08
Oct
A ranar Talata ne Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya yi alhinin mutuwar jami'an tsaron al'umma ( Community Protection Guards) da 'yan bindiga su ka yi wa kwantan ɓauna a garin Tsafe kamar yadda mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar. Lamarin ya faru ne a wani shingen jami'an da ke wajen garin Tsafe, inda ƴan bindigan su ka yi ma jami'an kwantan ɓauna su ka kashe su. Gwamnan ya bayyana wannan a matsayin tsantsar rashin imani, ya kuma jaddada cewa jami'an tsaro na bincike domin kamo waɗanda su ka yi wannan ta'addanci. Gwamnan ya yaba da…
