05
Oct
Daga BELLO A. BABAJI Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala jaddawalin sunayen ministocin da za su cigaba da aiki da shi bayan garambawul ga tawagar ma'aikatansa. Bayanai da dama a Fadar shugaban ƙasa sun ce, Tinubu ya kammala aikin jaddawalin inda aka cire wasu da kuma barin waɗanda za a cigaba da tafiya da su, wanda an yi tsammanin ya fitar a ranar Alhamis, kwana ɗaya kafin ya tafi hutu Birtaniya, kamar wani da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana. Sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a watan Agusta ne, Tinubu ya…
