Labarai

Gwamnoni da wasu jiga-jigan APC za su gana don tattauna matsalolin jam’iyyar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnonin jahohi da Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai, Barau I. Jibrin da Kakakin Majalisar wakilai, Hon. Tajuddeen Abbas da sauran jiga-jigan jam'iyyar APC za su gana a Abuja a ranar Talata don tattauna muhimman abubuwa game da jam'iyyar. Zaman ya ƙunshi waɗanda ke kan kujerunsu da tsofaffn gwamnoni da sauran masu-ruwa-da-tsaki. Manyan jam'iyyar a mataki na ƙasa suka shirya taron ƙarƙashin jagorancin zauren samar da cigaba na Ƙasa (NPH) don taya shugaban jam'iyyar da sakatarensa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ajibola Bashiru murnar cikar shekar ɗaya akan muƙamansu. Farfesa Abiodun Adeniyi daga Jami'ar Baze da ke…
Read More
Babu hujjar Arewa ta riƙa fama da talauci – Kashim Shettima

Babu hujjar Arewa ta riƙa fama da talauci – Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya musanta zargin da a ke cewa Shugaban ƙasa ya na nuna halin ko in kula ga Arewacin Nijeriya ganin yadda yankin ya ke da albarkatu da yawa. A wata tattaunawa da yayi da rediyo Faransa ranar Lahadi, ya bayyana cewa Arewacin Nijeriya ta na gaba wajen manufofin gwamnatin Tinubu. Ya cigaba da cewa, gwamnati na dagewa domin ganin ta inganta yankin Arewacin Nijeriya, duba da gwamnatin tarayya ta fitar da biliyan 100 domin inganta aikin noma. Ya cigaba da cewa gwamnatin ta ƙara mafi ƙarancin albashi daga dubu 30,000 zuwa 70,000. Kuma gwamnati ta ƙirƙiri…
Read More

NIS ta gayyaci matar da ta yaga fasfo ɗin mijinta a filin jiragen sama na Legas

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar shige da fice, NIS ta na gudanar da bincike kan lalata wani fasfo ɗin Nijeriya da wata mata ta yi inda ta gayyace ta domin yin bayani kan haka. Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa ya nuna yadda matar wacce matafiya ce ke ɗaiɗaita fasfo ɗin, wanda mallakin mijinta ne a filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Legas. Duk da cewa da farko ba a gano dalilin yin hakan ba, NIS ta ce aikin karya dokar ƙasa ce, kamar yadda mai magana da yawun NIS Kenneth Udo ya faɗa a ranar Litinin.…
Read More

WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar gudanar da jarrabawar ƙarshe ta ƴan makarantun sekandire a yammacin Afirka, WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar da aka yi na shaidar kammala sekandire a Afirka ta yamma (WASSCE). An samu sanarwar ne a lokacin da ofishinta ya wallafa bayanin a kafarta ta X. Ta ce, ta na ya mai sanar da ɗaliban da suka rubuta jarrabawar cewa a yau 12 ga watan Agusta, 2024 ta sako sakamakon na shekarar inda ta bayar da adireshi kamar haka ga waɗanda ke son duba nasu; http://waecdirect.org.
Read More

Zanga-zanga: ‘Yan sanda sun fara gurfanar da mutane 1,135 da ke tsare

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar 'Yan sanda a jihohin arewacin Nijeriya ta fara gudanar da bincike kan masu zanga-zangar da aka kama a yayin kwanaki 10 na zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar. Yayin da aka gudanar da zanga-zangar cikin lumana a kudanci, an samu ɓarkewar rikici da sace-sacen ababe da dama a Arewa wanda hakan ya sa aka sanya dokar hana fita a wasu jihohin yankin. Aƙalla mutane 17 ne aka samu rahoton cewa sun rasa rayukansu a jihohin Abuja, Kano, Neja, Borno, Jigawa da Kaduna yayin da aka samu da dama da suka samu raunuka wanda hakan ta…
Read More

Rikici tsakanin ƴan bindiga ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 30 a Zamfara

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƴan bindiga a ƙauyen Kawaye da ke ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 30 tare da jikkata wasu da dama. Hakan ya auku ne sakamakon wasu dabbobi da aka sace. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ɗaya ne daga cikin da yawa da ƴan bindigar ke yi a tsakaninsu wanda hakan ya yi sanadin salwantar rayuka da dama. Wannan hamayyar da ke tsakanin ɓangarorin ƴan bindigar ya haifar da mace-macce acikin su da ma shugabanninsu wanda hakan ya zama barazana ga zaman lafiyar yankin. Hakan nan,…
Read More

Doguwa ya sha alwashin kawo Kano ga APC a 2027

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazaɓar Doguwa/Tudun-Wada a jihar Kano, Hon. Alhasan Ado Doguwa ya yi alwashin kai jam'iyyar APC ga nasara a zaɓen gwamnan Kano na shekarar 2027. Doguwa ya faɗi hakan ne a ranar Lahadi a Abuja, a lokacin da ya ke mayar da martani ga takwaransa na mazaɓar Ƙiru/Bebeji, Abdulmumini Jibrin na ce masa (Doguwa) ya zama matsala ga nasarar APC a jihar. Jibrin ya ce Doguwa nauyin ne ga jam'iyyarsa. Sai dai bai amince da waɗannan kalamai, ya na mai cewa zai tabbatar APC ta yi nasara a babban zaɓen 2027 inda…
Read More
Akwai layin waya miliyan 30 da ba a haɗa su da NIN ba, inji kamfanonin sadarwa

Akwai layin waya miliyan 30 da ba a haɗa su da NIN ba, inji kamfanonin sadarwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban ƙungiyar Masu Gudanar da Harkokin Sadarwa ta Nijeriya, Gbenga Adebayo, ya bayyana cewa sama da layukan waya miliyan 30 ba su haɗu da lambar katin shaidar ɗan ƙasa yadda ya kamata ba, kuma suna cigaba da fuskantar haɗarin kullewa. Ya ce, waɗannan layukan sun fi yawa a cikin na’urorin bin diddigin motoci, na’urorin MiFi, na’urorin WiFi, da kuma injunan tallace-tallace. “Muna duba yiwuwar sama da katunan SIM miliyan 30, gami da waɗanda ke cikin na'urorin dijital daban-daban, waɗanda ba a haɗa su da NIN daidai ba. Yawancin waɗannan sim ɗin suna cikin na’urorin gano motoci,…
Read More
Masu shigo da man fetur za su yi wa matatar Ɗangote zagon ƙasa – Obasanjo

Masu shigo da man fetur za su yi wa matatar Ɗangote zagon ƙasa – Obasanjo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Toshon shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana shakku kan samun nasarar matatar man fetur ta Ɗangote wadda ta fara aiki a kwanakin baya. Matatar man fetur ta Dangote wadda hamshaƙin ɗan kasuwar na Afirka ya narkar da kuɗi dala biyan 20 wajen samarwa, ana sa ran za ta iya tace ganga 650,000 na ɗanyen mai a kowace rana. Sai dai a baya-bayan nan an samu taƙaddama tsakanin Dangote da gwamnatin Nijeriya, bayan da ɗan kasuwar ya yi zargin cewa ana yi masa zagon ƙasa. A tattaunawar da Obasanjo ya yi da jaridar Financial Times, ya ce…
Read More
Zanga-zangar yunwa a ka yi a Arewa saɓanin ta #ENDSARS ta ‘yan Yahoo

Zanga-zangar yunwa a ka yi a Arewa saɓanin ta #ENDSARS ta ‘yan Yahoo

Shugaban ƙungiyar Arewa Consultative Forum Shetima Yerima, a wata hira da yayi ya bayyana cewa 'yan Arewa sun fito zanga-zanga ne a dalilin yunwa da ƙuncin rayuwa da ke damun yankin. Hakan ya samo asali ne tun daga irin riƙon sakainar kashi da masu mulki su ka yi wa matsalolin al'ummar yankin. Ya cigaba da faɗa cewa, idan muka duba ko a rabon muƙamai, ba a ba 'yan Arewa sosai ba, waɗanda kuma a ka ba, ba su da mu'amala da mutane har su san halin da mutane ke ciki. Batun zargi da ake lokacin da a ka gudanar da…
Read More