01
Oct
Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya tabbatar da cewa babban dalilin shigar sa harkar siyasa ita ce don ya yi wa al'umma aiki, ba wai ya sauya akalar dukiyoyinsu ba. El-Rufa'i ya faɗi hakan ne a yayin wata hira a gidan Rediyon Freedom a Kaduna inda ya yi watsi da zargin sauya akalar kuɗaɗe a gwamnatinsa, ya na mai cewa a wadace ya ke kafin ya fara jagorancin jihar. A kwanakin baya ne Majalisar Dokokin jihar ta zargi gwamnatin El-Rufa'i da sauya akalar kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 423. Saidai, tsohon gwamnan…
