Labarai

Civil Defence ta ƙara wa jami’ai 167 girma a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Hukumar tsaro ta Civil Defence ta ƙara wa jami'anta a da ke faɗin Nijeriya girma a matakai daban-daban, inda a jihar Katsina jami'ai 167 suka samu shiga cikin sahun. Cikin waɗanda suka sumu ƙarin girman akwai mai magana da yawun hukumar a Katsina, DSC Buhari Hamisu wanda ya zama SC Buhari Hamisu a yanzu kamar yadda ya bayyana a wata takarda. Ya ce, nan ba da jimawa ba za a yi bikin ƙarin girman a hedikwatar hukumar ta jihar Katsina.
Read More

Gwamnatin Katsina za ta samar da rumbunan sauƙi a ƙananan hukumomin jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A zaman Majalisar Zartarwa karo na goma ƙarƙashin jagorancin gwamna Dikko Raɗɗa, ta amince da ƙirƙiro rumfar sauƙin. Da ya ke hira da manema labarai jim-kaɗan bayan kammala taron majalisar, mai bai wa gwamna shawara kan ci-gaban karkara, Injiniya Yakubu Nuhu Ɗanja, ya ce gwamnatin da amince da haka ne domin sauƙaƙa wa al'umma duba da yanayi na matsi da ake fama shi. Ya kuma ce, gwamnatin na duba yiwuwar faɗaɗa ƙirƙiro rumbun hatsi a kowacce mazaɓa 361 na jihar. Injiniya Ɗanja ya ƙara da cewa, Gwamna Raɗɗa ya bada umurni da a ƙirƙiro rumfar…
Read More
Amaechi ya fusata kan yadda ‘yan Nijeriya ba su tashi tsaye ba kan jefa su cikin tsadar rayuwa

Amaechi ya fusata kan yadda ‘yan Nijeriya ba su tashi tsaye ba kan jefa su cikin tsadar rayuwa

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana rashin jin daɗinsa da yadda jama’a ke nuna halin ko in kula dangane da matsanancin matsin tattalin arziki. Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na ABN TV, Amaechi ya yi tambaya kan dalilin da ya sa ‘yan Najeriya ba su nuna fushin su ba, domin ya ce,abubuwa sun yi tsadar da shi kanshi yanzu fama yake da har ta kai ba shi da kuɗin man dizal. “Ina fushi da ’yan ƙasa. Na sha faɗin hakan. Za su ga mutane suna sace masu kuɗi suna talauta su, amm ba za su…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa da Naira bilyan biyu

Gwamnatin Katsina za ta tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa da Naira bilyan biyu

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta sha alwashin rabawa waɗanda ambaliyar ruwa na bana ya rutsa da su, tallafin kuɗi Naira bilyan biyu. Gwamnan Jihar Dikko Umar Raɗɗa ne ya bayyana haka a yayin ƙaddamar da rabon tallafin shinkafa ga wasu daga cikin al'ummar jihar. Bankin masana’antu (BOI) ne ya bada tallafin shinkafar, inda aka raba sama da buhu 2,000 ga mabuƙata a ƙarshen makon nan. Raɗɗa ya ce, an ware Naira biliyan biyu ne domin tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa don sake gina gidajensu da kuma kasuwancinsu. Yayin da gwamnan ke yabawa bankin masana'antu kan…
Read More

Kotu ta jaddada dakatar da Aminu Ado Bayero daga gyara Fadar Nassarawa

Daga BELLO A. BABAJI Wata babbar kotun tarayya da ke Jihar Kano ta jaddada dakatar da Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero daga aikin gyaran ƙaramar Fadar Nassarawa. Gwamnatin jihar Kano, Antoni Janar na jihar da kuma Majalisar Masarautar Kano suka shigar da ƙarar dakatarwar ta hannun wani babban lauyan Nijeriya (SAN), Rilwanu Umar. A yayin hukuncinta, Alƙalin Alƙalan Kano, Mai Shari'a Dije Abdu Aboki ta tabbatar da buƙatar waɗanda suka shigar da ƙarar tare da umartar a mayar da ƙarar zuwa babbar kotu ta 15 don cigaba da sauraro. Haka nan, a cikin takardar, masu shigar da…
Read More
Rundunar ‘yan sandan Kano ta cafke mutum uku da ake zargin sun kashe matashi

Rundunar ‘yan sandan Kano ta cafke mutum uku da ake zargin sun kashe matashi

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta cafke wasu mutane uku da ake zargi da kashe wani matashi mai suna Ɗahiru Musa ɗan shekaru 32 da haihuwa a unguwar Ɗorayi Quarters Kano. Waɗanda ake zargin sun yi wa Musa ƙarya ne, inda suka sanya masa guba, sannan suka ƙona gawarsa da nufin lalata shaida. Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Kano. Haruna ya bayyana cewa Waɗanda ake zargin, Aliyu Adamu mai shekaru 22, Mubarak Abdulsalam mai shekaru 20 da Sadiq Sunusi mai shekaru 19. A halin yanzu…
Read More

Ƙudirin bai wa jami’an kiyaye haɗura bindigu ya tsallake karatu na biyu a majalisa

Daga BELLO A. BABAJI Wani ƙudiri da ke neman a samar da jami'ai na musamman a Hukumar kiyaye haɗura, FRSC da kuma inganta ta ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai. Ƴan majalisa Abiodun Derin Adesida da Olaide Lateef Muhammed ne suka ɗauki nauyin ƙudirin don a yi gyara ga dokar FRSC da za ta bada damar samar da 'Special Armed Squad'. Haka kuma, ƙudirin ya ƙunshi inganta jami'ai da ke da muƙamin 'Deputy Corp Marshall' ta hanyar amfana daga ribar yin ritaya da kuma inganta harkokin gudanarwa na ayyukansu. Sannan, ya ƙunshi a ba su iko na hana…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta wanke kanta a ƙarin farashin fetur, ta ce daga kasuwar duniya ne

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta nesanta kanta daga batun ƙarin farashin litar fetur, ta ce hakan ya faru ne sakamakon sauye-sauye da ake samu a kasuwannin duniya da kuma hukunci da kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya yi. A wata hira da jaridar Daily Trust, Ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin tarayya ba ta bai wa NNPCL umarnin haka ba, ya na mai cewa hakan na faruwa ne sakamakon jujjuyawar kasuwannin duniya da kuma rashin ikon kamfanin na bada farashin fetur la'akari da dokar sayar da man fetur ta ƙasa. Ya…
Read More

NLC ta buƙaci a gaggauta cire ƙarin da aka yi wa farashin fetur

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta nemi a cire ƙarin da aka yi ga kuɗin litar fetur a Nijeriya, ta ce hakan na ƙara talauta al'umma. A ranar Laraba ne kamfanin man NNPCL ya sanar da sabon farashin litar fetur wanda ya koma daga N898 zuwa sama da N1,030. Shugaban NLC, Joe Ajaero ya bayyana takaicinsa ganin yadda farashin fetur ke ƙaruwa a duk wata tare da cewa ba a kai ga zartar da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata ba a ƙasar. Cikin wata sanarwa da NLC ta fitar, Ajaero ya bayyana rashin jin daɗinsa…
Read More
Jama’a sun ƙaurace wa zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Filato

Jama’a sun ƙaurace wa zaɓen ƙananan hukumomi a Jihar Filato

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos Masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da zaɓe a Jihar Filato sun bayyana rashin jin daɗin su da yadda jama'a suka ƙaurace wa zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a dukkan faɗin jihar, a ranar Laraba 9 ga watan Oktoba, 2024, sakamakon rashin fita su kaɗa ƙuri'ar su ga ƴan takarar da suke so. Wakilinmu da ya kewaya cikin garin Jos don ganin yadda zaɓen ke gudana, ya lura da yadda aka bar masu aikin zaɓe suke zaune suna gyangyaɗi babu masu zuwa zaɓe. Wata jami'ar zaɓe Juliana Jonah da ta yi aiki a…
Read More