28
Sep
Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Tsohon Alƙalin Alƙalan Jihar Gombe, Mai Shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga, ya nuna damuwarsa matuƙa game da jinkirin ci gaban aikin haƙo man fetur a rijiyoyin Kolmani da ke masarautar Pindiga a Jihar Gombe da wani ɓangare na Jihar Bauchi. Yayin da yake magana da manema labarai a Gombe ya bayyana muhimmancin wannan aiki, yana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kammala aikin. Mai Shari’a Pindiga ya bayyana cewa aikin Kolmani na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, ta hanyar ƙara samun kuɗaɗen shiga da samar da ayyukan yi ga 'yan…
