Labarai

Masarautar Katsina ta yi naɗe-naɗen muƙamai

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmummuni Kabir Usman ya naɗa mataimakin gwamnan Jihar Katsina, Farouk Lawal Joɓe a matsayin Sarkin Fulanin Joɓe. Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar, Alhaji Jabiru Salisu Tsauri shi aka bai wa matsayin lamiɗon Katsina. Akwai kuma shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Matazu da Musawa, Alhaji Abdullahi Aliyu a matsayin Dujuman Katsina. A jawabinsa bayan naɗin nasu, Sarkin ya nuna jin-daɗinsa ganin yadda manyan jami'an gwamnati ke nuna sha'awarsu ta shiga harkar Masarautar Katsina da Daura. Ya ce, babu shakka haka zai kawo karin fahimta…
Read More
Shugabanci nagari ba zai yiwu ba idan ɓarayi na mulki – Obasanjo

Shugabanci nagari ba zai yiwu ba idan ɓarayi na mulki – Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasan Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa gurɓatattun 'yan siyasa ba za su iya samar da shugabanci nagari ba, tsohon shugaban ya faɗi haka ne a wani taro na tunawa da Dennis Joseph Slattery a cibiyar Civic Centrer da ke Victoria Island Legas. Taron wanda ƙungiyar tsofaffin ɗalibai na St Finbarr ta shirya domin karrama tsohon ɗan ƙasar Ireland Dennis Joseph domin irin gudunmuwar da ya bayar lokacin da ya isa Illewe- Ekiti a Nijeriya shekerar 1941. A jawabinsa Obasanjo, ya kira gurɓatattun shugabanni a matsayin ɓarayi waɗanda ba za su iya samar da shugabanci nagari ba. Ya…
Read More

Ban zo shugabanci don kuɗi ba – Shugaba Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ba wai ya na shugabantar Nijeriya ba ne don neman wata riba ko tara dukiya. Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da tawagar tsoffin shugabannin Majalisar Ƙasa a lokacin da suka kai masa ziyara Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ya na mai cewa ya na kan karagar mulkin ne don yin aiki wa Nijeriya da ƴaƴanta. Ya ce, duk da ƙalubale da ƙasar ke fuskanta, gwamnatinsa na cigaba da ƙoƙari wajen ganin an samu kyawawan sakamako da kuma sauyi mai amfani a…
Read More
Ƙungiyar ƙwadago ta tada ƙayar baya bayan gwamnati ta tsayar da Yuli watan da za ta fara biyan sabon albashi

Ƙungiyar ƙwadago ta tada ƙayar baya bayan gwamnati ta tsayar da Yuli watan da za ta fara biyan sabon albashi

A ranar Juma’a ne kwamitin da ke kula da gyare-gyare a kan albashin ma’aikatan gwamnati ya gana a ranar dangane da sabon samfurin mafi ƙarancin albashi kuma sun amince cewa za a sanya ranar aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi a ranar 29 ga Yuli, 2024. Wannan dai na zuwa ne a wata takardar fahimtar juna da aka fitar a ƙarshen taron wanda wakilinmu ya gani a Abuja ranar Juma’a. Kwamitin ya kuma ba da shawarar cewa a biya tallafin ƙari ga ma'aikata na 35,000 wanda gwamnati ta dakatar har zuwa ranar 28 ga Yuli, 2024. Kwamitin ƙarƙashin jagorancin shugaban…
Read More

Madatsar Lagdo: Al’umma sun ƙaurace wa matsugunansu bayan ruwa ya haɗiye gonaki a Taraba

Daga BELLO A. BABAJI Mazauna birane da ƙauyuka da ke gefen kogin Benue a Jihar Taraba sun fara ƙaura da nome ababen da suka shuka bayan ruwa ya fara haɗiye gonaki sakamakon buɗe madatsar Lagdo da ke Jamhuriyar Kamaru. Bincike ya nuna cewa adadin ruwa da ke kogin Benue ya ƙaru da wani kaso wanda hakan ya sa gonakin da ke kusa suka dilmiye a ruwa. Wani matuƙin jirgin ruwa mai suna Jalo Ibbi, ya bayyana wa jaridar 'Daily Trust' cewa ruwa ya fara ƙaruwa ne sa'o'i 20 da suka gabata wanda hakan ya sabbaba al'umma suka shiga tsaka-mai-wuya ganin…
Read More

Kwamitin gidauniyar rabon tallafi ga mabuƙata na Bafarawa ya fara aiki a Sakkwato

Daga BELLO A. BABAJI An ƙaddamar da kwamitin da zai tattara bayanan buƙatun mutanen da gidauniyar Dakta Attahiru Bafarawa, tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, za ta taimaka wa da kayan tallafi a faɗin jihar. Shugaban Hukumar kula da Zakka da Waƙafi ta Sakkwato, Malam Muhammad Lawal Maidoki ke jagorantar kwamitin tare da wasu mambobin da aka zaɓo daga ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar da mambobin babban kwamitin. Tsohon Gwamnan na Sakkwato, wanda kuma shi ne garkuwar Sakkwato, ya bayyana dalilan da suka sa zai bayar da gudunmawar da ta kai Naira biliyan ɗaya don rage raɗaɗin talauci da jama'a da dama ke…
Read More
Ɗan Nijeriya ya zama na huɗu a duniya da ya warke daga cutar ƙanjamau

Ɗan Nijeriya ya zama na huɗu a duniya da ya warke daga cutar ƙanjamau

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani ɗan Nijeriya mai suna Salisu Ahmed ɗan shekaru 66, ya zama mutum na huɗu a duniya kuma mafi tsufa da aka samu ya warke daga cutar ƙanjamau na tsawon lokaci bayan wani dashen kwayar halitta da aka yi masa. Ya kasance yana tare da kwayar cutar sama da shekaru talatin. Rayuwar Salisu Ahmed ta ɗauki sabon salo a lokacin da aka gano cewa yana ɗauke da cutar ƙanjamau (HIɓ) shekaru 31 da suka gabata. A wata hira da ya yi da Doyin David, Ahmed ya bayyana cewa ciwon da ya samu ya samo asali ne…
Read More
Kwastom ta fara binciken jami’anta da zargin tatsar ’yan kasuwa a Kano

Kwastom ta fara binciken jami’anta da zargin tatsar ’yan kasuwa a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Kwastom ta Nijeriya, reshen Kano da Jigawa ta ce ta ƙaddamar da bincike kan wasu jami'anta da ake zargi da tilasta wa ‘yan kasuwa biyan maƙudan kuɗaɗe a kasuwar Abubakar Rimi da aka fi sani da Sabon Gari. Binciken ya biyo bayan ƙorafin da ‘yan kasuwar suka yi na zargin wasu jami’an hukumar na karɓar kuɗi. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na masu shagunan Sabon Gari, kuma ƙungiyar ‘yan kasuwa ta yanar gizo, Nazifi Auwalu, ya ce kasuwancin ya yi wa mutanensu wahala, domin kuwa yadda ake tatsar dukiyar jama’a ya sanya fargaba a…
Read More
Biliyan N250 Matawalle ya wawushe a Zamfara — Gwamna Lawal

Biliyan N250 Matawalle ya wawushe a Zamfara — Gwamna Lawal

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ce tsohon gwamna Bello Matawalle ko taro bai bari a asusun jihar ba, lokacin ya sauka daga mulki. Dauda Lawal ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels. Ya ƙara da cewa bayan da ya karɓi mulki, ya gano cewa an yi sama da faɗi da kusan Naira biliyan 250. Gwamna Dauda Lawal ya ce, “EFCC ta yi iƙirarin a ranar 21 ga Mayu, 2023 cewa tana zargin an sace Naira biliyan 70. Ma’ana kafin in hau mulki. “A lokacin da na karɓi mulki,…
Read More