Labarai

Idan kuka cire tsoro za ku iya kama ‘yan bindiga da hannunku – Raɗɗa

Idan kuka cire tsoro za ku iya kama ‘yan bindiga da hannunku – Raɗɗa

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa, ya mayar da martani ga masu sukar gwamnatinsa bayan da gwamnatin ta buƙaci al’umma su kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga. A cewar Raɗɗa, kiran al’uma su yi fito na fito da ‘yan ta’adda ba kasawa ba ce daga gwamnati. “Ba kasawa ba ce, banda soja banda ɗan sanda, a matsayina na gwamna na yi abinda zan iya yi, na ɗauki matasa, na horar da su na ba su makamai na ba su motoci da babura don su samar da tsaro,” inji shi. Gwamnan ya ce, yana takaicin yadda…
Read More
Gidauniyar Musulunci ta Malam Inuwa Dutse ta yaye ɗalibai 30 da suka sauke Alƙur’ani cikin shekara ɗaya

Gidauniyar Musulunci ta Malam Inuwa Dutse ta yaye ɗalibai 30 da suka sauke Alƙur’ani cikin shekara ɗaya

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An yaye ɗalibai 30 da suka yi saukar Alƙur'ani a cikin shekara ɗaya a karo na farko  a ƙarƙashin Gidauniyar Musulunci ta Malam Inuwa Dutse. Da yake zantawa da 'yan jarida a yayin bikin saukar. Darakta Janar na biyu na gidauniyar, Ambasada Hon. Usman Inuwa Dutse ya ce lokacin da suka ƙaddamar da buɗe gidauniyar Musulunci  ta Malam Inuwa Dutse a ranar an buɗe masallacin Juma'a. Ya ci gaba da cewa ana sallar Idi a masallacin da duk wani abu da ya shafi addinin Musulunci, sannan sai suka yi tunanin cewa ya kamata su ɗebi…
Read More
Al’ummar ƙaramar Hukumar Fagge sun roƙi Tinubu ya naɗa Abdul’azeez Abdul’azeez a matsayin kakakinsa

Al’ummar ƙaramar Hukumar Fagge sun roƙi Tinubu ya naɗa Abdul’azeez Abdul’azeez a matsayin kakakinsa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Al'ummar ƙaramar Hukumar Fagge da masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar APC  a ƙaramar hukumar sun yi kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu akan ya maye gurbin Ajuri Ngalale da ya ajiye aiki na mai magana da yawun shugaban ƙasa a kwanakin baya da ɗansu mataimaki  na musamman ga shugaban ƙasar akan kafafen yaɗa labarai Malam Abdulaziz Abdul'azeez. A wata sanarwar bayan taron da masu ruwa da tsaki na Fagge suka gudanar da shugaban matasa APC  na ƙaramar hukumar Musa Rabiu Fagge ya yi jawabi a madadinsu ya nuna cewa Malam Abdul'azeez  ɗan asalin…
Read More
Gwamna Aliyu ya yi alƙawarin gudanar da sahihin zaɓen ƙananan hukumomi a Sakkwato

Gwamna Aliyu ya yi alƙawarin gudanar da sahihin zaɓen ƙananan hukumomi a Sakkwato

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu ya buƙaci Jam'iyyar PDP da ta janye matakin da ta ɗauka na ƙauracewa zaɓen ƙananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga watan Satumba. Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC daga ƙananan hukumomi 8 na shiyyar Sanatan Sakkwato ta Gabas da suka yi dandazo a Goronyo domin gudanar da yaƙin neman zaɓen jam’iyya mai mulki. Ya ce haryanzu shugabannin SIEC gwamnatin da ta shuɗe ta PDP ce ta naɗa su, kuma har yanzu sune suke ci gaba da…
Read More
Ana samun ƙaruwar yara masu fama da tamowa a Zamfara – MSF

Ana samun ƙaruwar yara masu fama da tamowa a Zamfara – MSF

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar agaji ta likitoci watau MSF ta nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun ƙaruwa a yawan yara da ke fama fa lalurar tamowa ko rashin abinci mai gina jiki a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nijeriya. Ta ce matsalar tafi kamari a yankunan Shinkafi da Zurmi inda ta yi wa yara fiye da dubu 97 gwaji kuma sakamakon ya nuna cewa kashi 27 cikin 100 daga cikinsu na fama da tamowa. Gwaje-gwajen da aka yi a watan Yuni da ya gabata a yankunan ya nuna cewa fiye da kashi…
Read More

Yadda kwamitin gudanarwa na PDP ya fifita ɓangaren Wike kan na gwamnoni a Jihar Ribas

Daga BELLO A BABAJI Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya ƙarfafa matsayinsa a rikicin shugabancin jam'iyyar PDP bayan da kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ya tabbatar da tawagarta mambobinta a jihar Ribas. Baya ga nasarar haka ga ƴan ɓangaren Wike, sun kuma dakatar da zaman Majalisar Zartarwa ta Ƙasa saboda gujewa sauya hukuncin wanda da farko an shirya yin sa ne a ranar 26 ga watan Satumba inda daga bisani aka mayar da shi ranar 24 ga watan Oktoba. Kwamitin gudanarwar ƙarƙashin jagorancin Shugaban jam'iyyar, Umar Damagum ya yi hukuncin a yayin wani zama a hedikwatar PDP da ke Flazar…
Read More

Ambaliyar Borno: Halin da muka tsinci kanmu a ciki – Mazauna Maiduguri

Daga BELLO A. BABAJI Wasu daga cikin wanɗanda suka tsira daga ambaliya mafi muni da aka yi a tsawon shekaru 30 a Maidugurin Jihar Borno sun bayyana yadda suka tsira daga iftila'in. Mamakon ruwan sama wanda aka fara a ranar Litinin da dare ya yi sanadiyar batsewar tafkin Alua wanda ya fasa wani yanki tare da haifar da ambaliya acikin garin na Maiduguri inda ya ɗaiɗaita gidaje, makarantu da asibitoci a birnin. Sai dai, yayin da dama daga cikin mutanen yankunan suka tsira, akwai iyalai masu yawa da suka watse sakamakon ambaliyar. Wani mai suna Abubakar Tijjani da lamarin ya…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ware Litinin a matsayin ranar hutu don bikin Maulidi

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranar Litinin, 16 ga watan Satumba, 2024 a matsayin lokacin hutu ga ma'aikata don bikin zagayowar ranar Maulidin haihuwar Annabi Muhammad (SAW). Ministan Harkokin Cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya faɗi hakan a madadin Gwamnatin Tarayya inda ya ce, ya na taya al'ummar musulmi na gida da waje murnar bikin. Cikin wata takarda da Sakatariyar Ma'aikatar, Dakta Magdalene Ajani ta fitar, ta ce, Tunji-Ojo ya yi kira ga al'ummar Musulmi da ƴan Nijeriya baki ɗaya su kasance masu haƙuri da sadaukarwa. Ya kuma yi kira gare su da su yi amfani…
Read More

Ronaldo ya zama mafi shahara a kafar sada zumunta bayan samun mabiya biliyan ɗaya

Daga BELLO A. BABAJI Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi bayan samun jimillar mabiya biliyan ɗaya a shafukansa na sada zumunta. Ganin haka ya sa Ronaldo yi yi godiya ga magoya bayansa tare da jinjina mu su kan soyayyar da suke nuna masa a lokacin da ya ke haskawa a fagen ƙwallo. Ronaldo, wanda a halin yanzu ɗan wasa ne na ƙungiyar AL Nassr ta ƙasar Saudiyya, ya bayyana a shafinsa na X cewa hakan ya samu ne sakamakon soyayyar da shi da magoya bayan nasa ke wa tamola. Ɗan wasan yana da…
Read More

PDP ta dakatar da Dino Melaye kan ayyukan zagon-ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Jam'iyyar PDP reshen Jihar Kogi, ta dakatar da ɗaya daga cikin manyan ƴaƴanta, Dino Melaye kan zarginsa da ayyukan zagon-ƙasa. Dino, wanda tsohon Sanata ne, an dakatar da shi ne daga Gunduma ta ɗaya ta Ayetoro Gbede bayan ƙin amsa gayyatar da aka yi masa. Jagoran Gundumar na jam'iyyar ya ce an dakatar da shi ne sakamakon yin ayyukan da suka shafi zagon-ƙasa da kuma zarginsa da rashin yin biyayya. Haka nan, an yi hukuncin ne yayin nazari game da rahoton kwamitin ladabdtarwa na jam'iyyar wanda aka wakilta ya yi bincike akan zargin da ake ma…
Read More