Labarai

Gwamnatin Katsina ta fara ɗaukar matakan kariya daga ambaliya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin jihar Katsina ta fara shiri domin kauce wa samun ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomi bakwai da ke jihar . Hakan ya biyo bayan hasashen da Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, NIMET ta yi game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohi. Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Garba Faskari ya faɗi haka a yayin da ya ke ganawa da masu-ruwa-da-tsaki akan kula da sauyin yanayi a Katsina. Ya ce, taron zai nemo hanyar da za a ankarar da waɗannan ƙanana hukumomi da aka yi hasashe akai. Ƙananan hukumomin kuwa sun haɗa da; Katsina, Kaita,…
Read More

An gudanar da musabaƙar Al-Ƙur’ani a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An kammala Musabaƙar karatun Ƙur'ani a masallacin Bani comassie da ke cikin garin Katsina, ƙarƙashin shugabancin limamin masallacin, Sheikh Sama Adamu Bakori. Shugaban kwamitin shirya Musabaƙar ya ce, yara 20 da suka fito a makarantun Islamiyya da na karatun Allo da na boko ne suka shiga gasar. Ya ce, ɗalibai goma ne suka samu nasarar lashe gasar karatun Al-Ƙur'anin. Ya kuma yi godiya ga shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar kuma lamiɗon Katsina, Alhaji Jabiru Salisu tsauri wanda ya ɗauki nauyin Musabaƙar. Sheikh Sama Bakori ya bayyana lamiɗon a matsayin mutumin kirki da ke ƙoƙarin taimaka…
Read More
Gwamnatin Katsina ta tallafa wa iyalan ‘yan sanda da suka mutu da Naira Miliyan 3.5

Gwamnatin Katsina ta tallafa wa iyalan ‘yan sanda da suka mutu da Naira Miliyan 3.5

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnatin Katsina ta tallafawa iyalan 'yan sandan da suka rasa rayukansu wajan yaƙi da 'yan ta'adda a jihar. Da yake miƙa kuɗaɗen ga iyalan mamatan, muƙaddashi kwamishinan 'yan sanda a jihar DCP Aminu Usman Gusau ya jajantawa iyalan 'yan sandan da bayyana su a matsayin jajirtattu. Ya ce sun sadaukar da rayukan su wajan bautawa ƙasa a sa'ilin da suke fagen fama . Muƙaddashin kwamishinan ya ƙara da cewa wannan tallafin kuɗin ba zai biya irin sadaukar da kai da suka yi ba wajen kare lafiyar al'ummar jihar Katsina. Sai ya yaba gwamnatin malam Dikko…
Read More

Gwamnatin Kano ta rusa kantomomin ƙananan hukumomin jihar

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rushe kantomomin riƙon ƙwarya na gudanarwar ƙananan hukumomin jihar 44. Hukuncin ya fara aiki ne nan-da-nan wanda aka sanar a zama na tantancewa da mambobin kwamitocin a Fadar gwamnatin jihar. Wata takarda da Kakakin gwamnan, Sanusi Tofa ya fitar, ta ce hakan na nufin kawo ƙarshen watanni shida na kantomomin waɗanda a lokacinsu suka yi aiki da gwamnatin jihar musamman wajen zartar da tsare-tsarenta na tushe da kuma shirye-shirye. Gwamna Abba ya yaba wa mambobin kwamitocin kan saduakarwarsu da ƙoƙari da suka yi wa harkokin ƙananan hukumomin, ya na…
Read More

Shettima zai wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba zai samu halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79 ba na wannan shekarar wanda za a yi a New York, yayin da ya umarci Mataimakinsa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Nijeriya a yayin tafiyar. Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya faɗi hakan cikin wata takarda da fitar inda ya ce kasancewar a makon da ya gabata, Tinubu ya dawo daga ƙasar Chana, ya sa ba zai samu zuwa taron ba, madadin haka, zai mayar da hankali kan al'amura na cikin gida da suka damu…
Read More

Gwamnatin Tarayya za ta garƙame masu zaman kansu da ke biyan ƙasa da sabon mafi ƙarancin albashi

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gargaɗi kamfanoni masu zaman kansu kan ƙin bin dokar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ga ma'aika wanda yin hakan laifi ne na sata. Sakataren Ma'aikatar Ƙwadago da Ɗaukar aiki, Alhaji Ismail Abubakar ya faɗi hakan a taron ƙungiyar masu ɗaukar aiki na hukumomi masu zaman kansu a Legas karo na 13. Alhaji Abubakar, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, ya ce duk kamfanin da bai biyan ma'aikatansa mafi ƙaranci N70,000, to za a garƙame shi a kurkuku. Daraktan ɗaukar aiki da biyan albashi na ma'aikatar, John…
Read More

Raɗɗa ya bai wa Borno miliyan N100 a matsayin tallafin ambaliya

Daga UMAR GARBA a Katsina A jiya Laraba, gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya kai ziyara jihar Borno don jajenta wa waɗanda iftila'in ambaliyar ruwa ya shafa. A yayin ziyararsa, ya bai wa jihar Naira miliyan 100 don tallafa wa mutanen da ambaliyar ta rutsa da su. Ya bayyana ambaliyar a matsayin wata jarabawa daga Allah (SWT) inda ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu yayin ambaliyar. "Ambaliyar na ɗaya daga cikin ambaliyar ruwa mafi muni da ta taɓa faruwa a ƙasarmu, musamman a nan Borno. Mu na fatan Allah Ya kawo ɗauki tare da fatan…
Read More
Ambaliyar ruwa da ambaliyar wuta!

Ambaliyar ruwa da ambaliyar wuta!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A wannan makon ina son haɗa ambaliyar ruwa da ta shafi sassan Nijeriya musamman Maiduguri a Jihar Borno da kuma ambaliyar wuta da Isra’ila ke cigaba da yi a Zirin Gaza. Gaskiya hotunan da ke yawo a kafafen yanar gizo da su ka haɗa har da faya-fayan bidiyo na da ban tsoro na yadda ruwa ya malale birnin Maiduguri kai kace sassan tafkin Chadi ne. Hoton da ya fi ɗaukar hankali na shi ne na wani matashi da ya goyo mahaifin sa a baya duk da ba majanyi don kai shi tudun mun tsira daga cikin…
Read More
Kashi 90 na masu safarar yara a Kano Hisba ke kamawa, ba NAPTIP ba – Malam Sufi

Kashi 90 na masu safarar yara a Kano Hisba ke kamawa, ba NAPTIP ba – Malam Sufi

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta bayyana cewa kashi 90 na safarar yara da hukumar NAPTIP take yin nasara a kotu hukumar Hisba ce ta ke kamawa. Darakta janar na hukumar ta jihar Kano, Malam Abba Sa'idu Sufi, da ya wakilci babban kwamandan Sheik Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka a yayin wata ziyara da Rundunar Ƴan kishin Kano RKK ta kai masa a hedkwatar hukumar ta jihar a ranar Talata da ta gabata. A ɓangaren zamantakewar aure kuwa Mal. Sufi yace kashi 70 cikin ɗari na ayyukan hukumar ya ta'allaƙa ne ga harkar…
Read More

EFCC ta kai samame masauƙin Gwamnan Kogi na Abuja don kama Yahaya Bello

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an hukumar EFCC sun kai samame gidan gwamnatin jihar Kogi da ke Abuja don kama tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello. Cikin wata sanarwa da Daraktan Ofishin Labaran tsohon gwamnan, Ohiare Michael ya fitar, ya ce jami'an sun je gidan ne don kamo mai gidan nasa wanda ya zarge su da yin harbe-harbe a lokacin kai samamen. Haka na zuwa ne jim-kaɗan bayan Ohiare ya fitar da sanarwar cewa Yahaya Bello ya amsa gayyatar da hukumar ta yi masa inda bayan zuwan sa ofishin ne sai jami'an na EFCC suka ce masa ya tafi amma ya dawo…
Read More