Labarai

PDP ta koka kan zargin katsalandan a tattara sakamakon zaɓen Edo

PDP ta koka kan zargin katsalandan a tattara sakamakon zaɓen Edo

Shugaban yaƙin neman zaɓen Gwamnan Jihar Edo, kuma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umar Fintiri, na jam’iyyar PDP, ya fitar da sakamakon da ya samu a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar. Fintiri wanda ya karanta wa ‘yan jarida sakamakon a wani taron manema labarai a birnin Benin, ya ce; "Duk wani abu da za ayi bayan wannan zai kasance ba bisa ƙa'ida ba, ya zama cin zarafi ne da son rai da cin mutuncin dokar zaɓe ta 2022." Gwamna Godwin Obaseki (Edo) Sheriff Oboriworhe (Delta) da Agbu Kefas (Taraba), sun kasance tare a daidai lokacin da yake ya ke…
Read More

Jami’an tsaro sun halaka ƙanin ƙasurgumin ɗan bindiga, Usman Moɗi-Moɗi

Daga UMAR GARBA a Katsina A cigaba da samun nasarar murƙushe ƴan ta'adda da jami'an tsaro ke yi a Arewa-maso-Yammacin ƙasar nan, ƴan sanda sun halaka mashahurin mai garkuwa da mutane a Katsina, wato Ɗan Ƙundu wanda ƙane ne ga ƙasurgumin ɗan ta'adda, Usman Moɗi-moɗi. A wani gagarumin aikin dawo da tsaro da rundunar ƴan sandan Najeriya ta gudanar a jihar Katsina, ta yi nasarar kashe Ɗan Ƙundu. Ƙundu ya shahara ta fannin ta'addanci a dajin Tsaskiya na ƙaramar hukumar Safana. A cewar Zagazola Makama, mai sharhi kan harkokin tsaro kuma masani kan yaƙi da tada ƙayar baya a yankin…
Read More

Mutane tara sun mutu bayan ɓarkewar kwalera a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mutane tara ne suka rasa rayukansu a ƙaramar hukumar Sandamu da ke Jihar Katsina sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa da aka fi sani da kwalera a wasu ƙauyuka. Shugaban ƙaramar hukumar Usman Nalado ya sanar wa manema labarai hakan inda ya ce tuni ya kai rahoton afkuwar lamarin ga hukumar kiwon lafiya a matakin farko. Ya ce, jami'an hukumar sun ziyarci ƙauyukan da abin ya shafa a ƙaramar hukumar domin gane wa idanunsu. Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Sandamu da Daura, Aminu Jamo ya kai tallafin kayan abinci da kuɗi don a…
Read More

Cika shekaru 37 da ƙirƙiro Jihar Katsina: Sheikh Pantami zai gabatar da wa’azi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Daga cikin bukukuwan cika shekara 37 da ƙirƙiro Jihar Katsina, ana sa ran tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami zai gabatar da wa'azi a Katsina mai taken 'Riƙon Amana'. Manufar zaɓo taken wa'azin shi ne a tunatar da masu madafun iko a jihar su san mahimmancin riƙon amana da nauyin da Allah ya ɗora masu wajen jagoranci. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al'adu, Dakta Salisu Bala Zango ya sanar da haka da ya ke hira da manema labarai akan irin shirye-shiryen da aka tsara a ranakun bukukuwan. Ya ce, akwai taro na musamman wanda…
Read More

Ranar Zaman Lafiya ta Duniya: Zaman lafiya wajibi ne ba zaɓi ba – Shugaban ƴan sintiri

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ranar 21 ga watan Satumbar kowacce shekara, ita ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware a matsayin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya. Ranar na mayar da hankali ne wajen kawo mafita kan tashe-tashen hankula da a ke fama da su na banbancin addini, yare da kuma ƙabilu a faɗin duniya. Sai dai, bikin a bana ya zo lokacin da ake tsaka da fama da matsalar rashin tsaro a sassan ƙasar nan musamman na hare-haren ƴan bindiga da garkuwa da mutane. Shugaba kuma Babban Kwamandan Ƙungiyar ƴan Sintiri ta Nijeriya (VGN), Kyaftin na sojan ruwa (mai ritaya), Abubakar…
Read More

INEC ta shigar da sama da kaso 88 na sakamakon zaɓen Edo a IReV

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta shigar da sama da kashi 88 na sakamakon zaɓen gwamna da ke gudana a jihar Edo a sahfinta na yanar gizo (IReV). Cikin mazaɓu 4,519, INEC ta samu shigar da sakamakon mazaɓu 3,995 zuwa ƙarfe 6:40 na yamma a ranar Asabar. A ranar 21 ga watan Satumba ne al'umma ke gudanar zaɓen kujerar gwamnan jihar ne kasancewar wa'adin gwamna mai ci, Godwin Obaseki na shekaru takwas zai ƙare a ranar 12 ga watan Nuwamba, 2024. Jihar Edo na ɗaya daga cikin jihohin da ke gudanar da zaɓen gwamna a wani…
Read More
Ƙungiyoyin mata sun buƙaci a inganta samar da abinci mai gina jiki ga ƙananan yara

Ƙungiyoyin mata sun buƙaci a inganta samar da abinci mai gina jiki ga ƙananan yara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ƙungiyoyin addini masu zaman kansu na mata sun yi kira da a inganta abinci mai gina jiki ga jarirai da ƙananan yara a ƙasar. Shugabannin ƙungiyar Mata Musulmi ta Nijeriya; Sakatariyar Katolika ta Nijeriya; ƙungiyar Matan Kirista ta Nijeriya; da kuma Cocin 'Redeemed Christian Church of God' sun yi wannan kiran ne a lokacin ziyarar da su ka kai na bada shawarwari ta hanyar Cibiyar Sadarwa da Tasirin zamantakewa, ga mata a wasu yankuna, tare da kira da a inganci abincin da mata ke ci domin su samu damar bai wa jarirai abinci mai gina…
Read More

An fara ƙirga ƙuri’u bayan INEC ta ƙara lokacin zaɓe a wasu yankuna a Edo

Daga BELLO A. BABAJI Bayan watanni ana yawon neman zaɓen kujerar gwamnan Jihar Edo, a yau ne a ke kaɗai kuri'a don sauya gwamanti mai ci kasancewar wa'adinta ya zo ƙarshe. Jam'iyyu 17 ne hukumar zaɓe, INEC ta tantance waɗanda ke gwabzawa a zaɓen don karɓar ragamar mulkin daga hannun gwamna Godwin Obaseki wanda wa'adinsa zai ƙare a watan Nuwamba. Ɗan takara Asue Ighodalo na jam'iyyar PDP da Monday Okpebholo na APC da kuma Olumide Akpata na LP su ne manyan ƴan takarar kujerar. A na gudanar da zaɓen ne a mazaɓu 4,519 a ƙananan hukumomi 18 na jihar. Tsohon…
Read More

Na hannun daman tsohon gwamnan Legas Jakande ya samu karramawa ta DRTS a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Mai taimaka wa marigayi tsohon gwamnan jihar Legas (Dakta Lateef Kayode Jakande), Kwamared Salihu Ɗantata Mahmud ya shiga sahun waɗanda suka samu lambar yabo daga ɓangaren wasanni na ofishin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa DRTS. Mista Andrew Agbasi shi ne shugaban reshen wasannin inda Daraktan hukumar, Dakta Abdullateef Bello shi ya gabatar da kyautukan lambobin yabon inda ya yaba wa Salihu kan taimakonsa ga ofishin wajen ƙarfafa alaƙa da ke tsakanin ɓangaren da ofishin labarai. Ya yi kira gare shi da ya faɗaɗa taimakonsa na wasanni zuwa sabon tsarin aiki na kwana uku da jami'an…
Read More

Sai da Matawalle ya rantse da Ƙur’ani kan bai da alaƙa da ƴan bindiga – Shinkafi ga gwamnan Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Zamfara kuma mai taimaka wa tsohon gwamna Bello Matawalle na musamman, Sani Shinkafi ya gargaɗi gwamna mai ci a yanzu na jihar, Dauda Lawal ya ƙaurace wa yaɗa zargin ƙarya akan takwarorinsa na siyasa a jihar. Ya ce, wasu daga cikin ayyukan gwamnan sun nuna kamar bai san doka ba kuma ya na shakkar bayanan matsayin ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle. Shinkafi ya buƙaci gwamnan ya fito ya bayyana matsayarsa game da wani jawabi da aka ce ya bazu a kafafen sadarwa da ke nuna cewa gwamnatinsa na da alaƙa…
Read More