Labarai

Har yanzu mafi yawancin gidajen mai ba su karɓi fetur daga matatar Ɗangote ba – IPMAN

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da aka kammala sati guda da kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL ke dakon man fetur daga matatar Ɗangote, mafi yawancin gidajen mai ba su samu man ba. Ƙungiyar ƴan kasuwar fetur mai zaman kanta ta Ƙasa (IPMAN) wacce ke wakiltar kashi 70 na gidajen man Nijeriya ta bayyana hakan duk da cewa matatar ta fara sayar wa NNPCL. Shugaban ƙungiyar, Abubakar Maigandi ya ce har yanzu su na jiran samun fetur daga matatar. A ranar Lahadi da ta gabata ne, NNPCL ya fara dakon fetur daga matatar Ɗangote wacce ke iya fitar da ganga…
Read More

Shettima ya tafi Amurka don halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 79

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bar Abuja don tafiya zuwa ƙasar Amurka domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 (UNGA). Cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nwocha (ta ofishin mataimakin shugaban ƙasa) ya fitar, ya ce Shettima ya tafi taron ne bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ya ce, Shugaban ya umarci mataimakin nasa ya halarci taron ne don zai mayar da hankali kan al'amuran cikin gida musamman game da annobar ambaliya da ke faruwa a wasu sassan Nijeriya a halin da ake…
Read More

Zaɓen Edo: INEC za ta yi bincike game da zargin sauya sakamako

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC), ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike game da zargin sauya sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Edo da a ke gaf da kammala sanar da sakamakonsa. Kamar yadda ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta tabbatar wa al'umma cewa za ta yi bincike kan zargin. Kawo yanzu, al'umma su na jiran su ji wani hukunci INEC za ta yi yayin da a ke fatan adalci. A yanzu haka, hukumar ta fitar da kashi 96.59 na sakamakon zaɓen gwamnan jihar a shafinta na yanar gizo.
Read More
Zaɓen Edo: Obaseki ya faɗi a  ƙaramar hukumarsa

Zaɓen Edo: Obaseki ya faɗi a ƙaramar hukumarsa

Gwamna Godwin Obaseki ya sha kaye a ƙaramar hukumar sa ta Oredo a hannun jam'iyyar APC kamar yadda hukumar zaɓe ta sanar. A sakamakon da hukumar zaɓen ta bayyana, ɗan takarar APC ya samu ƙuri'u 30,780 inda ɗan takarar PDP ya samu 24,938, sai ɗan takarar jam’iyyar LP yayi na uku da kuri'a 5,389. yanzu haka hukumar zaɓen ta cigaba da sanar sauran sakamakon daga sauran ƙananan hukumomin jihar.
Read More
Sanata Ɗandutse ya taya Katsinawa murnar cika shekara 37 da ƙiƙiro Jihar Katsina

Sanata Ɗandutse ya taya Katsinawa murnar cika shekara 37 da ƙiƙiro Jihar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sanata Muntari Ɗandutse mai wakiltar shiyar Funtua ya taya gwamna Dikko Raɗɗa da al'ummar jihar Katsina murnar cika shekara 37 da ƙirƙiro jihar. A wata takardar sanarwar ɗauke da sa hannun sanatan, ya jinjina wa shugabanin baya da suka jagoranci jihar da irin jagoranci na gari da suka nuna da yasa jihar tayi zarra. Haka kuma ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa da irin gagarumar nasarar da ya suma wajan daƙile ta'addanci a kudancin jihar da yanzu an fara samun zaman lafiya. Ɗandutse ya jinjina wa gwamnan akan harkan ilimi, musamman ɗaukan malaman makarantar firamare guda…
Read More
Magoya bayan PDP na zanga-zanga a ofishin INEC a Edo

Magoya bayan PDP na zanga-zanga a ofishin INEC a Edo

Yayin da al'ummar Jihar Edo ke dakon sanar da sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar jiya, magogya bayan jam'iyyar PDP sun yi wata zanga-zanga ne a ofishin INEC da ke babban birnin ta Benin domin nuna rashin jin daɗin su kan yadda sakamakon zaɓen ya ke fita. A sakamakon zaɓen da hukumar INEC ta fitar daga ƙananan hukumomi 16 daga cikin 18, jam'iyyar APC ta samu nasara a ƙananan hukumomi 10 yayin da PDP tai nasara a shida. Wannan sakamakon ya janyo cece-kuce da ya sa magogya bayan PDP zagaye harabar su na ɗaga ganye suna waƙe. Masu zanga-zangar na…
Read More

Zaɓen Edo: Wakilin PDP ya zargi INEC da haɗa kaso 90 na ƙuri’un ƙarya

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Edo, Osiagbovo Iyoha ya tada batun zargi mai ƙarfi game da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ake gaf da sanar da wanda ya yi nasara. Iyoha wanda shi ne wakilin jam'iyyar PDP a jihar, ya yi zargin cewa kashi 90 na sakamakon zaɓen daga hukumar zaɓe, INEC ya ke, ya na mai cewa ƙirƙirar sakamakon aka yi. Ya bayyana hakan ne a lokacin da a ke shirin karɓar sakamakon zaɓen ƙaramar hukumar Etsako ta Tsakiya wanda kuma shi ne na ƙarshe. Ya ce, akwai wata jami'iyyar da ke da iko…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: APC na kan gaba a zaɓen gwamnan Edo

Daga BELLO A. BABAJI Yayin da ake cigaba da ƙirga ƙuri'u da aka kaɗa a zaɓen gwamnan jihar Edo a ranar Asabar, ɗan takarar jam'iyyar APC, Monday Okpebholo ya na kan gaba. Sakamakon zaɓe na ƙananan hukumomi 16 cikin 18 na jihar kamar yadda hukumar zaɓe, INEC ta sanar, Okpebholo ya samu ƙuri'u 244,549 yayin da takwaransa na jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo ke na biyu da ƙuri'u 195,954. Olumide Akpata na jam'iyyar LP ya samu ƙuri'u 13,348. Kawo yanzu INEC ta je hutun sa'o'i uku don jiran sakamakon zaɓen sauran ƙananan hukumomi biyu da suka rage.
Read More

Kira ga saka dokar ta-ɓaci a Zamfara da APC ta yi rashin mutumta Zamfarawa ne – PDP

Daga BELLO A. BABAJI Kira da ɓangaren jami'yyar APC ƙarƙashin jagorancin tsoffin gwamnonin Zamfara, Bello Matawalle da Sanata Abdulaziz Yari suka yi na a sanya dokar ta-ɓaci jihar, alamu ne da ke nuna ƙiyayyarsu a fili game da ayyukan ci gaba da aka samu ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar, Dauda Lawal Dare. Wata takarda da Sakataren hulɗa da jama'a na PDP, Halliru Andi ya fitar, ta ce jam'iyyar PDP ta mayar da hankali wajen gyara ɓarnar da gwamnatocin APC ta yi na tsawon shekaru 25 wanda hakan ya nuna yadda nasarorin gwamna Dauda Lawal suka zama barazana ga APC a yunƙurinta…
Read More
Zaɓen Edo: ‘Yan sanda da sojoji sun fitar da Obaseki daga ofishin INEC

Zaɓen Edo: ‘Yan sanda da sojoji sun fitar da Obaseki daga ofishin INEC

Tawagar ‘yan sanda da sojoji sun yi wa gwamnan jihar Edo, Mista Godwin Obaseki rakiya daga babban ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ke birnin Benin. Mataimakin Sufeto Janar (DIG), Frank Mba, ya fitar da Obaseki daga harabar da karfe 4:10 na safiyar Lahadi. Gwamnan ya isa ofishin hukumar zaɓen ne da misalin karfe 2 na safe, inda yake nuna rashin amincewarsa da rashin bayyana sakamakon zaɓen ƙaramar hukumarsa ta Oredo. Sai dai an ce jami'ai sun sanar da shi cewa bai kamata ya kasance a harabar ba. Sai dai an ce gwamnan ya dage da…
Read More