05
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta ce ta soma bincike bayan da rahotanni daga jihar Kaduna suka ce wani hari da jirginta ya kai ya kashe farar hula aƙalla 24. Lamarin dai ya faru a ranar Juma’a ta makon jiya a yankin ƙaramar Hukumar Giwa da ke arewacin jihar ta Kaduna. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi ne, rundunar sojin saman Nijeriya ta ce ta kai hare-hare kan maɓoyar ‘yan ta’adda a dajin Yadi da ke ƙaramar hukumar ta Giwa. Sanawar wadda muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar Kabiru Ali…
