Labarai

NNPC ta tabbatar da biyan kuɗi amma ba na tallafi ba

NNPC ta tabbatar da biyan kuɗi amma ba na tallafi ba

Hukumar NNPCL ta musanta zargin da ake mata na biyan kuɗin tallafi, ta bayyana cewa ba wanda ta biya tallafi wata tara da ya shuɗe. Babban jami'in kamfanin da ke kula da harkokin kuɗi Umar Ajiya ya bayyana haka a Abuja ranar Litinin. Ya bayyana cewa kamfanin na kula da bambacin farashi wajen shigo da mai ƙasar. Kamfanin bai biya kuɗin tallafi ga kowanne mutum ba tsawon wata takwas da ya wuce. Kuɗin da kamfanin ke biya kuɗin bambancin farashi ne wajen shigo da man amma ba tallafi ba ne. Ya bayyana cewa, bambancin kuɗin farashi ne suke magana kuma…
Read More

NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki matuƙar aka cutar da shugabanta

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar ƙwadago ta Ƙasa, NLC ta umarci mambobinta a faɗin Najeriya su fara yajin aiki daga tsakiyar daren yau matuƙar aka cutar da shugabanta, Joe Ajaero da wasu manyan jami'ainta. Hakan na zuwa ne bayan da rundunar ƴan sanda ta gayyace shi ofishinta kan zargin sa da hannu acikin ɗaukar nauyin ta'addanci, sata ta yanar gizo da zamba cikin aminci. Cikin wani saƙo da ƙungiyar ta fitar bayan kammala wani zaman gaggawa da Majalisar Zartarwa, FEC, hukumar ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ke kan shugaban nata, ta na mai cewa hakan tasirin siyasa ne da…
Read More
Ƙungiyar ƙwadago ta shiga taron gaggawa kan zargin ta’addanci

Ƙungiyar ƙwadago ta shiga taron gaggawa kan zargin ta’addanci

Shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun shiga wani taron gaggawa tare da shugaban su Joe Ajaero a hedikwatar su da ke Abuja. Taron ya biyo bayan wata gayyata da hukamar 'yan sanda ta yi wa Shugaban ƙungiyar bisa zargin cewa ya na taimakawa 'yan ta'adda da laifukan yanar gizo. Takardar mai kwanan wata 19 ga watan Agusta ta samu sa hannun ACP Adamu Mu'azu a madadin kwaminshinan 'yan sanda. Takardar ta buƙaci Joe Ajaero ya kai kansa hukumar domin amsa tambayoyi, rashin yin hakan ya zama karya doka wanda hukumar ba za ta ɗauka da wasa ba.
Read More

NIMET ta yi hasashen samun tsawa da mamakon ruwan sama a Najeriya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da yanayi ta Ƙasa, NIMET ta ce ta yi hasashen za a samu tsawa da mamakon ruwan sama a faɗin Najeriya tsakanin ranakun Litinin da Laraba. Hasashen da hukumar ta fitar a Abuja ya nuna za a samu tsawa a yankunan jihohin Kano, Katsina, Zamfara, Jigawa, Kaduna, Taraba da Bauchi a lokacin safiya. A yankin Arewa ta Tsakiya kuma, za a samu madaidaicin saukar ruwan sama a yankunan jihohin Neja, Nasarawa, Benue, Kwara, Abuja da kuma Filato. A yammaci kuma za a samu tsaka-tsakin saukar ruwan sama haɗe da tsawa a wasu yankunan Abuja,…
Read More

Dalilan da suka sa ba zan tsoma baki a ayyukan EFCC da ICPC ba – Tinubu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce tun da ya karɓi ragamar shugabancin Najeriya ya fara yunƙurin dakatar da ayyukan rashawa ta hanyar bai wa hukumomin EFCC da ICPC isassun ƙuɗaɗe da kuma ƙauracewa sanya baki acikin ayyukansu. Tinubu ya faɗi hakan ne a ranar Litinin inda ya bayyana rashawa a matsayin ɗaya daga cikin manyan hanyoyin da ke daƙile cigaba a ƙasar, ya na mai cewa wajibi ne a hukunta duk wanda aka samu da hannu acikin laifin. Shugaban wanda Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilce shi a taro cibiyoyin harkokin rashawa na yammacin Afirka karo na…
Read More

Ɗa ga Kwankwaso ya shiga sahun waɗanda ake tuhuma kan badaƙalar N440m kuɗin magani

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano, PCACC ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan badaƙalar Naira miliyan 440 da ake zargin sauya akalarsu. Kuɗin wanda aka turo Naira miliyan 10 daga asusun kowace ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar, an tura su ga wani kamfanin magani mai suna 'Novomed Pharmaceuticals' na Musa Garba Kwankwaso, ɗa ga Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso. A halin yanzu dai hukumar ta fara gudanar da bincike kan sayan magani daga kamfanin sakamakon saɓa wa dokokin gudanarwar al'umma. Wata takarda da PCACC ta fitar da ke ɗauke da kwanan wata…
Read More
Act for Humanity: Kiran gaggawa na Ranar Jin Ƙai ta Duniya 2024

Act for Humanity: Kiran gaggawa na Ranar Jin Ƙai ta Duniya 2024

Daga MOHAMED MALICK FALL Kowace shekara, Ranar Jin Ƙai Ta Duniya (WHD) tana zama ranar tunatarwa mai amfani game da muhimmancin ayyukan jin ƙai a duniya. A wannan shekara, taken shi ne, #ActForHumanity’ ya jaddada alhakin gamayya da muke da shi na kare fararen hula da ma'aikatan jin ƙai da ke yi musu hidima a cikin rikice-rikicen duniya. A yayin da muke bikin wannan rana a ranar 19 ga Agusta, yana da matukar muhimmanci a yi tunani a kan manyan abubuwan da ke tattare da tashe-tashen hankula da ke faruwa, da kuma tsananin buƙatar shugabannin ƙasashen duniya su dauki ƙwararan…
Read More

Shekh Abdullahi Saleh Pakistan ne sabon shugaban NAHCON

Daga NASIR S. GWANGWAZO Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da naɗin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a matsayin shugaban hukumar aikin Hajji ta kasa (NAHCON). Farfesa Pakistan babban Malamin Addinin Musulunci ne a Najeriya wanda ya yi karatunsa a Jami'ar Madinah da kuma Jami'ar Peshawar da ke Pakistan. Shekh Pakistan ya ƙware a harkokin da suka shafi aikin Hajji, sannan ya taɓa rike shugabancin hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano. Cikin sanarwar da Mashawarci na Musamman ga Shugaban kasa kan yaɗa labarai, Cif Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce shugaban ƙasar ya buƙaci sabon shugaban hukumar yayi amfani…
Read More
Dillalin filaye ya zargi lauyoyinsa da rashin iya aiki

Dillalin filaye ya zargi lauyoyinsa da rashin iya aiki

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Wani dillalin filaye daga Jihar Kebbi mazaunin Babban Birnin tarayya Abuja, Alhaji Ibrahim Mohammed Kamba, ya zargi wasu lauyoyin da ke gudanar da shari’o’insa a kan rashin iya gudanar da aiki cikin ɗa'a. Kamba, ya yi wannan zargin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce lauyoyin sun haɗa baki da wasu mutane domin su yi masa maguɗi. Ya bayyana cewa wasu filaye da lauyoyinsa ke gudanar da ayyukansu a babban birnin tarayya Abuja sun haɗa da; Niger Dock Global inɓestment limited with Plot No.…
Read More
Birtaniya za ta wahala idan likitocin Nijeriya suka bar ƙasar – Farfesa Pate

Birtaniya za ta wahala idan likitocin Nijeriya suka bar ƙasar – Farfesa Pate

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan lafiya na Nijeriya Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce ma'aikatar lafiya ta Birtaniya, (NHS) za ta yi fama idan ma'aikatan lafiya 'yan asalin Nijeriya suka bar aiki a ƙasar. Pate ya ce a duk duniya ana neman ma'aikatan lafiya na Nijeriya, kuma kashi 67 cikin ɗari na ma'aikatan suna aiki ne a Birtaniya. Kuma kashi 25 cikin ɗari na ma'aikatan lafiya na gwamnatin Birtaniya, 'yan Nijeriya ne. Ministan ya ƙara da cewa ana son likitoci Nijeriya da ma'aikatan jinya kuma wannan abu ne da ƙasar za ta yi alfahari da shi. Ministan ya…
Read More