Labarai

Rashin tsaro: Sanata Yari da malaman Musulunci a Zamfara sun yi addu’a ta musamman wa Tinubu

Rashin tsaro: Sanata Yari da malaman Musulunci a Zamfara sun yi addu’a ta musamman wa Tinubu

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau  Tsohon gwamnan Jihar Zamfara Sanata Abdul'aziz Yari Abubakar ya shirya taron addu'o'i na ibada a ranar Talata tare da malaman addinin Musulunci na jihar Zamfara domin samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nasarar yaƙi da 'yan fashi a ƙasar nan.  Sanata Yari a lokacin da yake buɗe taron addu’o’in a gidansa da ke garin Talatan Mafara hedikwatar ƙaramar hukumar Talata Mafara ya bayyana addu’o’in da aka yi wa gwamnatin Shugaba Tinubu a matsayin lokacin da ya dace don samun nasarar yaƙi da ‘yan ta'adda a ƙasar nan.  A cewarsa, Nijeriya a karkashin shugaban kasa…
Read More
Daily Trust ta bada haƙuri kan rahoton ‘Yarjejeniyar Samoa’

Daily Trust ta bada haƙuri kan rahoton ‘Yarjejeniyar Samoa’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jaridar Daily Trust ta bayar da haƙuri kan labarin da ta yi na 'Yarjejeniyar Samoa', wanda ya tayar da ƙura. BBC ta rawaito cewa a wata sanarwa da ta fitar, mai taken, Yarjejeniyar Samoa: Muna bayar da haƙuri, ta ce, “A jaridarmu ta 4 ga Yulin 2024, babban labarinmu mai taken, “LGBT: Nijeriya ta shiga yarjejeniyar biliyan $150 da Samoa”, labarin ya tayar da ƙura a faɗin ƙasar. Wannan ya sa gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara a gaban hukumar sauraron ƙararrakin da suke da alaƙa da jaridu wato National Media Complaints Commission (NMCC),…
Read More
Rundunar soji ta kori Seaman Abbas daga aiki

Rundunar soji ta kori Seaman Abbas daga aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar da korar jami’in sojin ruwan nan mai suna Seaman Abbas Haruna daga aiki. Sallamar Seaman Abbas daga aiki na zuwa makonni bayan mai ɗakinsa da ta bayyana a cikin wani shiri na gidan Rediyon Human Rights ta fallasa irin uƙubar da yake ciki tsawon shekaru shida. Sai dai bayan wannan fallasa ta yamutsa hazo, Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya, Janar Christopher Musa da ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle suka ba da umarnin gaggauta gudanar da bincike. Da yake ƙarin haske kan lamarin a ranar Laraba yayin ganawa da manema…
Read More
 Jami’an NSCDC sun kama ƙasurgumin mai safarar makamai a Kaduna

 Jami’an NSCDC sun kama ƙasurgumin mai safarar makamai a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Sibil Difens NSCDC reshen jihar Kaduna ta bayyana cewa jami’an ta sun kama wani ƙasurgumin mai safarar makamai ɗauke da harsasai da dama sannan da wasu mutum bakwai masu haƙo ma’adinai ba tare da izini ba. Shugaban rundunar Nuhu Muhammadu ya sanar da haka a garin Kaduna ranar Laraba. “Jami’an rundunar a ranar Talatan yayin da suke sintiri a hanyar Mage road dake Tudun-Wadan Zaria suka kama ɗan achaɓa ɗaya da wani mutum. “Yayin da suke gudanar da bincike a kansu ɗaya daga cikin mutanen sai ya gudu. ɗayan da suke tare mai…
Read More
Matasa a Katsina sun ƙaurace wa shagulgulan murnar ranar samun ‘yancin kan Nijeriya

Matasa a Katsina sun ƙaurace wa shagulgulan murnar ranar samun ‘yancin kan Nijeriya

Daga UMAR GARBA a Katsina Mazauna jihar Katsina musamman matasa waɗanda kan shirya tarurruka don murnar zagayowar ranar samun 'yancin kai, sun ƙaurace wa shirya irin waɗannan shagulgula da su kan shirya a ranar 1 ga watan Oktoba na kowace shekara. A bisa al'ada matasa, samari da 'yan mata kan haɗu a wuraren shirya tarurruka sanye da tufafi iri ɗaya, galibi masu launin tutar ƙasar nan, ba don nishaɗantar da kansu ba kawai har ma da gudanar da jawabai da suka shafi cigaban ƙasar nan ko akasin haka. Matasan kan yi amfani da ranar don sanar da shugabanni matsalolinsu waɗanda…
Read More
2027: Ka yi hattara da Kwankwaso, jigo a APC ya gargaɗi Tinubu

2027: Ka yi hattara da Kwankwaso, jigo a APC ya gargaɗi Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani jigo a Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) a jihar Kano, Dakta Musa Kwankwaso, ya shawarci Shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan wajen ƙulla duk wata yarjejeniya da jagoran jam’iyyar New Nigeria People’s Party, Dr. Rabiu Kwankwaso, kafin zaɓen 2027 mai zuwa. Kwankwaso, wanda ya taɓa riƙe muƙamin kwamishina a gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje, ya ce duk wata yarjejeniya da Tinubu ke son ƙullawa da tsohon Gwamna Kwankwaso dole ne ya kasance a gaban shugabannin APC a Kano. Ya yi zargin cewa Kwankwaso na da ɗabi’ar watsi da yarjejeniyar siyasa. Da…
Read More
Kotu ta tsare magidanci kan yi wa ‘yar cikinsa fyaɗe

Kotu ta tsare magidanci kan yi wa ‘yar cikinsa fyaɗe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Ado-Ekiti a Jihar Eikiti, ta bayar da umarnin a tsare wani mutum mai shekara 42, Christopher Israel, a gidan gyaran hali bisa zargin yi wa ’yar cikinsa mai shekara 22 fyaɗe. Alƙalin kotun, Misis Olubunmi Bamidele, ba ta amsa roƙon Israel na yin shari’ar a sirrance. Ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali da ke Ado Ekiti, har zuwa lokacin da za ta nemi shawarar lauyoyi daga ofishin daraktan ƙararrakin jama’a. Ta ɗage shari’ar har zuwa ranar 6…
Read More
Bello Turji ya gindaya sharuɗɗan kawo ƙarshen hare-hare da yake jagoranta

Bello Turji ya gindaya sharuɗɗan kawo ƙarshen hare-hare da yake jagoranta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shahararren ɗan bindigar nan da ya yi ƙaurin suna wajen satar mutane da karɓar kuɗin fansa, Bello Turji, ya zargi gwamnan Zamfara Dauda Lawal da tsohon gwamnan jihar kuma ƙaramin ministan tsaron Nijeriya, Bello Matwalle da siyasantar da batun tsaro a jihar. Turji wanda ake zargin ya yi ƙaura daga jihar Zamfara tun bayan tsananta hare-hare da rundunar sojin Nijeriya ke yi, ya gindaya sharuɗa da za a bi wajen samar da zaman lafiya a jihar. Ya ce za a samu zaman lafiya a jihar ne idan jami’an tsaro da ‘yan bijilanti suka daina…
Read More
 ’Yan bindiga na ci gaba da kashe kansu a Katsina

 ’Yan bindiga na ci gaba da kashe kansu a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wani ƙazamin rikici ya ɓarke tsakanin dabar ‘yan bindiga a Jihar Katsina, rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan bindinga 20 da ba sa jituwa a tsakaninsu. Daga cikin mutanen da suka rasa rayukansu akwai fitattun shugabannin 'yan bindigar da mabiyansu. Rikicin ya afku da sanyin safiyar Alhamis ɗin nan, rahotanni sun bayyana cewa ɓarayin dajin sun gwabza faɗan ne a yankin ɗan Ali da ke ƙaramar hukumar ɗan Musa ta jihar Katsina. Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya bayyana cikakken bayani kan yadda rikicin ya ɓarke ta hanyar wani saƙo da ya…
Read More
Akwai rufa-rufa da siyasa a sake fasalin Naira na Emefiele – Shonubi

Akwai rufa-rufa da siyasa a sake fasalin Naira na Emefiele – Shonubi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon Muƙaddashin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Folashodun Shonubi, a ranar Laraba ya shaida wa mai shari’a Maryann Anenih na babbar kotun birnin tarayya da ke Maitama Abuja cewa akwai siyasa a sake fasalin naira da aka yi a shekarar 2022. Shonubi wanda ya kasance mataimakin gwamnan ayyuka kafin a naɗa shi muaaddashin gwamnan CBN, amma yanzu ya yi ritaya, a martanin da ya mayar kan lauyan masu kare Olalekan Ojo (SAN) a ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya shaida wa kotun cewa tsohon shugaban babban bankin…
Read More