05
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar Kamfanonin Jiragen Yawo na Aikin Hajji da Umrah ta Nijeriya (AHOUN) ta yi barazanar maka Hukumar Aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) a kotu idan ba ta dawo wa mambobinta kuɗaɗensu Naira biliyan 17 ba. Da yake jawabi yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin, Shugaban NAHOUN, Abdullateef Ekundayo Yusuf, ya ce NAHCON ta daɗe tana riƙe kuɗaɗen mambobinsu. Ya ce kuɗaɗen sun haɗa da ajiyar gargaɗi da kuɗaɗen bizar da ba a yi amfani da su ba, da kuɗaɗen da aka biya fiye da ƙima da kuma kuɗaɗen ajiyar Umrah, da dai…
