18
Sep
Daga BELLO A. BABAJI Ministan Labarai da Wayar da kan ƴan Ƙasa, Alhaji Idris Mohammed ya yi kira ga Ƙungiyar Jaridu ta Chana (CMG) su haɗe hannu da gwamnatin tarayya don magance barazanar labarai masu rikitarwa da ke addabar kafafen sadarwa na ƙasashen biyu. Ministan ya bayyana haka ne a Abuja, a yayin taron bikin cikar Jamhuriyar Chana shekaru 75 da CMG ta shirya. Idris, wanda Daraktan Labarai na Ma'aikatar, Suleiman Haruna ya wakilce shi, ya ce ci gaban da CMG ta samar wata hanya ce ta ƙarfafa alaƙa musamman kan ababen da suka haɗu a kai. Ya ce, a…
