13
Aug
Daga RABI'U SANUSI Shugaban Kwamitin Kula da binciken kadarori da aka kafa a Ƙaramar hukumar Ungogo, Dr. Saminu Umar Rijiyar Zaki, ya kammala aikinsa ya kuma gabatar da rahoton ga shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Ungoggo Alh sani Abdu Ungoggo a ofishinsa. Wannan na zuwa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun ƙaramar hukumar ta Ungoggo Malam Adamu ya fitar ga manema labarai Rahoton, wanda ya ƙunshi ayyuka, ci gaba, da ƙalubalen da ƙaramar hukumar ta fuskanta yayin lokacin canjin shugabanci, Dr. Saminu Umar ya nuna godiya bisa damar da aka ba shi na jagoranci tare da jaddada…
