Labarai

Munanan halayen mu ne silar faɗawar ‘yan ƙasar cikin ƙuncin rayuwa, cewar Sanata Buba

Munanan halayen mu ne silar faɗawar ‘yan ƙasar cikin ƙuncin rayuwa, cewar Sanata Buba

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Sanata Shehu Buba Umar ya lura da cewar, tirka-tirkar halayen rayuwa da 'yan Nijeriya suka tsinci kansu a ciki ya biyo bayan tsiwurwurori da kasassaɓoɓin jama'a ne da a kulli-yaumin suke kawo cikas da rashin tattibi na zamantakewa, haɗi da gurɓata lamuran rayuwa da samun kawunanmu cikin matsatsin rayuwa na rashin fasali. Ya ce, "a matsayina na wanda ya yi yaƙina da ƙudurorin Mahalicci, zan iya yin furucin cewa, waɗannan wahalhalun rayuwa da muka samu kawunanmu a ciki, ya biyo bayan sakamakon kasassaɓoɓi da munanan halayenmu ne da suke haddasa ƙuncin rayuwa da munanan zamantakewa…
Read More
Hukumar Kasuwar Abubakar Rimi ta ƙaddamar da motocin kwashe shara

Hukumar Kasuwar Abubakar Rimi ta ƙaddamar da motocin kwashe shara

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Hukumar Gudanarwar Kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi ƙarƙashin jagorancin Manajan Daraktanta Alhaji Abdul Bashir Husain bisa irin matakai da take ɗauka don kyautata cigaban kasuwar. Gwamnan da Kwamishinan Yaɗa Labarai da al'amuran cikin gida Baba Aliyu ɗantiye ya wakilta a yayin ƙaddamar da kayan kwashe shara da hukumar kasuwar Muhammad Abubakar Rimi ta gudanar a harabar kasuwar ranar Alhamis. Ya yi nuni da cewa kasuwanni wajen na tara shara saboda hada-hadar jama'a wannan mataki na samar da kayan shara yana da muhimmanci. Ya ce kasuwar Muhammadu…
Read More
 Tinubu zai rage farashin lantarki da yi wa haraji garambawul

 Tinubu zai rage farashin lantarki da yi wa haraji garambawul

Daga MAHDI M. MUHAMMAD da  SANI AHMAD GIWA Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta bayyana ƙudurin rage farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa. Ministan Wutar Lantarki, Cif Adebayo Adelabu ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba, 2024, lokacin da ya karɓi baƙuncin Babban Sakataren Asusun Ajiyar Kuɗaɗen Caca na ƙasa, Tosin Adeyanju, wanda ya jagoranci tawagar gudanarwar hukumar zuwa ziyarar ban girma ga ministan a hedikwatar ma'aikatar da ke Abuja. Wannan ƙuduri ya zo ne a daidai lokacin da ’yan Nijeriya suke kokawa da tsadar wutar lantarki a bana bayan ƙarin kuɗin…
Read More

Sana’ar kayan nauyi na kawo nakasu ga harkar ilimi a Katsina – SUBEB

Dakta Kabir Magaji, shugaban SUBEB na Katsina Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar ilimin firamare ta bai ɗaya (SUBEB) reshen Jihar Katsina ta koka kan yadda sana'ar kayan nauyi ke raunana karatun firamare a jihar. Shugaban hukumar, Dakta Kabir Magaji ya bayyana hakan a yayin hira da manema labarai da aka yi a ofishinsa. Ya ce, a duk rana sai ya samu rahoton ɓalle ƙofofin makarantu inda ɓarayi ke ɓaɓɓalle kujeru da tebura domin su cire ƙarafunan su saida wa masu kayan nauyi. "Ba su ma tsaya nan ba hatta kwanon rufi na azuzzuwan makarantun cirewa suke yi su saida…
Read More

Yadda mutanen Gaza ke mutuwa saboda ƙarancin abinci

Daga BELLO A. BABAJI Ana tilasta yara a ƙasar Palastine cigaba da kwana a ƙasa inda su ke fafutukar samun nitsuwa don jin labarai kafin yin bacci wanda an ɗauki tsawon lokaci ba samu ba. Shugaban ofishin jakadancin Palestine, Abdullah Abu Shawesh ya ce kwanaki 363 kenan da ake rugugin wuta a ƙasarsu wanda hakan ya sabbaba mutuwar mutanen da ba su gaza 41,616 ba da raunata 96,359 wanɗanda mafi yawancin su mata ne da ƙananan yara. Ya ce, aƙalla iyalai 902 ne aka cire daga jaddawalin rijistar ƴan ƙasar ta Palestine. Rahoton 'Human Right Watch' ya ce, zuwa ranar…
Read More

Lakcar ƙasa-da-ƙasa ta NAN: Babban Hafsan Tsaro ya jaddada muhimmancin haɗaka a magance matsalolin Sahel

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba, 2024 ne jaridar 'News Agency Nigeria' ta yi taron shekara-shekara na ƙasa-da-ƙasa karo na farko a cibiyar albarkatun rundunar soji da ke Abuja. Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa a yayin taron, ya yi jawabin ƙaruwar taɓarɓarewar al'amura a shiyyar Sahel inda ya buƙaci Nijeriya da haɗin-gwiwar ƙwararru a fagen tsaro su haɗe kai wajen kawo ƙarshen rashin tsaro a yankin. Ya ce, lamarin lalacewar harkar tsaro a Sahel ya samo asali ne daga rashin ingantaccen shugabanci, wariya ga harkokin tattali da kuma rushewar gwamnatin Libya a…
Read More

KILAF ya ayyana finafinai 57 da ka iya samun lambobin yabo a bajekolin 2024

Daga BELLO A. BABAJI Shirin taron kasuwancin finafinan Afrika na yarukan Kano (KILAF), ya ayyana finafinai 57 da ka iya samun lambobin yabo a bajekoli na 2024 da za a yi ranar 30 ga watan Nuwamba a Kano. Cikin wata hira da manema labarai da Shugaban KILAF, Malam Abdulkareem Mohammed, ya ce taron wanda shi ne karo na bakwai, an samu finafinai 57 cikin 510 da aka fitar a duniya waɗanda suka fito daga ƙasashe 66 inda 35 ƙasashe ne na Nahiyar Afirka. Ya kuma bayyana cewa, daga finafinan 57 da suka fito daga ƙasashe 16, kowane ɗaya daga cikin…
Read More

Kotu ta haramta wa VIO tsayar da motoci da tsare su

Daga BELLO A. BABAJI Wata babbar kotu da ke Abuja, ta aika wa hukumar kula da zirga-zirgar motoci (VIO) saƙon umarnin dakatar da ita daga tsayar da motoci a kan hanya da tsare su a ofishinsu da kuma cin tarar direbobi. Mai Shari'a Nkeonye Evelyn Maha ta bayyana hakan a lokacin da ta ke hukunci kan ƙara mai lamba kamar haka; FHC/ABJ/CS/1695/2023, inda ta ce jami'an hukumar ba su da ikon karɓe motoci ko sanya tara masu tsauri ga direbobi. Waɗanda aka zayyano a matsayin masu kare ƙarar sune; Daraktan hukumar sufurin motoci, Area Kwamanda, ministan Abuja da sauran su.…
Read More

Tinubu ya miƙa wa Majalisa ƙudiri huɗu na gyare-gyaren haraji

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya rubuta wa Majalisar ƙasa ƙudiri guda huɗu da suka shafi lamarin haraji don yin nazari da kuma tabbatar da su. Kakakin Majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya karanta ƙudirin inda ya ce an tsara su ne la'akari da gyare-gyare da gwamnatin Shugaba Tinubu ke yi. Ƙudiri huɗun sune; ƙudirin haraji ta ƙasa na 2024, ƙudirin sanya haraji, ƙudirin samar da hukumar haraji ta ƙasa da kuma ƙudirin samar da hukumar haɗaka ta haraji. Ƙudirin farko zai yi aiki ne wajen samar da tsarin gudanar da harkokin tattara haraji bisa salo na gama-gari. Sai…
Read More
Zargin alhmundahana: Kotu ta bada belin tsohon gwamnan Taraba Ishaku

Zargin alhmundahana: Kotu ta bada belin tsohon gwamnan Taraba Ishaku

Daga USMAN KAROFI a Abuja Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Maitama ta bada belin tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku akan kuɗi naira miliyan 150. An gurfanar da Ishaku a ranar Litinin tare da Bello Yero, tsohon sakataren dindindin na ofishin kula da ƙananan hukumomi da masarautu. Mutanen biyu dai na fuskantar tuhuma guda 15 da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin Ƙasa ta’annati (EFCC) ta shigar, inda ake tuhumar su da laifin zamba, haɗa baki, da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba. A yayin da ake gurfanar da su a ranar Litinin, mutanen…
Read More