Labarai

Da Daloli muka sayar mu ku da fetur ba Naira ba – Matatar Ɗangote ga NNPCL

Daga BELLO A. BABAJI Matatar mai ta Ɗangote da ke Legas ta musanta sayar wa NNPCL fetur akan N898 kowacce lita. Cikin wata takarda da Kakakin matatar, Anthony Chiejina ya fitar, ya bayyana iƙirarin kamfanin a matsayin ruɗar da al'umma. Ya ce, sun samu labarin da aka jingina wa kakakin NNPCL, Olufemi Soneye na cewa wai sun sayar mu su da mai akan N898 kowacce lita wanda ya ce hakan ba gaskiya ba ce. Ya yi kira ga ƴan Nijeriya su ƙaurace wa bayanin hakan tare da cewa su jira sanarwa ta musamman daga kwamitin da shugaban ƙasa ya naɗa…
Read More

NNPC ya sayi kowacce litar fetur akan N898 daga matatar Ɗangote

Daga BELLO A BABAJI Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya ce, ya sayi fetur daga matatar Ɗangote akan N898 kowacce lita yayin ya fara jidon farko a ranar Lahadi. An ga manyan motocin NNPCL na ɗaukar mai daga matatar wacce ta ke Lekki a jihar Legas a kafafen sada zumunta. A ranar Asabar ne NNPC ya ce zai tura motoci 100 zuwa matatar don ɗibar zango farko na man fetur mallakarta. An ruwaito cewa, NNPCL ya sayi kowacce lita ne akan N760 wanda kakakin kamfanin, Olufemi Soneye ya musa, ya na mai cewa N898 suka sayi kowacce lita guda.
Read More
Tarihin ƙarin farashin man fetur a Nijeriya daga 1973 zuwa 2024

Tarihin ƙarin farashin man fetur a Nijeriya daga 1973 zuwa 2024

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tsawon shekaru da dama 'yan Nijeriya sun shaida yadda farashin man fetur ke tashi lokaci bayan lokaci, wanda ya tashi daga Kobo 6 a shekarar 1973 zuwa Naira 897 a 2024 kan kowace lita. A makon da ya gabata ne Kamfanin NNPCL ya sanar da ƙarin farashin man fetur a ƙasar daga naira 617 zuwa naira 897 kan kowace lita. Nijeriya dai ce ƙasa mafi arzikin man fetur a nahiyar Afirka, kuma ita ce ta fi kowace ƙasa a nahiyar fitar da man zuwa kasuwar duniya. Lamarin da ya sa da dama ke ganin bai kamata…
Read More
Matashi ya kashe kakansa da kawunsa 

Matashi ya kashe kakansa da kawunsa 

’Yan sanda sun kama wani matashi kan zargin kashe kakansa da kuma kawunsa a yankin Apete da ke Ibadan a Jihar Oyo. Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, SP Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamari cikin wani saƙo da ya aike wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) a ranar Litinin. Osifeso ya ce, “An fara gudanar da bincike kan lamarin, za a fitar da bayanan da suka dace idan aka kammala bincike.” Ya ƙara da cewa, ’yan sanda suna aiki don gano dalilin da ya sa matashin ya aikata laifin. Ya ce, da zarar sun kammala…
Read More
Ba mu ƙara harajin ‘VAT’ ba – Ministan Kuɗi

Ba mu ƙara harajin ‘VAT’ ba – Ministan Kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Nijeriya ta musanta raɗe-raɗin cewa ta ƙara yawan harijin kayayyaki na ‘ɓAT’ zuwa kashi 10%, daga kashi 7.5%. Ministan Kuɗi na Nijeriya, Wale Edun a cikin wata sanarwa ya ce har yanzu dokokin ƙasar sun ƙayyade cewa hariji kayayyakin da ake biya kashi 7.5% ne. Ya ce: “Harajin kayayyaki a Nijeriya yana nan a kashi 7.5% , kuma hakan gwamnati ke karɓa. Domin haka gwamnati da dukkan hukumomin ta suna biyayya ga wannan tanadi na doka, kuma ba za su saɓa ba. Rahotan da aka riƙa yaɗawa game da ƙarin harajin kayyakin a Nijeriya ya…
Read More
Kotu ta umarci NNPC ya biya Naira miliyan 629 ga ma’aikacin da ya kora

Kotu ta umarci NNPC ya biya Naira miliyan 629 ga ma’aikacin da ya kora

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kotun ƙoli ta masana’antu ta ƙasa ta bayar da umarnin biyan wani ma’aikacin kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) naira miliyan 629 bisa rashin adalci da kamfanin ya yi masa a shekarar 2018. Alƙalin Alƙalan Sashen Shari’a na Fatakwal, Mai Shari’a Faustina Kola-Olalere, ta ce korar da aka yi wa mai shigar da ƙara, Dakta Williams daga kamfanin NNPC ya yi daidai da rashin bin dokokin aiki. An bayyana hakan ne a shafin intanet na kotun masana'antu ta kasa a ranar Litinin. Williams ya tabbatar da cewa ya yi aiki a matsayin mataimakin mai kula da…
Read More
Yanzu Buhari yana yi mana dariya bisa taɓarɓarewar tattalin arziki – Abati

Yanzu Buhari yana yi mana dariya bisa taɓarɓarewar tattalin arziki – Abati

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani gogaggen ɗan jarida kuma tsohon babban mai bai wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin yaza labarai, Dr Reuben Abati, a ranar Litinin ɗin da ta gabata ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai je ƙauyensa Daura a jihar Katsina yana raha kan halin da ƙasar nan ke ciki. Abati ya ce babban abin kunya ne ta fuskar tafiyar da tattalin arziki ga mutanen yankin Kudu maso Yamma da a cewarsa, suka yi ikirarin kwarewa wajen tafiyar da tattalin arzikin ƙasar. Abati, wanda shi ne jigo a cikin shahararren shirin nan na…
Read More
Gwamnati ta dakatar da kuɗaɗen tallafin da ake bai wa jami’o’in Nijeriya

Gwamnati ta dakatar da kuɗaɗen tallafin da ake bai wa jami’o’in Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ba da umarnin cire kuɗazen tallafi na jami’o’in tarayya da cibiyoyin ilimi daga asusun baitul mali. A wata wasiƙa da Hukumar Kula da Jami’o’i ta ƙasa ta aike wa shugabannin jami’o’in, mai ɗauke da kwanan watan 6 ga watan Satumba, 2024, Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya miƙa umarnin shugaban ƙasar zuwa ga Ministan Kuzi da Tattalin Arziki na Aasa, Wale Edun, inda ya ba da umarnin a dakatar da ba da tallafin. Umurnin ya kuma bai wa jami'o'i da cibiyoyin ilimi ’yancin cin gashin kansu don gudanar da asusun asusun tallafin…
Read More
Matsin rayuwa: Babban lauya ya gargaɗi Tinubu kan ruruwar wutar juyin-juya hali

Matsin rayuwa: Babban lauya ya gargaɗi Tinubu kan ruruwar wutar juyin-juya hali

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Lauyan Nijeriya (SAN) kuma Shugaban ƙungiyar Tsofaffin ɗaliban Makarantar Sakandaren Gwamnati na ƙasa, GSS, da ke Maraba, Ilorin, Barista Seni Ibiwoye, ya gargaɗi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan ka da ya zama silar juyin-juya hali a Nijeriya saboda taɓarɓarewar tattalin arziki. Ibiwoye ya yi gargaɗin cewa ci gaba da sakaci na iya haifar da juyin-juya hali a faɗin ƙasar tare da sakamakon mara kyau. Ibiwoye ya yi wannan gargadin ne a ranar Juma’a a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jarida a wajen bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar GSS Maraba, a Ilorin,…
Read More

Gwamnan Katsina ya halarci bikin sallar Gani a Daura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan jihar Katsina, Dikko Raɗɗa na daga cikin dubban mutanen da suka halarci bikin sallar gani a garin Daura da ke jihar. Sallar Gani tana ɗaya daga cikin bukukuwan da ake yi a kowacce shekara a ƙasar Daura na zagayowar wannan wata mai tsaki da aka haifi fiyayyayen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Cikin bukukuwan da ake yi akwai hawan Dawaki da Sarkin Daura ya kan jagoranta tare da hakimansa da sauran masu riƙe da sarautar gargajiya a kowacce shekara. A jawabinsa, mai martaba sarkin Daura Faruk Umar Faruk ya gode wa gwamna Raɗɗa kan ƙoƙarin…
Read More