Labarai

Rikicin Ribas: Kotun Ɗaukaka ƙara ta dawo da ƴan ɓangaren Wike da haramta kasafin Fubara na 2024

Daga BELLO A. BABAJI Kotun Ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin wata ƙaramar kotu da ta yi na haramta miƙa kasafin kuɗin Jihar Ribas na 2024 da ƴan Majalisar Dokoki huɗu suka yi. Cikin hukuncinsa, Mai Shari'a Joseph Oyewole ya ce ɗaukaka ƙarar da Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya yi da ke neman a soke hukuncin ranar 22 ga watan Janairu, ba shi da inganci. Alƙalin, a lokacin da ya ke bayyana rashin halaccin kasafin Naira biliyan 800 da ƴan majalisa huɗun suka yi, ya ce tunda Fubara ya janye duka takardun da ya shigar game da…
Read More
Matatun mai uku sun shirya samar da fetur saboda biyan ɗanyen mai da Naira

Matatun mai uku sun shirya samar da fetur saboda biyan ɗanyen mai da Naira

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A makon nan ne Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPCL, ya fara samar da ɗanyen mai a naira ga matatar man Dangote bayan sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta yi na cewa an fara cinikin ɗanyen man fetur a naira. Haka kuma, biyo bayan alƙawarin da gwamnati ta yi, wasu matatun mai guda uku suna shirin fara samar da man fetur. Matatun man guda uku sun haɗa da ganga 11,000 a kowace rana mai ƙarfin matatar mai na Aradel da ke jihar Ribas; Matatar mai mai aarfin 20,000 Clairgold a jihar Delta; da Azikel mai ƙarfin 12,000…
Read More
Dalilin jihohi na karɓar rance duk da kasonsu na Asusun Tarayya

Dalilin jihohi na karɓar rance duk da kasonsu na Asusun Tarayya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alƙaluma daga Ofishin Kula da Basussuka (DMO) sun nuna cewa a cikin watanni shida na farko bayan hawansu mulki, sabbin gwamnoni 13 sun karɓi bashin Naira biliyan 226.8 daga hannun masu kuɗi na cikin gida da waje. A ci gaba da nazarin alƙaluman, an kuma nuna cewa ƙarin wasu gwamnoni 16 ne suka bayar da gudunmawa wajen ƙaruwar basussukan, ta hanyar ƙara adadin basussukan jihohinsu da Naira biliyan 509.3, wanda ya ƙunshi Naira biliyan 243.95 daga masu lamuni na cikin gida da kuma Dala miliyan 298.5 (N265.37) daga ƙasashen waje da hukumomi kamar Bankin Duniya da…
Read More
Ban yi nadamar juya wa PDP baya ba a zaɓen 2023 – Wike

Ban yi nadamar juya wa PDP baya ba a zaɓen 2023 – Wike

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, a ranar Talata ya ce bai yi nadamar juya wa jam’iyyar PDP baya ba a zaɓen shugaban ƙasa na 2023. Wike, wanda ya yi magana a gidan Talabijin na Channels a shirin siyasa A Yau, ya musanta cewa yana aikata ayyukan da bai dace ba ta hanyar ƙin goyon bayan Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a lokacin. Ya kare matakin da ya ɗauka, inda ya ce an ɗauki matakin ne domin a yi adalci da gaskiya. “A zaɓen shugaban ƙasa, na ce zan goyi bayan daidaito,…
Read More
Nijeriya ta fara sayar da ɗanyen mai da Naira ga matatar Ɗangote

Nijeriya ta fara sayar da ɗanyen mai da Naira ga matatar Ɗangote

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta ce ƙasar ta fara sayar da ɗanyen mai da tataccen mai da kuɗin nairar Nijeriya. Ministan Kuɗi da Tattalin Arzikin na ƙasar, Wale Edun ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ma'aikatar kuɗin ƙasar, ta wallafa a shafinta na ɗ ranar Asabar. Sanarwar ta ce an fara sayar da ɗanyen man da kuɗin naira ne tun daga ranar ɗaya ga watan Okotoban da muke ciki. Ministan ya ce hakan na daga cikin matakin da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka da ake sa ran zai haɓa tattalin arzikin ƙasar da ci gaba da…
Read More
Ku tuba ko mu aika ku lahira — Matawalle ga masu ba ’yan ta’adda bayanai

Ku tuba ko mu aika ku lahira — Matawalle ga masu ba ’yan ta’adda bayanai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Karamin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya gargaɗi masu ba wa ’yan ta’adda bayanai cewa su tuba ko su gamu da ajalinsu. Ya yi wannan gargaɗin ne a ƙauyen Gundumi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa ƙananan hukumomin Isa da Sabon Birni a jihar Sakkwato domin ziyarar gani da ido a ranar Alhamis. Ministan wanda ya nuna baƙin cikinsa kan yadda rayuwa ta koma a ƙauyen, ya ce “wannan wurin a da ya kasance yana da walwala da harkoki da dama. “Ina tabbatar muku za ta dawo, za mu kawo wani sansanin…
Read More
Mun gina matatarmu ne babu tallafin gwamnati – Ɗangote

Mun gina matatarmu ne babu tallafin gwamnati – Ɗangote

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote a ranar Talata ya bayyana cewa an gina matatar man Dangote ba tare da tallafin gwamnati ba. Ɗangote ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron ƙungiyar masu matatun mai ta Nijeriya, CORAN, a Legas. Taron dai yana da taken, "Mayar da Nijeriya a matsayin mai fitar da albarkatun man fetur." Ɗangote, wanda ya samu wakilcin Ahmed Mansur, rukunin Dangote, ya ce akwai buƙatar ƙarfafa gwiwar masu zuba jari don cimma burin ƙasar nan na zama cibiyar tace mai ta duniya. Ya jaddada muhimmancin tabbatar da…
Read More
Soyinka ya ce babu Allah

Soyinka ya ce babu Allah

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Fitaccen marubucin adabi, Farfesa Wole Soyinka, ya ce, ya amince a kira shi wanda bai yarda akwai Allah ba, kuma ya bayyana dalilin da ya sa ya fi son addinin Orisa na gargajiya. A yayin da ya ke bayyana hakan a wata hira da ya yi da Larry Madowo na CNN a baya-bayan nan, fitaccen marubucin adabin ya ce zurfin imani a Musulunci da Kiristanci bai dace da bautar Orisa da yake yi ba, ya ƙara da cewa Orisa ya fi burge shi. A cewarsa, bautar Orisa na ɗaya daga cikin addinan Afirka da ke guje…
Read More

Cin zarafi: An yanke wa wani ɗan Lebanon hukuncin shekaru 14 a kurkuku a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Wata babbar kotun tarayya da ke Jihar Kano ta yanke wa wani ɗan ƙasar Labanon, Zuhier R. Akar mai shekaru 67 hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekaru 14 sakamakon lalata wasu yara mata biyu. Hukumar hana fataucin ɗan-adam (NAPTIP) reshen jihar, ta tsare Aktar ne wanda ke zama a yankin Gidan Wanka da ke ƙaramar hukumar Fagge da laifuka biyu da ke da alaƙa da lalata. A lokacin gudanar da hukuncin, Mai Shari'a S. M. Shua'ibu ya ce an tabbatar da wanda ake tuhuma da aikata laifin inda ya zartar masa da hukuncin zama…
Read More

Halin da Nijeriya ke ciki ba daga Tinubu ba ne – Matar shugaban ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Matar shugaban ƙasa, Sanata Remi Tinubu ta ce halin da Nijeriya ke ciki a yanzu, ba mijinta Shugaba Bola Tinubu ba ne ya haddasa. Ta ce, mijin nata ya duƙufa ne wajen samar da daidaito ga al'amuran da suka taɓarɓare a Nijeriya a cikin shekaru biyu da ya ke kan mulki. Ta bayyana hakan ne a Fadar Ooni Ile-Ife ta jihar Osun a lokacin da ta kai ziyara ga sarkin inda daga bisani da ƙaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita 2.7 da kuma buɗe wajen taro da aka sanya wa sunanta a jami'ar Obafemi Awolowo.…
Read More