Labarai

Cibiyar gudanarwa ta Amurka ta bai wa Gwamna Abba lambar yabo

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya samu kyautar girmamawa daga cibiyar gudanarwa da shugabanci ta ƙasar Amurka. Kamar yadda wata sanarwa daga kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ta bayyana, cibiyar ta bai wa gwamnan lambar girman ne saboda ƙoƙarinsa na samar da cigaba wa al'umma da kula da dukiyarsu. Wakilin cibiyar, Barista Steven Lounge ya gabatar da hakan a wani taron karramawa, a masauƙin gwamnatin jihar Kano da ke Abuja. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan gwamnan ya samu lambar girma na Ƙasa daga ƙungiyar malamai ta ƙasa (NUT) a lokacin zagoryar ranar malamai…
Read More

Shugaban sakandire a Zamfara ya lashe kyautar gwarzon malami na shugaban ƙasa ta 2024

Daga BELLO A. BABAJI Wani shugaban makarantar Sakandire daga Jihar Zamfara ya samu kyautar lambar yabo na ofishin shugaban ƙasa na gwarzon malami ta shekarar 2024. A ranar 5 ga watan Oktoban kowacce shekara ne ake bikin ranar malamai ta duniya wanda UNESCO ta shirya da aka fara a shekarar 1994 don yaba wa malamai saboda ƙoƙarinsu na samar da ci-gaba acikin al'umma. An gudanar da bikin ne a filin taro na 'Eagle Square' da ke Abuja wanda Sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume ya jagoranta inda shugaban makarantar Sambo Secondary School, Mallam Musa Yahaya da ke Gusau ya…
Read More

‘Yan sanda sun musanta hana sallar juma’a da aka ce ƴan bindinga sun yi a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundanar ƴan sandan Jihar Katsina ta musanta wasu rahotanni dake cewa ƴan bindinga sun tarwatsa mutane a garin Ɗan Ali dake ƙaramar hukumar Ɗan Musa a jihar, a lokacin da suke sallar juma'a. Rundanar ta ce an ƙirƙiri labarin ne don a jefa al'ummar yankin cikin firgici da razani, don haka rundunar ta yi kira ga al'umma da su yi watsi da labarin. Wasu rahotanni sun bayyana cewa, ƴan bindinga ɗauke da muggan makamai sun yi dirar mikiya a garin Ɗan Ali a ranar Juma'a, 4 ga watan Oktoba, inda suka riƙa bi masallatai suna…
Read More
Gobara ta tashi a kasuwar Kantin Kwari da ke Kano

Gobara ta tashi a kasuwar Kantin Kwari da ke Kano

Wata gobara ta tashi a daren ranar Asabar a shahararriyar kasuwar Kantin-Kwari da ke Kano. Kayayyaki da kadarori na miliyoyin a ka kiyasta asarar su a wannan mummunar gobarar kamar yadda Jaridar Blueprint ta rawaito. Jaridar Blueprint ta cigaba da rawaito yadda yan kasuwa su ka fito su na fafatawa da wutar domin ganin sun rage asarar da su ka tafka. Ɗaya daga cikin ’yan kasuwar , Alhaji Hamisu Sabo, wanda ya zanta da Blueprint ya bayyana abin da ya faru da shi. Ya ce, “Wani ya kira ni da misalin karfe 7:30 na yamma a yau Asabar ya na…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: APP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi 22 cikin 23 a Jihar Ribas

Da Ɗumi-Ɗumi: APP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi 22 cikin 23 a Jihar Ribas

Jam’iyyar Action People’s Party (APP) ta lashe kujeru 22 daga cikin 23 a zaɓen ƙananan hukumomi da aka kammala a Jihar Ribas. Babban Jami’in Zabe na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Ribas, Mai Shari’a Adolphus Enebeli ne ya bayyana sakamakon zaɓen ranar Asabar a Fatakwal. Ya ce an dakatar da sanarwar ne a karamar hukumar Etche saboda har yanzu ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen. Sauran bayanai na zuwa...
Read More

Darajar Osimhen a kasuwa ta ragu saboda Turkiyya

Daga BELLO A. BABAJI Manajan hada-hadar ƴan wasa a ƙasar Turkiyya, Gökhan Yağmur ya ce darajar ɗan wasan aro a ƙungiyar Galatasaray kuma ɗan Super Eagles ta Nijeriya, Victor Osimhen ta ragu duk ƙoƙarin da ya ke yi tun bayan komawara sa daga Napoli. Osimhen ya ci ƙwallaye biyu da bada wasu biyu da aka ci acikin wasanni biyar tun da ya je ƙungiyar. Manajan ya ce ba ƙoƙarin ɗan wasa ke sa ya ƙara daraja a Turkiyya ba, ya na mai cewa ana la'akari ne da yadda kasuwa ta ke. Ya ce, wasannin kofin zakarun Turai da na gida…
Read More
‘Ya’yan Buhari da wasu manyan ƙasa na fuskantar barazanar ƙwace filayensu a Abuja

‘Ya’yan Buhari da wasu manyan ƙasa na fuskantar barazanar ƙwace filayensu a Abuja

Hukumar babban birnin tarayya Abuja, ta yi gargaɗi ga wasu fitattun ‘yan Najeriya da suka haɗa da ‘ya’yan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Yusuf da Zahra, da su biya kuɗaɗen da ake bin su na filaye a cikin kwanaki 14, ko kuma su rasa haƙƙin mallakar su. Ana sanar da duk wanda abin ya shafa cewa rashin biyan duk wasu kuɗaɗen filaye da kuma caji a cikin lokacin da aka ƙayyade zai haifar da janye tayin mallaka (R-of-O) akan filayen da aka ambata. Hukumar da ke kula da babban birnin tarayya Abuja ta hannun hukumar raya babban birnin tarayya FCDA,…
Read More

Gwamnatin Sakkwato ta amince da gina madatsun ruwa uku da sayen tirakta 244

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Sakkwato ta sanar da shirinta na gina madatsun ruwa guda uku a ƙoƙarinta na taimaka wa ayyukan noman fadama da na rani a jihar don inganta harkar noma. Mai taimaka wa gwamnan kan harkar tattali, Bashir Achida ya faɗi hakan a yayin wata hira da manema labarai a Abuja, ranar Juma'a. Ya ce, gwamnatin jihar za ta sayi motocin gona, wato tirakta guda 244 don inganta noman zamani duk don tabbatar da samun isasshen abinci ga kasuwa da al'ummar jihar. Achida ya bayyana hakan a matsayin wani shiri na inganta al'umma wanda acikinsa akwai kiwon…
Read More

Tsaro: Yanzu kowa zai iya tafiya komai dare a Nijeriya – Ribaɗu

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ikirarin cewa an samu ci-gaba ta fuskar tsaro a gwamnatinsa. Tinubu, ta bakin mai ba shi shawara kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu a yayin wata lakca da NAN ta shirya, ya faɗi hakan ne inda ya kamanta da yadda tsaro ya ke a shekarar 2022 da farkon 2023 a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari na da kuma yanzu. Ribaɗu ya ce daga yanzu, mutane za su iya tafiye-tafiye cikin aminci daga Abuja zuwa ko'ina a Nijeriya ba tare da fargaba ko tsoron riskar harin ƴan…
Read More
Gwamnan Akwa Ibom ya bayyana ɗiyar shi  a matsayin wadda za ta maye gurbin ofishin matar gwamna

Gwamnan Akwa Ibom ya bayyana ɗiyar shi a matsayin wadda za ta maye gurbin ofishin matar gwamna

Daga USMAN KAROFI Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya nada ɗiyar sa, Helen Eno-Obareki, a matsayin wadda za ta riƙe ofishin matar gwamna na riƙo, bayan rasuwar matarsa ​​Fasto Patience Eno. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a yayin ziyarar ta’aziyya da uwargidan shugaban Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu da wasu jiga-jigan ƙasar suka kai a Uyo. A cewar gwamnan, ɗiyar sa za ta ɗauki nauyin aikin ofishin matar gwamna, tare da tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan da marigayiyar matarsa ​​ta ƙaddamar, musamman na Golden Initiative For All. Don in kula da Ofishin matar gwamna…
Read More