21
Sep
Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa mutum ne mai tausayi da ƙoƙarin kawar da matsalolin da suka dami al'umma musamman yana sa ido da kula da kishin taimakawa bunƙasa lafiyar al'umma. Shugaban sashin kula da harhaɗa magunguna kuma jam'in hulɗa da jama'a na.Kano Medical Centre, Pharmacy Ammar Khalid Mustafa ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf da taimakon Kwamishinan lafiya suna ɗaukar matakai da suka kamata domin ganin sun kyautata lafiyar al'ummar Jihar Kano a fannoni da dama. Pharmacy Ammar Khalil Mustafa…
