Labarai

‘Yan kasuwa sun daidaita farashinsu na fetur da na matatar Ɗangote

‘Yan kasuwa sun daidaita farashinsu na fetur da na matatar Ɗangote

Masu sayar da man fetur masu zaman kansu a ranar Laraba sun daidaita farashin man fetur a Babban Birnin Tarayya don daidaita shi da farashin da suka saya daga Kamfanin matatar Ɗangote. Bincike ya nuna cewa yawancin gidajen mai sun gyara farashin lita ɗaya na man fetur zuwa Naira 1,200. Wannan canjin ya biyo bayan cikakken sauƙin tsarin kasuwancin man fetur, wanda ya baiwa Kamfanin Mai na Ƙasa na Najeriya (NNPC) damar kawo ƙarshen yarjejeniyar sayen mai daga matatar Ɗangote. Wannan ya buɗe ƙofa ga sauran masu sayar da man fetur don su iya siyan mai kai tsaye daga matatar…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta farfaɗo da kamfanin sarrafa fatu da ke garin Daura

Gwamnatin Katsina za ta farfaɗo da kamfanin sarrafa fatu da ke garin Daura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina za ta farfaɗo da kamfanin sarrafa fatu da ke garin Daura a ƙaramar hukumar Daura. Gwamna Dikko Raɗda ya sanar da haka a hira da manema labarai bayan ya kammala ziyarar gani da ido a Kamfanin wanda na ɗaya daga da cikin kamfanonin da tsohon gwamna a tsohuwar Jihar Kaduna marigayi Malam Balarabe Musa ya kafa a kananan hukumomi 14 shekara 42 da sauka wuce. Mallam Dikko Raɗda ya nuna takaicin sa ganin shugabannin da su ka gabata ba su yi wani yunƙuri na farfaɗo da kamfanin ba. Ya ce gwamnatin sa…
Read More
Rundunar soja za ta binciki tsohon kwamandanta na Kano kan zargin sama da faɗi da kuɗin ƙananan sojoji

Rundunar soja za ta binciki tsohon kwamandanta na Kano kan zargin sama da faɗi da kuɗin ƙananan sojoji

Hedikwatar sojojin Nijeriya ta fara gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa tsohon kwamandan Birged na 3 a Kano, Birgediya Janar M.A. Sadiq. Wakilinmu ya tattaro cewa an sallami janar ɗin ne biyo bayan tuhumar da ake masa na ƙin biyan wasu haƙƙoƙin da ke ƙarƙashinsa, tare da wasu zarge-zarge na almundahana a lokacin da yake riƙe da muƙamin kwamanda. Wata majiya ta soji ta shaida wa wakilinmu cewa Janar ɗin na ci gaba da zama a tsare kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. Da aka tuntuɓi daraktan yaɗa labarai na tsaro, Birgediya Janar…
Read More

NNPC ya ƙara kuɗin litar fetur a Abuja da Legas

Daga BELLO A. BABAJI Gidajen man fetur mallakar kamfanin NNPCL, sun ƙara farashin kowacce lita a jihohin Abuja da Legas. Kafin yanzu, ana sayar da litar ne akan N897 wanda yanzu kuma an mayar da shi zuwa N1,030 a Abuja. A yankin Maitama da ke Abuja, an ruwaito cewa mutane sun yi cincirindo wajen sayan man inda suke ta ƙorafi game da ƙarin. 'News Point Nigeria' ta ruwaito cewa masu sayan man sun ɗauki tsawon lokaci su na jira don a fara sayar da man a yankin Gudu na Abuja inda wani ma'aikaci ya ce ana aikin mayar da na'urar…
Read More
Yan bindiga sun kashe Sarkin Kanya a Jihar Kebbi

Yan bindiga sun kashe Sarkin Kanya a Jihar Kebbi

' Daga USMAN KAROFI 'Yan bindiga sun kashe Sarkin Kanya Alhaji Isah Akiyu, na ƙaramar hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi bayan sun yi garkuwa da shi. 'Yan bindigan sun fara neman kuɗin fansa domin sakin Sarkin Kanya. Duk da ƙoƙarin al’ummar yankin wajen tattaunawa domin dawowarsa lafiya, masu garkuwan sun kashe shi, kisan gilla. Kisan wannan basaraken gargajiya ya girgiza garin Danko Wasagu da kewaye, yayin da mazauna yankin ke alhini tare da bayyana tsoro game da ƙaruwar ayyukan 'yan bindiga a Jihar Kebbi. Mutane da dama sun yi kira ga gwamnati da jami'an tsaro da su ƙara himma…
Read More

Ɗan-Isan Zazzau ya rasu a hatsarin mota

Daga BELLO A. BABAJI An samu rahoton rasuwar Yariman Masarautar Zazzau kuma Ɗan-Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris bayan aukuwar wani hatsari akan hanyar Abuja-Kaduna da daren nan. Kakakin Masarautar, Malam Abdullahi Aliyu Kwarbai ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Mamacin, mai shekaru 41, ya rayu ne da mata ɗaya da ƴaƴa biyu. Kafin rasuwarsa, shi ne Mataimakin Sakataren Majalisar Masarautar. A kwanakin baya ne mahaifiyarsa, Hajiya Habiba Shehu Idris, wacce ita ce mahaifiya ga Sarki na yanzu, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ta rasu. Wakilin Blueprint ya ce iyalan mamacin za su sanar da lokacin da za…
Read More
Jami’ar koyon kiwon lafiya a Katsina za ta fara karatu kafin ƙarshen shekara

Jami’ar koyon kiwon lafiya a Katsina za ta fara karatu kafin ƙarshen shekara

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban kwamitin TETFUND a majalisar dattijai sanata Muntari Ɗandutse ya sanar da cewa shirye shirye ya kammala na fara karantar wa a jami'ar koyon kiwon lafiya na garin Funtua a Jihar Katsina. Ya ce ɗalibai 60 za su fara karatu a kowane tsangaya da hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa ta amincewa. Sanata Ɗandutse ya ce tuni gwamnatin Jihar Katsina ta amince da bawa jami'ar Naira biliyan biyu domin fara wasu aikace aikace na fara zangon karatu a jami'ar. Sanatan ya yaba da irin kyakkyawar shugaban ci na Malam Dikko Raɗda akan ƙoƙarin da yake…
Read More
An kama mai unguwa da laifin ba ‘yan ta’adda bayanan sirri a Katsina

An kama mai unguwa da laifin ba ‘yan ta’adda bayanan sirri a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina. 'Yan sanda a garin runka na ƙaramar hukumar Safana sun kama mutane biyu a cikin su har da mai unguwa da taimakawa 'yan ta'adda da bayanan sirri. Mai magana da yawun 'yan sanda ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana haka a lokacin da ya gabatar da masu laifin a gaban manema labarai. Mai unguwar ƙauyen Runka Usman Adamu mai shekara 45 da haihuwa ya tabbatar da zargin da ake masa, ya bayyana wa BBC cewa abokin hirar sa Rabe ne ya gabatar dashi ga ɗaya daga cikin ɓarayin daji mai suna Umar. Ya kuma tabbatar…
Read More

An kori ɗan Osama Bin Laden daga Faransa

Daga BELLO A. BABAJI Hukumomin ƙasar Faransa sun umarci Omar, wanda ɗan sanannen Shugaban ƴan ƙungiyar Al-Ƙa'ida, Osama Bin Laden ne da ya fice daga ƙasar. Omar, mai shekaru 43, an buƙaci ya yi hakan ne ta kafar sada zumunta kamar yadda Ministan Harkokin Cikin gida na ƙasar, Bruno Retailleau ya bayyana. An haifi Omar ne a ƙasar Saudiyya wanda ya kuma taɓa zama a Sudan da Afghanistan. Sun kuma rabu da mahaifin nasa a lokacin da ya ke da shekara 19 a duniya inda daga bisani a shekarar 2016 ya koma yankin Normandy da ke Arewacin Faransa. Saidai, Minista…
Read More

‘Yan sanda sun ceto mutane takwas da ƴan bindiga suka yi yunƙurin sacewa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƴan sanda a Katsina sun daƙile yunƙurin da ƴan bindiga suka yi na sace mutane a ƙananan hukumomin Faskari da Ɗan-Musa. A Ɗan-Musa, ƴan bindigar sun tare mata su biyu a ƙauyen Matarau da ke kan hanyar Ƴan-Tumaki zuwa garin Ɗan-Musa, inda ƴan sandan suka kai wa matan ɗauki tare da yin ɗauki ba daɗi da ƴan bindigar har sai da suka samu nasarar ceto matan. A Faskari kuwa ASP Sadiq Aliyu wanda shi ne Kakakin ƴan sandan jihar, ya ce ƴan bindigar sun tare hanyar ƙauyen Marabar Bangare da Unguwar Kafa a kusa da…
Read More