Labarai

Jagororin Tsaron Nijeriya sun je Borno jajen ambaliya

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya ziyarci Maiduguri inda ya jajenta wa gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum da Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Garbai bisa ambaliyar da aka yi a birnin wadda ta ɗaiɗaita dubunnan mutane. Wata takarda da Daraktan Labarai na CDS, Burgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ta ce Babban Hafsan Tsaron ya taya gwamnatin jihar da al'ummarta jimamin aukuwar ambaliyar, ya na mai cewa abu ne da ba a yi tsammanin sa ba wanda ke da wahalar dakatarwa. Ya kuma yi fatan kar irin hakan ya sake faruwa tare…
Read More
Ƙuncin rayuwa da ake fuskanta a Nijeriya ya wuce gona da iri — Abdulsalami

Ƙuncin rayuwa da ake fuskanta a Nijeriya ya wuce gona da iri — Abdulsalami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Mulkin Soji a Nijeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya bayyana damuwa kan matsi da ƙuncin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar da a cewarsa ya wuce gona da iri. Dangane da hakan ne Janar Abdulsalami ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakan kawo ƙarshen wannan raɗaɗi da ake fuskanta a faɗin ƙasar. Tsohon Shugaban ƙasar ya ce matakin da gwamnatin take ɗauka na rarraba wa ’yan ƙasa kayayyakin tallafin rage raɗaɗi ba zai magance komai ba la’akari da ƙolokuwar da tsadar rayuwa ta kai a ƙasar. Janar Abdulsalami ya ce akwai…
Read More
Aikin CRC: Burina Fagge ta zama akan gaba – Hon. Habu Fagge

Aikin CRC: Burina Fagge ta zama akan gaba – Hon. Habu Fagge

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano  Shugaban Hukumar CRC mai kyautata ɗa'a, ilimi da tarbiyyar al'umma da aka fi sani da CRC  Community Re-orrientation Council wacce manyan ayyukanta akwai aikin bunƙasa ilimi ta hanyar gyaran makaratun firamare na jihar Kano, wanda kowacce ƙaramar hukuma za ta samu gyaran makaratun aƙalla biyar da CRC za ta yi kafin shigowar sabuwar shekarar 2025 in Ubangi ya amince, kamar dai yadda hukumar CRC a matakin jihar Kano ta tabbatar a wannan lokaci.                          Hon. Alhaji Habu Muhammad Fagge, shi ne shugaban CRC na ƙaramar hukumar Fagge a Kano, ya faɗa a hira da manema labarai…
Read More
Sarkin Katsina zai naɗa Farouƙ Lawal a matsayin Sarkin Fulanin Joɓe

Sarkin Katsina zai naɗa Farouƙ Lawal a matsayin Sarkin Fulanin Joɓe

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai martaba Sarkin Katsina Abdulmummuni Kabir Usman zai naɗa mataimakin gwamnan jihar Katsina Lawal Farouk Joɓe a matsayin Sarkin Fulanin Joɓe. Haka kuma shi ma shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Katsina Alhaji Jabiru Tsauri za a naɗa shi a matsayin Lamiɗon Katsina. Har-wa-yau duk rana guda Sarkin zai naɗa shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar wakilai mai wakiltar Musawa da Matazu Alhaji Abdullahi Aliyu a matsayin Dujuman Katsina. Tuni dai Gwamna Dikko Raɗɗa ya ɗauki nauyin gayyatar jama'a wajen naɗin sarautun da ya bayyana a matsayin abin tarihi a gare shi. Da yake hira da…
Read More
Kotu ta bada belin hadimin Tambuwal da ya soki gwamnan Sakkwato 

Kotu ta bada belin hadimin Tambuwal da ya soki gwamnan Sakkwato 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata Kotun Majistiri da ke jihar Sakkwato a ranar Laraba ta bada belin Shafi'u Umar, hadimin tsohon Gwamnan jihar, Aminu Tambuwal, kan Naira miliyan ɗaya. Shafi'u Umar mai shekaru 37, ana zarginsa da yaɗa ƙarya kan Gwamna Ahmad Aliyu da matarsa a shafin sada zumunta na zamani. Haka kuma ana tuhumar sa da ɓata suna. A ranar 26 ga watan Agusta ne aka fara shari'ar, inda ɗan sanda dake gabatar da ƙara, Sufeto Abdulrahman Mansur, ya ce laifin ya saɓa da dokar Panel Code. A cewar takardar rahoton farko, wanda ake ƙarar ya aikata…
Read More
Tinubu na shirin yi wa ministoci garanbawul

Tinubu na shirin yi wa ministoci garanbawul

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alamu masu ƙarfi na nuni da cewa, Shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin aiwatar da wani babban garanbawul a gwamnatinsa ta hanyar yin manyan sauye-sauye ga ministocinsa, inda har ake kyautata tsammanin zai iya rushe Ma'aikatar Harkokin Jinƙai da Agaji. Wannan dai na ɗaya daga cikin abubuwan da ake tsammanin shugaban ƙasar zai yi idan ya tashi garambawul a Majalisar Zartaswa ta gwamnatinsa ne. Har ila yau, garambawul ɗin zai dunƙule wasu ma'aikatu da hukumomi wuri guda, yayin da wasu ministoci za a sauke su daga muƙamansu, kamar yadda wata majiya daga Fadar Shugaban ƙasa…
Read More
PDP ta zargi gwamnatin Kebbi da yawon sharholiya 

PDP ta zargi gwamnatin Kebbi da yawon sharholiya 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Jam'iyyar PDP ta adawa a jihar Kebbi ta nuna rashin gamsuwa bisa ga yawace-yawacen da ta ce Gwamna Malam Nasir Idris ƙauran Gwandu yana yi ba tare da dawowa da wani sakamako mai amfanin al'umma ba. Wannan yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun Sakataren Jam'iyyar Honarabul Abubakar Bawa Kalgo da aka raba wa manema labarai ranar Lahadi 15 ga wannan watan na Satumba 2024. Takardar ta ayyana cewa tun bayan da aka rantsar da Malam Nasir Idris a matsayin gwamna a jihar sama da shekara ɗaya kenan ya rinƙa…
Read More
Za a daina tuhumar masu yunƙurin kashe kai a Nijeriya

Za a daina tuhumar masu yunƙurin kashe kai a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammed Pate, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin daƙile yunƙurin masu ɗabi'ar kashe kansu a ƙasar. Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja a wani taron manema labarai domin tunawa da ranar rigakafin kashe kai ta duniya ta shekarar 2024. An ware ranar 10 ga Satumba kowace shekara, bikin yana da "Canza Labari akan kashe kai" a matsayin jigon 2024. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, ana aikata laifin kashe kansa a ƙasar, sai dai an yi ta kiraye-kirayen masu ruwa da…
Read More
Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 da za a gudanar bana a birnin New York na Amurka. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Fadar Shugaban Nijeriya ta fitar a ranar Alhamis. Sanarwar da mataimaki na musamman ga Shugaban Nijeriya a kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ya fitar ta ce Shugaba Bola Tinubu ba zai samu damar halatar taron ba. Shugaba Bola Tinubu yana so ya zauna a gida domin ya maida hankali a kan wasu batutuwa na cikin gida da magance…
Read More

Ambaliya: Gwamnan Zamfara ya jajenta wa Borno da bada tallafin N100m

Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya jajenta wa gwamnatin Jihar Borno da mutanenta biyo bayan ambaliyar ruwan sama da aka yi a Maiduguri, babban birnin Borno. Gwamna Lawal, wanda Sakataren gwamnatinsa, Malam Abubakar Nakwada ya wakiltce shi, ya jagoranci tawagar gwamnatin Zamfara zuwa gaisuwar jajen a ranar Alhamis. Kakakin gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya ce dalilin ziyarar shi ne don a jajenta wa gwamnatin Borno da mutanen jihar kan ambaliyar wacce ta auku a makon da ya gabata, kamar yadda ya faɗa a cikin wani saƙo da ya fitar. A lokacin da ya ke…
Read More