Labarai

Nijeriya na asarar Dala Biliyan ɗaya duk wata ga masu fita neman lafiya ƙasashen waje

Nijeriya na asarar Dala Biliyan ɗaya duk wata ga masu fita neman lafiya ƙasashen waje

Bankin Raya Afirka ya bayyana cewa Afirka tana rasa dala tiriliyan 2.4 duk shekara ta fuskar tattalin arziki saboda rashin zuba jari a ɓangaren lafiya, inda Nijeriya ke rasa dala biliyan ɗaya duk wata saboda rashin haramta yawon neman lafiya a ƙasashen waje. AFDB ya tabbatar wa gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, cewa zai taimaka masa wajen haɓaka tattalin arzikin jihar zuwa tattalin arzikin ƙarni na 21, ta hanyar bunƙasa ɓangaren kiwon lafiya a jihar da kuma taimaka wa Nijeriya wajen tsare dala biliyan ɗaya da ake asara duk wata saboda rashin haramta yawon neman lafiya a ƙasashen waje.…
Read More
Ambaliya ta rushe gidaje 321,000 tare da mamaye gonaki a Kebbi

Ambaliya ta rushe gidaje 321,000 tare da mamaye gonaki a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Gwamnatin Jihar Kebbi ta nemi agaji don tallafawa al'ummomin da ambaliyar bana ta lalatawa matsugunai da kuma gonaki. Kwamishinan yaɗa labarai Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi ne ya bayyana haka ranar Juma'ar da ta gabata lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ofishinsa. Kwamishinan ya bayyana cewa kimanin gidaje 328,000 ne suka rushe yayin da gonakin abinci da suka hada da gero, shinkafa, wake, masara, gyada da dai sauransu da yawansu ya kai hekta 858, 000 ruwan ya mamaye. Ya ƙara da cewa gwamnatin Jihar Kebbi tana neman agaji don tallafawa ga…
Read More

Wawure kuɗaɗen zaɓen ƙananan hukumomi: Jam’iyyun siyasa sun buƙaci gwamnan Kaduna ya binciki hadiminsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyun siyasa tara a Jihar Kaduna, sun zargi Abdul Ahmed Ishak, mashawarcin Gwamna Uba Sani na musamman kan hulɗa da masu-ruwa-da-tsaki, da yin awon gaba da kuɗaɗen zaɓen da aka tanada don samar da adalci a tsakanin dukkan jam’iyyu. Jam’iyyun da suka haɗa da; PRP, YPP, LP, NNPP, PDP, AAC, AA, ZLP da BP sun yi wannan zargin ne a wata sanarwar haɗin-gwiwa da suka raba wa manema labarai a Kaduna. "Wannan cin amana ne ga ƙudirin Gwamna na yin gaskiya da riƙon amana. Muna buƙatar a yi bincike cikin gaggawa tare da gyara." Sanarwar ta…
Read More

Gwamnatin Katsina ta bada umarnin buɗe burtali da wuraren kiwo a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A yunƙurinta na tabbatar da adalci ga manoma da makiyaya a gwamnatin Jihar Katsina ta bada umarnin buɗe duk wani Burtali ko wurin kiwo da aka rufe ba bisa ka'ida ba. Umarnin ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafe ne daga Fulani makiyaya akan yadda manoma ke datse hanyoyin kiwo da mashayar dabbobinsu ta hanyar nome wuraren. Akan haka ne Gwamnan jihar, Dikko Raɗɗa ya umarci Sakataren gwamnatin, Abdullahi Garba Faskari ya ziyarci ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa don warware matsalolin. Ƙananan hukumomin sune; Kaita, Mashi, Zango, Mai-Adua da Dutsinma inda a lokacin da ya kai ziyara,…
Read More

Jami’an tsaro sun ceto manoma shida daga hannun ƴan bindiga a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami'an tsaro sun ceto manoman da ƴan bindiga suka sace a lokacin da su ke girbin masara a gonarsu dake ƙauyen Gurbin Magajiya a ƙaramar hukumar Jibiya. Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Dakta Nasiru Mu'azu Ɗan-Musa ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya ce jami'an ƴan sintiri da aka fi sani da ƴan banga suka ankarar da sauran jami'an tsaro na al'umma da ƴan sanda, sojoji da da jami'an tsaro na farin kaya (DSS) waɗanda suka afka cikin dajin da aka ce an boye manoman. Kwamishinan ya ce an ceto…
Read More

Yadda tsaro ke dawo wa Nijeriya cikin ruwan sanyi

Daga RAHMA ABDULMAJID A shekarar 2023 da ta gabata ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa Malam Nuhu Ribaɗu muƙamin mai bai wa Nijeriya shawara kan harkokin tsaro wanda hakan ya zamo bambaraƙwai duba da cewa wadanda suka saba riƙe wannan kujerar kan fito ne da ga tsoffin manyan hafsoshin soji, yayin da shi kuma Malam Nuhu tsohon ɗan sanda ne. Hakan ya sa cikin wasu ƴan Nijeriya ya ɗuri ruwa inda suka riƙa dora alamar tambaya kan ko Malamin zai iya kai bantensa..! Ba kawai amsa wannan tambayar Ribaɗu ya yi ba, har ma da fito da sabon…
Read More

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya yi wa gwamnan Akwa-Ibom ta’aziyyar rasuwar matarsa

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya aika saƙon ta'aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Umo Bassey Eno da al'ummar jihar kan rasuwar matarsa, Misis Patience Umo Eno. Daraktan Labarai na Hedikwatar Tsaro, Janar Tukur Gusau ya fitar da hakan cikin wata takarda a ranar Juma'a inda Janar Musa ya bayyana alhininsa game da rashin wanda ya ce hakan wani muhimmin giɓi ne ga iyalan gwamnan da ma al'ummar jihar baki ɗaya ganin yadda ta ke bada gudunmawa wajen tafiyar da harkokin gwamnatin jihar. Janar Musa ya kuma jinjina wa kyawawan halayenta, ya na mai…
Read More

EFCC ta kama wani tsohon gwamna kan badaƙalar biliyan N27

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati, EFCC sun kama tsohon gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku kan zargin badaƙalar Naira biliyan 27. Rahotanni sun bayyana cewa an kama Ishaku ne, wanda ya sauka a kujerar gwamnan Taraba a shekarar 2023 bayan shafe shekaru takwas, a gidansa da ke Abuja a safiyar ranar Juma'a. Har zuwa daren ranar, tsohon gwamnan na ofishin hukumar inda wata majiya ta ce ana tuhumar sa ne da laifuka 15 wanɗanda da zarar an samu hujjoji akan sa, za a miƙa shi ga kotu. Majiyar ta ƙara da cewa, tun…
Read More

Bobrisky: VeryDarkMan ya gana da Ministan Cikin Gida, Tunji-Ojo

Daga BELLO A. BABAJI Wani ɗan gwagwarmaya mai suna Martins Otse da aka fi sani da 'VeryDarkMan' ya bayyana yadda ya haɗu da Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo. Ɗan gwagwarmayar ya yaba wa ministan kan dakatar da wasu jami'an gidan yari da ake zargin su da hannu a lamarin Bobrisky. Ya ce, ministan ya yi hakan ne don mayar da Nijeriya waje mai tsafta, ya na mai cewa hakan zai samu ne ta hanyar ƙoƙarin da ake yi a matakin da mutum ya tsinci kan sa. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan wata ɗaukar murya da ya fitar game…
Read More
Za a yi Babban Taron ƙungiyar Editoci na 2024 a Bayelsa

Za a yi Babban Taron ƙungiyar Editoci na 2024 a Bayelsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta ce za a gudanar da babban taronta na shekara-shekara na bana daga ranar 7 zuwa 9 ga watan Nuwamba, 2024 a garin Yeanagoa na Jihar Bayelsa. Kungiyar ƙwararrun editoci da shugabannin kafafen yaɗa labarai a Nijeriya, a cikin wata sanarwa a ranar Litinin ɗin da ta gabata ta bakin shugabanta, Eze Anaba da Babban Sakatare, Dokta Iyobosa Uwugiaren, sun ce taron Editocin Nijeriya (ANEC), wanda za a gudanar, Mataimakin Shugaban Tarayyar Nijeriya Alhaji Kashim Shettima ne zai ƙaddamar da Shugaban kuma Babban Editan jaridar THISDAY da Arise Media Group, Prince Nduka…
Read More