Labarai

Tinubu ya miƙa wuya ga buƙatar Majalisar Wakilai ta bai wa kakakinta lambar GCON

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da buƙatar Majalisar Wakilai na a bai wa kakakinta, Tajuddeen Abbas matsayin GCON (Grand Commander of the Order of the Niger). Hakan na zuwa ne bayan nuna rashin amincewa da mambobin majalisar suka yi na ayyana kakakin da mataimakin shugaban Majalisar Dattijai a matsayin CFR, wato 'Commander of the Federal Republic' da Shugaba Tinubu ya yi a jawabinsa na ranar zagayowar ƴancin kai. Hakan ya haifar da muhawara a zauren Majalisar, a ranar Laraba ne mambobin suka nuna cewa kakakin nasu ya cancanci lambar girma sama da wannan. Mai taimaka…
Read More

Shettima ya nemi Hukumar FRSC ta aiwatar da sababbin dabarun daƙile haɗura a titinan Nijeriya

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya umarci Hukumar Kiyaye haɗɗura ta Ƙasa da ta aiwatar da sabbin matakan kariya a kan titinan dake faɗin Nijeriya don rage yawan afkuwar haɗurra. Shettima ya bayar da umarnin ne a yayin da ya karɓi baƙoncin shugaban hukumar, Marshal Shehu Muhammad da wasu ƙusoshin hukumar a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. A yayin baƙoncin, Shettima ya ƙaddamar da majalisar bayar da shawara kan dabarun kiyaye afkuwar haɗɗura wadda aka ɗora wa alhakin rage afkuwar haɗɗura kafin shekarar 2030. Hakazalika, Shettima wanda shi ke jan ragamar Majalisar ya ƙara nuna muhimmanci amfani da fasahar…
Read More
‘Yan ta’adda sun hana sallar Juma’a a Katsina

‘Yan ta’adda sun hana sallar Juma’a a Katsina

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gumurzun faɗa a ɓangarorin 'yan bindiga a garin Ɗan Ali a ƙaramar hukumar Ɗanmusa ya sanya dole jama'ar Musulmi da suka je sallar Juma'a a garin suka ranta a na kare kafin gudanar da sallar Juma'a. Wani mazaunin garin da bai so a faɗi sunan shi yace wannan faɗa ne da aka daɗe ana gwabzawa tsakanin Buzare da Nure waɗanda da abokai ne amma yanzu suka zama abokan gaba. Ya ce kowanan su yana jagorantar gungun yan ta'adda a yankin ƙaramar hukumar Ɗanmusa da suka maida sansaninsu. Ya cigaba da bayyana cewa shi Buzare…
Read More

SUBEB ta fara horar da ƴan firamare kiwon kaji a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar bada ilimi a matakin farko, SUBEB ta fara horar da yara ƴan makarantun firamare yadda ake kiwon kaji a Jihar Katsina. Shugaban hukumar, Dakta Kabir Magaji ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a ofisoshinsa inda ya ce hukumar ta ware makarantu 120 domin gudanar da shirin. Daktan ya kuma ce, hukumar ta kashe Naira miliyan 48 wajen sayan kajin kiwo da abincinsu tare da biyan alawus na malaman da ke horar da ɗaliban. Ya bayyana cewa, hukumar ta ƙirƙiro da shirin ne domin taimaka wa ɗaliban su zama masu dogaro…
Read More
Gwamnatin Katsina ta kashe biliyan N3.77 wajen kiwon lafiya

Gwamnatin Katsina ta kashe biliyan N3.77 wajen kiwon lafiya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da cewa gwamnatinsa ta kashe Naira biliyan uku da miliyan saba'in da bakwai wajen kiyon lafiya a faɗin jihar. Gwamnan ya yi wannan magana ne a lokacin da yake buɗe cibiyar masu ɗauke da ciwon sikila da Uwargidan Gwamnan Hajiya ɗulaihah Umar Dikko Raɗɗa ta assasa a babban asibitin Katsina. Ya ce kuɗaɗen an kashe su ne wajen biya wa ɗaliban koyon karatun kiyon lafiya suke a ciki da wajen Nijeriya.  Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnati ta biya tallafin kuɗi naira miliyan 112 ga ɗalibai 542, da kuma…
Read More
Hisbah ta kama wata mata da ta mayar da gidan da take haya wajen baɗala a Kano 

Hisbah ta kama wata mata da ta mayar da gidan da take haya wajen baɗala a Kano 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama wata mata da ake zargin ta mayar da gidan da ta karɓa haya amma ta maida shi wajen saukar baƙi, maza da mata suna aikata baɗala. Muƙaddashin Babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Dakta Mujahid Aminudeen ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da hukumar ta aike wa Manhaja a ranar Lahadi. Ya ce an kama matar a unguwar Samegu bayan mazauna unguwar sun kawo ƙorafin ta'adar da ta ke yi. Hakazalika Dakta ta kama wasu 'yan mata a titin Filin Sukuwa da ake zargin…
Read More
‘Yancin Nijeriya: Za mu tallafa wa jihohi da motocin CNG domin rage tsadar kuɗin mota – Tinubu

‘Yancin Nijeriya: Za mu tallafa wa jihohi da motocin CNG domin rage tsadar kuɗin mota – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jigawa ta haɗa guiwa da kamfanin Safa & Fresh domin kafa cibiyoyin maida motoci masu amfani da gas a jihar. Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta tallafa wa jihohin ƙasar nan 36 har da babban birnin tarayya wajen samun motocin bas masu amfani da iskar gas samfurin CNG domin sauƙaƙa wa al’umma tsadar kuɗin mota. A cikin jawabinsa na Tunawa da Ranar Samun ‘Yancin Kan Nijeriya a ranar Talata, shugaban ya ce an kusa kammala shirin sauya fasalin makamashi. “Muna dab da kammala shirin sauya fasalin makamashi. Muna kan…
Read More
Ƙaramar Hukumar Fagge na ƙoƙarin ganin ta fita daga sahun masu ɗauke da cutar Shan Inna

Ƙaramar Hukumar Fagge na ƙoƙarin ganin ta fita daga sahun masu ɗauke da cutar Shan Inna

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Shugaban kula da sashen lafiya a matakin farko na ƙaramar hukumar Fagge, Malam Ahmad ɗahiru ya bayyana cewa ƙaramar hukumar na matuƙar ƙoƙarin ganin ta fita daga jerin ƙananan hukumomi dake ɗauke da cutar shan Inna. Ya ce a wannan karon na zagayen allurar riga-kafin cutar akwai buƙatar sanya ido sosai domin ƙaramar hukumar ta Fagge ta tsinci kanta cikin waɗanda ke ɗauke da cutar wacce aka samu a cikin ruwa.  Ya ce duk jihar Kano Fagge ce ke ɗauke da ƙwayar cutar mafi rinjaye kuma sun sami tallafi daga Gwamnatin jihar Kano ta ba…
Read More
Al’ummar Jihar Kano su zama cikin shirin yin ƙidayar al’umma – Dakta Ibrahim Daurawa

Al’ummar Jihar Kano su zama cikin shirin yin ƙidayar al’umma – Dakta Ibrahim Daurawa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Shugaban Hukumar ƙidaya ta jihar Kano, Dakta Aminu Ibrahim Tsayawa ya bayyana cewa shirin yin ƙidaya ga al'ummar ƙasar nan na nan tafe nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana haka ne a Kano yayin da yake zantawa da 'yan jarida a cikin makon nan.   Ya ce jama'ar jihar Kano su zama a cikin shirin ƙidayar, domin da sanin yawansu ne za su samu kaso da ya dace da ita na samun rabon albarkatun ƙasa da gwamnatin tarayya. Ya ce duk da dai ba a kai ga sanya takamaimai ranar da za a yi ƙidayar…
Read More
‘Yan sanda a Imo sun kama mutanen da ake zargi da sayar da ƙananan yara 

‘Yan sanda a Imo sun kama mutanen da ake zargi da sayar da ƙananan yara 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar 'yan sanda a jihar Imo ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da safarar ƙananan yara, inda ake zarginsu da sayar da yara kan Naira Miliyan 1. Manhaja ta rawaito cewa mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a jihar, Henry Okoye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Mista Okoye, ya ce mutanen waɗanda suka haɗa da maza 2 mata 2 suna sace yara daga wurin iyayensu. Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce an kama mutanen ne bayan bibiyarsu a maɓoyarsu a jihar.…
Read More