Labarai

Dorinar ruwa ta yi ajalin dogarin Sarkin Yawuri

Dorinar ruwa ta yi ajalin dogarin Sarkin Yawuri

An shiga firgici bayan da wata dorinar ruwa ta yi ajalin dogarin Sarkin Yawuri da ke Jihar Kebbi. Marigayin, mai suna Usman Maigadi, ya rasa ransa ne a cikin lambun Mai Martaba Sarkin Yawuri, Alhaji (Dr.) Muhammad Zayyanu-Abdullahi. An ruwaito cewa dabbar ta yi tsammanin marigayin na ƙoƙarin zuwa inda ta ke domin cutar da jaririyarta ne. Rahotannin sun tabbatar da cewa marigayin mai shekaru 60 ya gamu da tsautsayin ne a ranar Lahadi 22 ga watan Satumbar 2024. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Tillo da ke ƙaramar Hukumar Yauri yayin da dattijon ke kamun kifi. Shugaban ƙaramar Hikumar…
Read More
Zimbabwe za ta yanka giwaye 200 don ciyar da talakawa

Zimbabwe za ta yanka giwaye 200 don ciyar da talakawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Zimbabwe ta amince da yanke giwaye 200 don ciyar da ’yan ƙasar da ke fama da yunwa. Mai magana da yawun hukumar kula da wuraren shaƙatawa da namun daji na Zimbabwe, Tinashe Farawo, ya tabbatar wa CNN da faruwar lamarin a ranar Litinin. "Muna nufin yanka giwaye 200," inji Farawo, yayin da yake koka da yadda ake samun ƙaruwar rikicin giwaye da 'yan adam a sanadiyyar rashin isasshen abinci da ake fama da shi sakamakon tsananin fari a ƙasar da ke gabashin Afirka. Ya ƙara da cewa, “Dabbobin suna yin ɓarna sosai a cikin al’umma,…
Read More
Yan sanda a Katsina sun ceto mutane shida daga hannun ‘yan bindiga

Yan sanda a Katsina sun ceto mutane shida daga hannun ‘yan bindiga

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar 'yan sanda a Katsina ta ce ta samu nasarar daƙile sace mutane a wasu sassan jihar. Mai magana da yawun 'yan sanda a Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya shaidawa manema labarai haka. Ya kuma tabbatar da ceto mutum shida da 'yan sandan su kayi. Ya ce ɗaya lamarin ya faru ne a hanyar kauran Namoda zuwa Katsina a cikin dare bayan 'yan sanda da haɗin gwiwa na sojoji sukai bata kashi da 'yan bindigan. Sakamakon arangama da jami'an tsaro su ka yi da 'yan bindigan inji ASP Sadiq, sun sami ceto…
Read More

Shahararren ɗan Boko Haram, Bochum Abacha ya miƙa kan sa ga jami’an MNJTF

Daga BELLO A. BABAJI Wata nasara da aka samu a ƙoƙarin yaƙi da ta'addanci a yankin Tafkin Chadi ita ce, shahararren ɗan Boko Haram mai suna Bochu Abacha ya miƙa kan sa ga jami'an haɗaka na MNJTF a ƙaramar hukumar Kukawa ta Jihar Borno. Abacha, wanda ya kan yi ayyukansa na ta'addanci ne a yankin Monguno-Baga ya ce ya yi hakan ne saboda ayyukan da MNJTF ke gudanarwa da kuma janyewa daga ra'ayin cigaba da tafiya da ƙungiyar. Ya tsere ne daga sansanin Boko Haram na Mussaram tare da wata bindiga mai ƙirar AK47, da wasu makamai da albirusai da…
Read More

Zaki ya kashe mai kula da shi a gandun dajin Obasanjo

Daga BELLO A. BABAJI Wani abin alhini ya auku a wani gandun daji na tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun inda wani zaki ya farmaki mai kula da shi, Babaji Daule. Gandun wani sashi ne na wajen ajiyar littafai na Olusegun Obasanjo (OOPL). Rahotonni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a safiyar ranar Asabar, 29 ga watan Satumba inda babban jami'in tsaron wajen ya bada rahoton batun da misalin ƙarfe 7:40 na safe. Bayanai sun tabbatar da cewa, mai kula da wajen bai rufe ɗakin ajiyar zakin ba ne yadda ya kamata yayin…
Read More

Dalilin da ya sa aka dakatar da Joshua daga Boxing bayan kai da ya sha kashi a hannun Dubois

Daga BELLO A. BABAJI An dakatar da Anthony Joshua daga wasan Boxing na kwanaki 28 bayan da Daniel Dubois ya doke shi. Ɗan wasan, wanda ya zama zakara har sau biyu a gasar heavyweight ya sha kaye ne a hannun Dubois wanda ya doke shi a mataki na biyar a ranar Asabar a filin wasa na Wembley. Sakamakon kayen ne hukumar kula da Boxing ta Turai ta dakatar da Joshua na tsawon kwanaki 28. Wannan doka ce daga hukumar kan cewa duk ƴan Boxing na Turai da aka doke su a irin wannan matakin, to za a zartar da hukuncin…
Read More

Badaƙalar N3.1b: Yadda na kai wa Suswam Dala 15.8m a gidansa – Wani shaida ga kotu

Daga BELLO A. BABAJI Abubakar Umar, ɗaya ne daga cikin shaidu shida da ke cikin shari'ar tsohon gwamnan Jihar Benue, Gabriel Suswan inda ya bayyana wa wata babbar kotu da ke Maitama a Abuja cewa, a shekarar 2014 Suswam a lokacin da ya ke gwamna ya aike shi da Naira biliyan 3.1 don a canja su zuwa Dala. Kuɗin adadinsa ya kai Dala miliyan 15.8 wanda kuma ya ce ya kai masa gidansa a Maitama bayan an canja su. Kakakin hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC), Dele Oyewale ya faɗi hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar.…
Read More

Zargin ta’addanci: Kotu ta amince da ƙarar dake neman tilasta gwamnati ta binciki Matawalle

Daga BELLO A. BABAJI Wata babbar kotu a Abuja ta amince da ƙarar da ke neman a tilasta gwamnati ta yi bincike kan batun zargin alaƙar da ke tsakanin ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle da ayyukan ƴan bindiga a jihar Zamfara. Wani ɗan gwagwarmayar ƴancin Ɗan-adam kuma mazaunin Zamfara mai suna Abubakar Ɗahru ya shigar da takardar inda ya sanya sunayen Shugaba Bola Tinubu, Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a da Sufeton ƴan sanda a matsayin ƴan ɓangaren amsa ƙarar. A cikin takardar, Ɗahiru ya nemi kotun ta umarci Shugaba Tinubu ya bai wa Sufeton ƴan sanda umarnin gudanar…
Read More

Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa 198, mafi yawa a sama da shekaru 30

Daga BELLO A. BABAJI Ƙasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa mafi yawa cikin sama da shekaru 30 akan fursunoni 198 a ranar Asabar, kamar yadda ƙididdiga ta AFP ta nuna. Wannan ya nuna ƙasar ita ce ta uku a zartar da hukuncin kisa kan fursunoni da adadi mafi yawa bayan ƙasashen Chana da Iran a shekarar 2023 kamar yadda ƙungiyar 'Amnesty International' ta bayyana. Haka nan, ƙungiyar ta ce adadin ya wuce na shekarun 2022 da 1995 inda aka samu 196 da kuma 192. Amnesty International ta fara aikin tattara bayanai game hakan ne tun a shekarar 1990.
Read More