dama da shi a harkar tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar ƙasa a maimakon barin hakan…
Read More
Annobar kwalara ta jefa Jihar Jigawa cikin alhini da zulumi bayan mutuwar mutum 41

Annobar kwalara ta jefa Jihar Jigawa cikin alhini da zulumi bayan mutuwar mutum 41

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wata annobar cutar amai da gudawa, wacce ake kyautata zaton cutar kwalara ce, ta yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 41 a Jihar Jigawa, inda mata da ƙananan yara suka fi kamuwa da cutar. ɓarkewar cutar da ta shafi al'ummomi da dama, ta sa jihar cikin alhini da zulumi. ƙauyen Gatafa da ke ƙaramar hukumar Auyo na daga cikin waɗanda lamarin ya fi shafa, inda aka ƙirga sabbin kaburbura guda 41 da wakilin gidan talabijin na Channels, Sadiƙ Iliyasu, ya yi a maƙabartar ƙauyen. Sauran al’ummomin da cutar ta ɓullawa a garin Auyo sun haɗa da Auyakayi,…
Read More
Man Dangote zai rage farashin sufuri da tsadar abinci, inji shuganan CBN

Man Dangote zai rage farashin sufuri da tsadar abinci, inji shuganan CBN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Olayemi Cardoso ya bayyana cewa, fara jigilar man fetur daga matatar man fetur ta Dangote zai rage farashin sufuri da tsadar abinci a ƙasar. Mista Cardoso ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai a ranar Talata, bayan taron kwamitin tsare-tsaren harkokin kuɗi wato MPC a Abuja. "Kwamitin ya nuna ƙwarin gwiwar cewa samar da man fetur daga matatar man fetur ta Dangote zai taimaka wajen rage farashin kayan masarufi. "Haka kuma zai taimaka wajen rage buƙatun kuɗaɗen ƙasashen waje da ake yi domin shigo da man fetur Nijeriya," inji Cardoso.…
Read More
Muna zaune lafiya tare da sauran ƙabilu a Legas – Mansir Sani

Muna zaune lafiya tare da sauran ƙabilu a Legas – Mansir Sani

Daga DAUDA USMAN a Legas Sarkin al'ummar Hausawa mazauna Unguwar Odugunya barak ta ƙaramar Jukumar Ikorodu dake cikin garin Legas, Alhaji Mansir Sani ɗan asalin ƙaramar hukumar Faskari dake cikin jihar Katsina, ya bayyana cewar su da sauran al'ummar Hausawa mazauna unguwar Ikorodu ta jihar  Legas suna cigaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da sauran ƙabilu mazauna yankin na Legas gaba ɗaya. Sarkin Hausawan na Pdugunya Barak Alhaji Mansir Sani ya yi wannan tsokaci ne jim kaɗan bayan kammala taronsu da waɗansu sarakunan Yarabawa wanda suka saba yi a duk ƙarshen mako domin tattaunawa bisa kan abubuwan…
Read More
Kano ta ciyo bashin biliyan N177.4 daga Faransa don samar da ruwa

Kano ta ciyo bashin biliyan N177.4 daga Faransa don samar da ruwa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta samu rancen Naira biliyan 177.4 daga Hukumar Raya kasar Faransa gina sabbin matatun ruwa a Tamburawa da inganta samar da ruwan sha.  Gwamna Abba ya ce aikin na da nufin inganta hanyoyin samun ruwan sha, duba da ƙaruwar al’ummar jihar cikin hanzari. Abba ya jaddada muhimmancin aikin, wanda ya ce fuskanci tsaiko sakamakon annobar COɓID-19 da sauran ƙalubale, amma yanzu ana sa ran kammala shi nan da shekaru biyu masu zuwa. Ya ce za a gudanar da aikin ne a ƙarƙashin shirin sake fasalin ruwan birane na ƙasa, kuma ma’aikatar…
Read More
Gwamnatin Jigawa za ta kashe biliyan N26.27 domin sayo kayan aikin noma

Gwamnatin Jigawa za ta kashe biliyan N26.27 domin sayo kayan aikin noma

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Umar Namadi na Jihar Jigawa, ta amince da ware kuɗi har Naira N26,274,553,600.00 don sayen tantan ɗin noma guda 300, garmar huɗa guda 300, garmar noma guda 300, garmar ‘disc ridger’ guda 300, bodin tantan (Tipping Trailer) guda 300, injin shuka guda 150, injin shuka shinkafa guda 150, motar girbin amfanin gona guda 40, da kuma na’urar feshin maganin ƙwari guda 80. Haka kuma an ware Naira 263,160,000 don tura ma’aikata 30 zuwa ƙasar Chaina, don samun horo na tsawon watanni uku kan yadda za su riƙa kula da kuma gyaran sababbin na’urorin…
Read More