Ma’aikatan kamfanoni sun gudanar da zanga-zanga kan ƙarin kuɗin wutar lantarki

Spread the love

Daga HARUNA AKARADA  

Da safiyar ranar Juma’a ne wasu ma’aikatan rukunin ƙananan masana’antu dake Unguwar Dawakin Dakata a Kano suka gudanar da zanga-zangar lumana don nuna damuwa da rashin amincewarsu kan ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi wa masana’antun nasu da suke aiki a wajen, wanda hakan ya janyo masu masana’antun nasu suka rufe kamfanonin nasu basa aiki a wajen na tsawon wasu kwanaki.

Wakilinmu da ya halarci wajen gudanar da zanga-zangar ya rawaito cewa magidanta ne maza da mata suka gudanar da wannan zanga-zanga suna riƙe da kwalaye masu ɗauke da rubutun nuna rashin amincewarsu da ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yi wa kamfanonin nasu. 

ɗaya daga cikin mata masu zanga-zangar ta shaida wa wakilinmu cewa “mun fito wannan zanga-zangar ta lumana ne domin bayyanawa hukumomin da abin ya shafa damuwarmu na halin da muka shiga na rashin gudanar da aiki a kamfanonin da muke aiki sakamakon ƙarin kuɗin wutar lantarki da aka yi musu yau kimanin kwanakinmu biyar muna zaune ba aiki muna zaman daɓaro, ga shi kuma dukkanninmu magidanta ne masu yara a gidajenmu, kuma sai mun fito aikin muke samun abinda za mu sarrafa gida.

“Saboda haka muna roƙon gwamnatin Kano da ta sanya baki kan wannan koke namu.”

Da yake musu jawabin share kukansu wakilin kwamishinan kasuwanci a gwamnatin Kano dake wannan rukuni na ƙananun masana’antu, Malam Zulkifilu Alasan ya haƙurkurtar da masu zanga-zangar sannan ya bayyana masu  cewa “gwamnatin Kano za ta yi dukkan abinda ya dace domin ganin an shawo kan matsalar gaba ɗaya, don za mu samu mu zauna da manyan jami’an gidan wutar lantarkin don ganin wannan ƙarin kuɗin bai yi tasiri ba.”

By ukarofi