30
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta naɗa kwamitin bincike game da batun zargin rashawa da saɓa wa ƙa'idodin aiki a Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCos). Ministan Harkokin Cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya ƙaddamar da kwamitin a ranar Litinin a Abuja inda ya ce kwamitin zai yi bincike game da zargin jami'an hukumar da bai wa Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky mafaka. Ministan ya ce, akwai buƙatar a tsaftace hukumar don tabbatar da gaskiya da adalci. A kwanakin baya ne ministan wanda shine shugaban hukumar haɗaka ta hukumomin Civil Defence, gyaran hali da shige-da-fice (CDCFIB),…
