19
Sep
Hukumar NGSA ta ce mutane kar su samu fargaba game da alamar girgizar ƙasa da aka yi a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda ta shawarci mazauna garin kada su tashi hankalun su. Sanarwa daga darakta-janar, Farfesa Olusegun Ige, ya bayyana cewa NGSA ta bibiyi girgizar ƙasan kuma ta gano cewa ba zai haifar da wata barazana ga muhalli ba. "Binciken farko na siffofin ya nuna cewa tushen motsin ƙasan yana da nisan ƙasa da 5 km daga sashin bincike. "Kungiyar NGSA ta kuma ziyarci yankunan da abin ya shafa domin tantance abubuwan da suka faru. "Har ila yau, ƙarfin girgizar…
