Labarai

Sama da mutane 350 suka kamu da cutar Daji a Katsina

Sama da mutane 350 suka kamu da cutar Daji a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Batsari Hon.Mustapha Tukur Ruma ya bayyana haka a zauren Majalisar dokoki na Katsina. Yayi kira ga Majilisar da ta buƙaci gwamnatin jihar da ɗauki matakin gaggawa akan ɓullar cutar a ƙaramar hukumar kada ta bazu a sauran ƙananan hukumomin da suke maƙwabtaka da mazaɓar sa. Ɗan Majilisar yace,"akwai halin matsi na rayuwa ga kuma wannan annoba,idan kaje asibiti zaka ga masu ɗauke da cutar suke ciki". Bayan tattaunawa akan ƙudirin kakakin majalisar Rt Hon Nasiru Yahaya ya buƙaci akawun majalisar daya turawa ɓangaren zartarwa domin ɗaukan mataki cikin…
Read More

Haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba: ‘Yan sandan Zamfara sun kama ƴan ƙasashen waje

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar ƴan sanda ta cafke wasu ƴan ƙasashen waje guda uku daga ƙasar Burkina Faso bisa laifin haƙar ma’adanai ta haramtacciyar hanya da kuma zargin su da mu'amala da ƴan ta'adda a jihar Zamfara. Kwamishinan ƴan sandan jihar, Mohammed Dalijan, ne ya bayyana hakan a yayin da ya ke baje kolin waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Gusau, babban birnin jihar ranar Laraba. Ya ce, an kama waɗanda ake zargin ne a dajin ƙaramar hukumar Anka, inda sansanin ɗan ta’addan nan da aka hallaka yake hakar ma’adinai, watau marigayi Halilu Sububu. Wasu daga…
Read More
Gwamatin Nijeriya ta ƙaddamar da kwamitocin yaƙi da ambaliya

Gwamatin Nijeriya ta ƙaddamar da kwamitocin yaƙi da ambaliya

A yau Laraba ne ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli Farfesa Joseph Terlumun Utsev ya ƙaddamar da wani kwamitin ƙwararru da zai samar da dabarun daƙile afkuwar ambaliyar ruwa a faɗin ƙasar nan. Kwamitin zai yi aikin samar da taswirar inganta madatsun ruwa da tsarin zamantakewa da ma wasu ƙarin shirye-shiryen inganta muhalli cikin gaggawa. Tun da farko, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wasu muhimman tsare-tsare guda biyu da suka haɗa da kafa asusun bayar da agajin Ibtila'i da samar da kwamitin yaƙi da ambaliyar ruwa. Waɗanda suka halarci taron Ƙaddamar da kwamitin sun haɗa da Ministan watsa…
Read More

An haramta wa Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya shiga Isra’ila

Daga BELLO A. BABAJI Ministan harkokin waje na ƙasar Isra'ila, Katz ya sanar da cewa an haramta wa Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres shiga Isra'ila. Hakan na zuwa ne sakamakon rashin yin alla-wadai da harin da Iran ta kai wa Isara'ila a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024 da kuma amabtan ta a matsayin wacce ke da alhaki da Sakataren bai yi ba duk da cewa ƙasashen duniya sun yi hakan. Katz ya ce, duk wanda bai yi alla-wadai da harin da Iran ta kai wa ƙasarsu ba, bai halatta yi a shigo ƙasar ba. Kawo yanzu ba a…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya koma Landan domin hutun shekara

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya koma Landan domin hutun shekara

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin tafiya ƙasar Ingila domin hutun shekara. Tinubu dai ya tafi ƙasar Birtaniya ne bayan tafiyarsa ƙasar Sin a watan Satumba. Wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman Bayo Onanuga ya fitar a ranar Laraba, ya ce zai yi amfani da makonni biyu a matsayin hutun aiki, da kuma ja da baya don yin tunani kan sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa. Zai dawo ƙasar ne bayan kammala hutun. Shugaban ƙasar in bamu mance ba ya yi bikin cikar Nijeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai da jawabi ga 'yan ƙasa inda ya…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu ya tafi hutu

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja a ranar Laraba zuwa ƙasar Birtaniya don fara hutunsa na shekara wanda zai ɗauki tsawon mako biyu. Zai yi amfani da lokacin ne don hutun aiki da kuma yin nazari ga ayyukan gwamnatinsa na gyare-gyaren harkokin tattali, kamar yadda mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai da tsare-tsare, Mista Bayo Onanuga ya faɗa cikin wata sanarwa a Abuja. Bayan hutun ya ƙare ne shugaban zai dawo Nijeriya.
Read More

Gwamnan Zamfara ya yi bikin cikar shekaru 28 da ƙirƙiro jihar, ya buƙaci a yi addu’ar samun Zama lafiya

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci a ƙara kaimi wajen addu’o’in zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya a daidai lokacin da ƙasar ke bikin cika shekaru 64 da samun ƴancin kai. Jihar Zamfara na cikin jihohi shida da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha ta kafa a ranar 1 ga Oktoba, 1996. Gwamna Lawal, acikin wani saƙon fatan alheri da kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Talata, ya ce ranar 1 ga watan Oktoba rana ce ta musamman ta yin tunani akan irin gwagwarmaya da sadaukarwar da kakannin da suka yi fafutukar…
Read More
Gwamnatin Katsina ta wajabta yin gwajin ƙwayoyin halitta kafin aure

Gwamnatin Katsina ta wajabta yin gwajin ƙwayoyin halitta kafin aure

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta wajabta yin gwaje gwajen ƙwayoyin halitta ga waɗanda ke shirin yin aure ciki harda gwajin cutar sikila. Gwamnan jihar Dikko Raɗɗa, ya bayyana cewa ya zama wajibi ga masu shirin yin aure a jihar su yi gwajin cutar sikila domin daƙile yaɗuwar cutar. Raɗɗa ya bayyana haka ne a ranar Litinin a jawabin da ya gabatar wajen buɗe cibiyar kula da cutar sikila da kuma ƙaddamar da rabon magungunan cutar kyauta ga masu ciwon na sikila duk wata a babban asibitin jihar dake birnin Katsina. Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya…
Read More
Gajeren labari da dogon labari dukansu abu guda suka ƙunsa – Fauziyya Sani Jibril 

Gajeren labari da dogon labari dukansu abu guda suka ƙunsa – Fauziyya Sani Jibril 

Dalilin rubutu na san manyan mutane (Ci gaba daga makon jiya) Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  MANHAJA: Wanne abin farinciki ko akasin haka ne ya taɓa faruwa da ke ta sanadiyyar rubutu wanda ba za ki manta da su ba? FAUZIYYA: Gaskiya abubuwan suna da yawa, daga ciki akwai yadda na ji daɗin kasancewa ta a cikin marubuta, saboda zumunci da kuma karamcin da suke da shi. Bugu da ƙari duk da ban daɗe sosai a zauren marubata ba, ga kuma tarin ƙwararrun marubuta, amma a hakan na samu nasarar zama Gwarzuwa a gasanni har guda biyu, wanda tazarar gasannin ba…
Read More

Buɗaɗɗiyar wasika ga gwamnatin Nijeriya: An bar jaki an koma dukan taiki akan Lafiya

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu! Cikin girmamawa gare ku shugabanni da Jami’o’in Lafiya na ƙasa ta baki ɗaya. Na ɗauki alƙalamina ne domin na kiraye ku akan wani ganganci da kantafi da rayukan al’umma da na ga hukumar haraji ta Nkjeriya ta yi a wani asibiti mai zaman kansa a birnin Kano, wato 'Best Choice Specialist Hospital' da ke unguwar Gadon Ƙaya kan shataletalen Tal’udu. Wasu daga cikin marasa lafiya da wasu iyaye sun kawo wa jaridar Alfijir labarai ƙorafi akan yadda jami’an hukumar tattara harajin suka zo tare da jam’ian tsaro da bindigogi su na musu barazana akan sai dole…
Read More