Labarai

Bello Turji ya gudu amma bai tsira ba, sojoji sun kusa kashe la’ananne – Gwamnan Zamfara

Bello Turji ya gudu amma bai tsira ba, sojoji sun kusa kashe la’ananne – Gwamnan Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya bayyana kyakkyawan yaƙinin cewa ta’addancin da Bello Turji ke yi a faɗin Jihar Zamfara ya zo ƙarshe, yayin da ya ce a yanzu Turji ya gudu zuwa kan iyakar Zamfara da Sokoto, wajen yankin Shinkafi. Lawal ya bayyana haka a ranar Litinin, cikin wata tattaunawar da gidan talbijin na Channels tare da Seun Okinbswole. Gwamna Lawal ya bayyana hakan kwana uku bayan sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe gogarma Halilu Sububu, a Jihar Zamfara. Lawal ya ce wannan ƙoƙarin da sojoji suka yi, zai iya daƙile ayyukan…
Read More
Gwamnatin Borno ta gargaɗi jama’a su ƙaurace wa kayan lambun da ambaliya ta shafa don gudun Kwalara

Gwamnatin Borno ta gargaɗi jama’a su ƙaurace wa kayan lambun da ambaliya ta shafa don gudun Kwalara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata sanarwar da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Tsaron Jiha ta Jihar Barno ta fitar a ranar Talata, a shafin ta na Facebook, ta yi kakkausan gargaɗin cewa jama’a su guji sayen kayan miyar da gawarwakin jama’a da dabbobi da kuma dagwalon ruwan najasa suka sa wa cututtuka sanadiyyar garwaya da ambaliya. Sanarwar ta ƙara da cewa haka kuma sinadarai masu guba duk sun gauraya da kayan miyar, irin su alayyahu da sauran kayan lambu da ake amfani da su wajen miya. Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Tsaron Jiha ta ce, “sanadiyyar ibtila’in ambaliya, kayan miya…
Read More
Sojoji sun kashe ‘yan fashin daji tare da kuɓutar da mutane 20 a Kaduna

Sojoji sun kashe ‘yan fashin daji tare da kuɓutar da mutane 20 a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sojoji sun kashe 'yan fashin daji 4 tare da kuɓutar da mutanen da aka yi garkuwa da su guda 20 a wani farmaki na kwanaki biyu da suka kai a Birnin Gwari da ƙaramar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna. Samuel Aruwan, wanda ke riƙon muƙamin kwamishinan ma'aikatar tsaro ta cikin gida na jihar Kaduna, ya yi bayanin cewa sojojin na rundunar tsaftace daji sun yi aikin su a Alawa na ƙaramar hukumar Birnin Gwari. Rahotanni sun ce sojojin sun hangi giftawar 'yan fashin dajin a kusa da Kwaga, inda daga bisani suka hallaka biyu…
Read More
Tinubu ya saka hannu kan ƙudirin kafa cibiyar hana yaɗuwar ƙananan makamai ba bisa ƙa’ida ba – Ribaɗu

Tinubu ya saka hannu kan ƙudirin kafa cibiyar hana yaɗuwar ƙananan makamai ba bisa ƙa’ida ba – Ribaɗu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribaɗu ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan ƙudurin dokar kafa cibiyar kula da ƙananan makamai ta ƙasa. Ribadu ya bayyana haka ne a wajen taron ƙarawa juna sani kan hana yaɗuwar ƙananan makamai a Nijeriya da kuma yankin yammacin Afirka a ranar Talata a Abuja. Ya ce hakan zai ƙara wa cibiyar ƙwarin guiwa wajen gudanar da ayyukanta. A jawabinsa na buɗe taron, kodinetan hukumar NCCSALW na ƙasa DIG Johnson Kokumo mai ritaya, ya ce cibiyar a ‘yan kwanakin nan,…
Read More
Ambaliya: Fursunoni 281 sun tsere a Maiduguri — NCS

Ambaliya: Fursunoni 281 sun tsere a Maiduguri — NCS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar da ke Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Nijeriya (NCS), ta ce fursunoni 281 ne, suka tsere sakamakon ambaliyar ruwa da ta shafe wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Kakakin hukumar, Umar Abubakar, ya ce: “Wannan lamari mara daɗi ya haifar da ɓarna, inda ya rushe katangarar gidajen gyaran hali da suka haɗa da matsakaicin cibiyar tsaron hukumar ta Maiduguri (MSCC).” Ya bayyana cewa: “Bayan kwashe fursunonin da jami’an hukumar tare da tallafi daga jami’an tsaro zuwa wani waje mai tsaro, sai aka gano fursunoni 281 sun ɓace.” Ya ƙara da…
Read More
Tinubu ya fi ƙarfin satar dukiyar Nijeriya — Minista

Tinubu ya fi ƙarfin satar dukiyar Nijeriya — Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Karamin Ministan Harkokin Matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fi ƙarfin ya saci dukiyar Nijeriya. Da yake jawabi a wajen taron ƙungiyar Haɗin Kan Ma’aikata (JUNC), a Ma’aikatar Harkokin Ci Gaban Matasa a Abuja, Olawande, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya su ƙara haƙuri da halin da ake ciki a ƙasar nan. Ya yi alƙawarin cewa nan ba da daɗewa ba za a ga sauye-sauyen da suka dace. Ya bayyana cewa Tinubu mutum ne mai arziƙi, kuma ba shi da sha’awar satar dukiyar ƙasar nan. “Tinubu ba talaka…
Read More
OPEC ta bayyana haƙiƙanin dalilin hauhawar farashin fetur a Nijeriya

OPEC ta bayyana haƙiƙanin dalilin hauhawar farashin fetur a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD ƙungiyar ƙasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC) ta ce, ƙarin farashin man fetur a Nijeriya ya haifar da fargaba, inda da yawa ke nuna yatsa tsakanin masu samar da man, musamman ma matatar man Dangote da Kamfanin NNPC. Sai dai babban Sakataren OPEC, Haitham Al Ghais, ya bayyana cewa, ainihin dalilan da ke haddasa hauhawar farashin man fetur, sun ta'allaƙa ne a abubuwa da dama, musamman a irin harajin da gwamnatoci ke sanyawa, ciki har da na manyan ƙasashe masu man fetur. A wani rubutu da aka wallafa a ranar Talata, Al Ghais ya bayyana cewa…
Read More
Donald Trump ya ƙaddamar da sabon dandalin Kirifto

Donald Trump ya ƙaddamar da sabon dandalin Kirifto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump tare da ‘ya’yansa da ‘yan kasuwa sun ƙaddamar da wani tsarin hada-hadar kuɗi. An ƙaddamar da dandalin mai suna 'World Liberty Financial' a ƙarshen ranar Litinin, Satumba 16, 2024, yayin gabatarwar kan layi na sa'o'i biyu. An ce, dandalin World Liberty Financial zai yi aikine bisa tsarin abin hada-hadar kuɗi, tsarin da ke shiga tsakani kamar banki don gudanar da mu'amala cikin tsari, inji tattaunawar da masu dandalin. ƙididdigar kuɗi, ko DeFi, ta dogara ne akan abin da ake kira fasaha na 'blockchain', wanda ke kiyaye bayanan ma'amaloli a bayyane.…
Read More

Ɗan Nijeriya ya kafa tarihi a wasan Monaco da Barcelona a gasar UEFA

Daga BELLO A. BABAJI Ɗan wasan Monaco, George Ilenikhena ya kafa sabon tarihi a gasar zakarun Nahiyar Turai bayan taimaka wa kungiyarsa doke Barcelona a wasan farko na gasar. An sako ɗan wasan ne a minti na 59 inda ya zura ƙwallo a minti na 71 wanda ya bai wa Monaco nasara da ci 2 da 1. Hakan ya nuna ɗan wasan mai shekaru 18 shi ne mutum na biyu mai mafi ƙarancin shekaru da ya zura ƙwallo a gasar wa ƙungiyar. Da farko dai, Barcelona ta mamaye wasan inda daga bisani Alƙalin wasa ya bai wa ɗanta, Eric Garcia…
Read More

2027: Ku fara tattara kayanku – Kashedin PDP ga APC a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sabon shugaban jam'iyyar PDP, Hon. Nura Amadi Kurfi ya gargaɗi jam'iyyar APC mai mulki a Jihar Katsina da ta fara tattara komatsanta daga gidan gwamanti kafin ranar zaɓen 2027. Hon. Kurfi ya yi wannan hannunka mai sanda ne jim-kaɗan bayan amsar rantsuwar kama aiki a matsayin sabon zaɓaɓɓen shugaban PDP ɓangaren Sanata Yakubu Lado Ɗan-Marke. An rantsar da shugaban PDP na Katsina, Muhammad Nura Amadi Kurfi tare da sauran waɗanda za su shugabanci jam'iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa A lokacin da ya ke magana Hon. Kurfi ya yaba wa shugabancin jam'iyyar a matakin…
Read More