Labarai

Jerin sunayen ‘yan bindiga 13 da sojojin Nijeriya su ka kashe

Jerin sunayen ‘yan bindiga 13 da sojojin Nijeriya su ka kashe

Arewacin Nijeriya, musamman Arewa maso Yamma na shan fama da tashe-tashen hankula da ya shafi 'yan bindiga. Rikicin wannan yankin ya samo asali ne tun shekarar 2011, bayan da wani rikici ya ɓarke tsakanin manoma Hausawa da Fulani makiyaya. Sai dai wannan rikici ya rikiɗe ya zama babban barazana ga tsaro ga jihohin yankunan kamar sh Katsina, Kaduna da Zamfara. A baya bayan nan ne rundunar sojin Nijeriya ta kashe wani fitaccen ɗan bindiga da ake kira Kachalla Halilu Sububu a wani farmaki da su ka kai masa. Sububu babban ɗan bindiga ne da ya shahara wajen ayyukan ta'addanci a…
Read More

Tinubu ya jajenta wa mutanen da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya jajenta wa gwamnatin Zamfara kan ambaliyar wasu sassan jihar da kuma mutanen da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 40 a ƙaramar hukumar Gummi. Ya bayyana alhininsa kan musibun da suka samu mutanen yankin da ma jihar baki ɗaya tare da yin alƙawarin tallafa wa mutanen da lamarin ya shafa. Shugaba Tinubu, ya kuma umarci hukumomin bada agaji su yi nazari game da dalilan faruwar abubuwan biyu don gano haƙiƙanin matsalolin da suka haddasa hakan. Ya kuma umarce su da su yi aiki da gwamnatin…
Read More

Har yanzu ɗan uwa ga Wike shi ne kwamishinan zaɓen Edo – INEC

Daga BELLO A BABAJI Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta yi watsi da kiran da jami'yyar PDP ta yi mata na a sauya kwamishinan zaɓe na Edo, Anugbum Onuoha yayin da ake ƙara kusantar zaɓen jihar da za a yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024. A baya ne jam'iyyar PDP ta buƙaci a sauya Onuoha daga muƙamin kwamishinan zaɓen kasancewar ya na da alaƙa ta jini da Ministan Abuja, Nyesom Wike wanda su ke hasashen zai iya amfani da shi wajen cimma wata manufa. Cikin wata takarda da shugaban jam'iyyar na jihar, Anthony Aziegbemhin ya aika wa shugaban…
Read More

Tinubu ya je Maiduguri jajen ambaliya

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya je garin Maiduguri, babban birnin Borno don jajenta wa gwamnatin jihar da mutanenta kan ambaliyar da ta auku a makon da ya gabata. A ranar Lahadi ne Shugaba Tinubu ya dawo Nijeriya daga Landan wanda zai duba matakin ɓarnar da ambaliyar ta yi a gidaje, asibitoci, kasuwanni, makarantu da sauran kadarorin al'umma. Bayan isarsa babban filin jiragen sama na Maiduguri ne, gwamnan jihar, Babagana Zulum da wasu manyan jami'an gwamnati suka tarbi shugaban ƙasar. Hukumar bada Agaji ta Gaggawa ta ce, ambaliyar ta shafi kusan rabin birnin bayan mamakon ruwan sama…
Read More

Dakatar da ni da PDP ta yi wasan yara ne – Sanata Tsauri

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Tsohon Sanata, Umar Ibrahim Tsauri ya bayyana dakatar da aka yi masa daga jam'iyyar PDP a matsayin kodai wasan yara ko kuma anyi ne da gangan don a tozarta shi. Yayin da yake mayar da martani game da batun dakatar da shi da jam'iyyar ta yi a matakin gundumar Tsauri wadda nan ne mazaɓarsa, ya ce kawo yanzu bai samu takardar dakatarwar ba, ya na mai cewa ya yi magana ne don yawan kiransa ta waya da akai tayi daga ko'ina a faɗin ƙasar nan. Ya ce a matsayinsa na wanda ya yi Sanata ya…
Read More

Yadda farashin fetur zai kasance a NNPCL bayan ɗibar farko daga matatar Ɗangote

Daga BELLO A BABAJI Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ce zai sayar da kowacce litar fetur a Arewacin Nijeriya a farashin sama da N1,000 bayan yin jidon farko daga matatar Ɗangote. Kakakin NNPCL, Olufemi Soneye ya faɗi hakan a ranar Litinin cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya yi bayanin yadda farashin zai kasance la'akari da jihar da ake sayar da shi. A Jihar Borno, za ake sayarwa ne akan N1,019 yayin da a jihohin Abuja, Sakkwato, Kano da makusantansu, za a ke sayarwa a N999.22. A Oyo da Ribas da sauran jihohin Kudu kuma, za ake…
Read More

Za mu yi adalci kan batun sojan da aka ce an zalunta – DHQ

Daga BELLO A. BABAJI Hedikwatar Tsaro, DHQ ta ce ta samu labarin wani faifan bidiyo da ke yawo inda a ciki ake zargin an tsare wani jami'in sojan ruwa mai suna Abbas Haruna na tsawon shekaru shida ba bisa adalci ba. Cikin wata takarda da Daraktan Labarai na rundunar, Burgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, DHQ ta tabbatar wa al'umma cewa jami'an tsaron Nijeriya za su cigaba da aiki da adalci da bin dokar ƙasa. Ya ce, kotun rundunar ta kan tabbatar da yin adalci da bada dama ga waɗanda aka zalunta gami da yi mu su adalci a yadda…
Read More

Trump ya sake tsallake harin harbin bindiga a wani karo

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon shugaban Amurka kuma ɗan takarar shugaban ƙasar, Donald Trump ya sake tsallake wani harin bindiga inda aka yi ta harbe-harbe a kusa da shi a wani yanki na Jihar Florida, a ranar Lahadi. Kakakinsa, Steven Cheung, ya ce Trump ya na cikin ƙoshin lafiya inda ya ce su na aiki da hukumomi wajen gano ainihin bayanan al'amarin. Kawo yanzu babu tabbatcin harin an kai shi ne musamman don Trump kamar yadda kakakin nasa ya wallafa a shafin X. Hakan na zuwa ne watanni biyu bayan wani harin kisa da aka kai wa tsohon shugaban a…
Read More

Ambaliyar Borno: NCS ta fitar da jaddawalin waɗanda suka tsere daga gidan yari

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Gyaran Hali ta Ƙasa (NCS) ta ce aƙalla fursunoni 281 ne daga gidan yarin da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno suka tsere. Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ambaliyar ruwan sama da ta auku a birnin inda ta ɗaiɗaita wani kaso mai tsoka na yankin yayin da fursunoni bakwai suka koma kurkukun. A ranar Lahadi, Kakakin hukumar, Umar Abubakar ya fitar da jaddawalin bayanan fursunonin da suka arce. Ya ce, sun tabbatar da rugujewar wani sashi na ginin kurkukun Maiduguri wanda hakan ne ya sabbaba arcewar wasu daga cikin fursunonin. Ya bayyana cewa,…
Read More

Kwalara ta kashe mutum huɗu a Adamawa

Daga BELLO A BABAJI Aƙalla mutane huɗu ne suka rasa rayukansu a ƙaramar hukumar Yola ta Arewa da ke Jihar Adamawa sakamakon ɓarkewar cutar kwalara. Kantoman ƙaramar hukumar, Barista Jibril Ibrahim ya tabbatar da hakan wa manema labarai a ranar Lahadi inda ya ce hakan ya shafi gundumomin Alkawa, Ajiya da Limawa waɗanda yanzu haka akwai mutane 40 da ke karɓar kulawa a babban asibitin Yola game da lamarin. Ya ce, jami'an lafiya na cigaba da kula da yanayin tare da nuna buƙatar taimako daga gwamnatin jihar, ya na mai kira ga al'umma su taimaka wa likitoci a ƙoƙarinsu na…
Read More