Labarai

Mutum 13 sun mutu yayin da 108 ke karɓar kulawa sakamakon ɓarkewar Kwalara a Jigawa

Mutum 13 sun mutu yayin da 108 ke karɓar kulawa sakamakon ɓarkewar Kwalara a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Kimanin mutane 13 ne suka mutu a cikin wata guda sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa da aka fi sani da Kwalara a ƙaramar hukumar Auyo da ke Jihar Jigawa. Jami’in kiwon lafiya a matakin farko Na ƙaramar hukumar, Malam Abdullahi Musa Auyo ya tabbatar da faruwar lamarin. Musa Auyo ya shaida wa wakilinmu haka a lokacin da hukumomin RUWASA da na bada agajin gaggawa ta UNICEF suka ziyarci ƙaramar hukumar don bada kayan agaji ga marasa lafiyar tare da ɗaukar matakan kariya don hana cigaba da yaɗuwar cutar a yankin. Ya ce, an…
Read More
Gaggan ‘yan bindiga sun taru a Zamfara domin zaɓen sabon shugaba bayan kashe Halilu Sububu

Gaggan ‘yan bindiga sun taru a Zamfara domin zaɓen sabon shugaba bayan kashe Halilu Sububu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Talata ne ‘yan bindiga suka taru a gidan Marigayi Kachalla Halilu Sububu da ke Tungar Daji, Bagega, cikin ƙaramar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara, domin zaɓen sabbin shugabanni. Idan dai ba a manta ba jami’an tsaro sun yi nasarar kashe Kachalla Halilu da wasu ‘yan ƙungiyar sa kwanan nan. Wani mai sharhi kan harkokin tsaro a Sakkwato, Bashiru Altine Guyawa, ya kuma bayyana cewa 'yan ta'addan za su fara da addu'ar kwana uku ga Marigayi Kachalla Halilu Sububu, sannan a zaɓi sabon shugaba da zai maye gurbinsa. A yanzu haka suna baje…
Read More
An ƙaddamar da takin 4Tree a Kano  

An ƙaddamar da takin 4Tree a Kano  

Dag MUHAMMADU MUJITABA a Kano    A karon farko an ƙaddamar da wani sabon taki na gargajiya da ke cikin leda a zamanance wanda ba shi da illa ga muhalli, ƙasa, da lafiyar al'umma bayan an yi amfani da takin a gonaki a noman damina ko noman rani kamar dai yadda MD Eseni Ibiam Orji, shugaban kamfanin Natari Group da ya samar da takin ta hanyar bincike da haɗin gwiwar ƙasar Thailand a Nijeriya da ya bayyana a wajen ƙaddamar da takin a Kano. Babban jami'in kula harkokin kasuwancin takin shiyyar Arewa maso Yamma, Alhaji Suleiman Saminu, ya ce an…
Read More
Cikin kwana 10 za a rufe sansanonin ’yan gudun hijirar Maiduguri

Cikin kwana 10 za a rufe sansanonin ’yan gudun hijirar Maiduguri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Borno ta ce za ta rufe duk sansanonin bayar da agaji 32 da aka kafa don tallafa wa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri cikin makonni biyu, daga ranar Litinin da ta gabata. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Farfesa Usman Tar, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da manema labarai a Maiduguri ranar Laraba. Ya ce ibtila’in ambaliyan ya raba kusan iyalai 30,000, da jimilla kusan mutane 600,000 da gidajensu a faɗin birnin. “Gwamnatin jihar ta yanke shawarar cewa sansanonin ’yan gudun hijira ba za su ci gaba da aiki sama…
Read More
Edo 2024: Bishop Kukah ya kare PDP bisa ƙin saka hannu a yarjejeniyar zaman lafiya

Edo 2024: Bishop Kukah ya kare PDP bisa ƙin saka hannu a yarjejeniyar zaman lafiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban limamin cocin Katolika na Sakkwato, Bishop Matthew Kukah, ya ce, babu wanda zai iya tilasta wa jam'iyyar PDP reshen jihar Edo sanya hannu kan duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da za a yi a zaɓen gwamna da za a gudanar a ranar 21 ga watan Satumba, inda ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bai sanya hannu ba lokacin da ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023. An rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya na kwamitin zaman lafiya na ƙasa ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Nijeriya, Janar Abdulsalam Abubakar don gujewa tashe-tashen…
Read More
An damfari bankunan Nijeriya biliyan N42.6 a wata uku – Rahoto

An damfari bankunan Nijeriya biliyan N42.6 a wata uku – Rahoto

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Bankunan kasuwancin Nijeriya sun yi asarar Naira Biliyan 42.6 ta hanyar ’yan damfara da sauran ayyukan zamba tsakanin Afrilu da Yuni 2024, a cewar wani rahoto na baya-bayan nan. An yi asarar wannan adadi ne a kashi na biyu na shekarar 2024 kaɗai, ya zarce yawan asarar da aka yi daga zamba a duk shekarar 2023, inda bankuna suka yi asarar Naira biliyan 9.4. Rahoton ya samo asali ne kan zamba da shari’o’in jabu da cibiyoyin kuɗi 28 da ke ƙasar suka bayar. FITC ta bayyana cewa an samu rahotanni 80 na zamba a cikin wannan…
Read More
Bafarawa ya bada gudunmawar Naira biliyan ɗaya don cike giɓin da aka samu a mulkinsa

Bafarawa ya bada gudunmawar Naira biliyan ɗaya don cike giɓin da aka samu a mulkinsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A wannan Larabar ce tsohon Gwamnan Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayar da gudummawar Naira biliyan 1 a matsayin tallafi ga al’ummar jihar. Ya bayyana cewa hakan ya samo asali ne daga burinsa na ganin ya cike duk wani giɓi da ya haifar a lokacin da yake kan riƙe akalar jagorancin jihar. Bafarawa wanda ya mulki Jihar Sakkwato na tsawon wa’adi biyu a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, ya ce “a shekaru 70 na haihuwata, ina jin daɗin kyautatawa mutane. “Burina a yanzu shi ne in tabbatar da cewa na cike duk wani giɓi…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta shirya kwamitin cikar Nijeriya shekaru 64 na ƴancin kai

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta shirya kwamitin ministoci game da ranar ƴancin kai ta 2024. Kwamitin zai kula ne da shiryawa da tabbatar da zartar da baki ɗaya ayyukan da za a yi na karrama ranar. Nijeriya, wacce Turai ta bai wa ƴancin-kai a shekarar 1960, za ta cika shekaru 64 da samun hakan a ranar 1 ga watan Oktoba, 2024. Cikin wata takarda da Daraktan Labarai na ofishin shugaban ma'aikatan Fadar shugaban ƙasar, Segun Imohiosen ya fitar, ta ce shugaban ma'aikatan Fadar (SGF), Sanata Akume shi zai jagoranci kwamitin inda ya ce bikin ƴancin-kan za a gudanar…
Read More

Tsage gaskiya: Shin Yahaya Bello ya je ofishin EFCC kuma ya gana da jami’anta?

Daga BELLO A BABAJI An samu ruɗani game da batun zuwan tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello hedikwatar EFCC kan bincike da ake shirin gudanarwa akan sa game da badaƙalar wasu biliyoyin kuɗaɗe. Yayin da ofishin labarai na tsohon gwamnan ya ce mai gidansa ya amsa gayyatar da hukumar ta yi masa, sai kuma hukumar da ta fitar da sanarwar cewa har yanzu shi ɗin mutum ne da ake nema ruwa a jallo. Ohiare Michael, wanda shi ne Daraktan Ofishin, ya ce, Yahaya Bello ya amsa gayyatar ne bayan tattaunawa da masana harkar shari'a da abokanan siyasarsa wanda an nuna…
Read More

Ministan Labarai ya kirayi ƴan Nijeriya su yi amfani da damar shirye-shiryen farfaɗo da tattali na Shugaba Tinubu

Daga BELLO A BABAJI Ministan Labarai, Mohammed Idris ya shawarci ƴan Nijeriya su yi amfani da dama ta shirye-shirye da gwamnatin tarayya ke yi ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa. Ministan ya faɗi hakan ne a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Laraba a taron wayar da kan al'umma game da shirye-shirye da gwamnati ta samar don inganta al'umma. Jami'in hulɗa da jama'a na Ma'aikatar Labarai, Stanley Ugoeze wanda shi ya wakilci ministan a taron ya ce taron musamman an yi shi ne don wayar da kan ƴan ƙasa kan damanmaki da ke cikin…
Read More